Skip to content
Part 36 of 36 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Bayan sun ƙara ƴan maganganu ne ta mayar da dubanta a kan system ɗin da ke gabanta, tsohon record ɗinsa da tuni ya aiko musu da copy ta fara dubawa, domin ganin meye sila makancewar wannan Gentle Man ɗin.

Shiru ɗin da ya ratsa office ɗin ne ya ba Deeni damar ƙawata yadda zaman ya ke, tabbas duk da bai ga Dr. Niranjana ba, amma voice ɗinta ta tabbatar mashi da babbar mace ce, a cikin shigar sari mai lifaya ya riƙa kallon ta, idanunta kuma ɗauke da farin gilashi tana cigaba da duban system ɗin kan table ɗinta, a gefe kuma wasu files ne da sauran tarkacen da ya kamata a samu a kan table ɗin doctor.

Wannan hasashe na zuciyarsa ne ya tuna mashi can baya, take tsohon ciwon son aikinsa ya motsa, idanunsa ya lumshe tare da haɗiye wani gululu da ya tokare mashi zuciya.

Lokaci ɗaya Dr. Niranjana da Bashir suka dube shi, ɗan dafa jikinsa Bashir ya yi gami da faɗin “Ya dai Dr.?”, sai da Deeni ya sauke gwauron numfashi kafin ya ce “Ba komai”, ba don Bashir ya gamsu da maganarsa ba ya ce “Okay”, saboda sun san ba a surutu a gaban Doctor, musamman idan yana a kan aikinsa.

Ita kuwa adana maganarta ta yi har sai lokacin da ta gama duba record ɗin, ɗan matsar da system ɗin ta yi a gefe tare da ambatar sunansa, bayan duk sun maida nutsuwarsu a kanta ne ta ce “I have checked your record, and detected the reasons of your blindness is retinal detachment.”

Jinjina kai Deeni ya yi tare da faɗin “Ok Ma”, cike da son jin bayananta ya ƙara nutsar da zuciyarsa, domin a kan ƙwarewa take aikinta, cigaba da magana ta yi “So, I want examine you after some questions, then will decide what we should do next”, kusan a tare suka ce Okay.” Tambayoyi ta cigaba da yi ma Deeni na tun kafin ya makance, da kuma bayan ya makance, har da sakamakon aikin da aka yi mashi, shin ya ji alamun sauƙi ko a’a.??

A natse ya riƙa bata amsar duk kalar tambayar da ta yi mashi, wanda suka haɗa da suna da history na ciwon ido, amma kaf danginsa babu makaho, sannan kuma ya sha fama da ciwon kai, ko a ranar da ya makance ya yi ciwon kan da bai taɓa yin irinsa a duniya ba. Daga ƙarshe kuma ya tabbatar mata da yana aiki da screen sosai, amma baya da diabetes wanda shi ma yana haifar da cutar makanta. A fannin aikin da aka yi masa kuwa ya tabbatar mata da shi dai ba ji wani chanji ba, sai a jiya da ya ji reflection ɗin waya a idanunsa.

Sosai ta ji daɗin bayanansa, bayan duk ta gama naɗar bayanan ne ta yi shirin examine ɗinsa kamar yadda ta faɗa, domin ganin yanayin da idanun ke ciki, shin sauƙi aka samu ko kuma gaba ciwon ya ci.

Office ɗin cike yake da differents tools ɗin da suke examine eyes na patients, kowane tool yana amfani ne da irin matsalar da mutum ke fama da ita.

A bangaren da retina scope yake suka matsa da zama, retina scope tool ne da ake checking masu matsalar retina detachment, wanda shi ne asalin ciwon da Deeni ke fama da shi.

Retinal detachment shi ne, ɗagowa ko kuma cirewar shimfiɗar da ke a kan ƙwayar ido, wanda wannan shimfiɗar ita ce take ɗaukar haske ko kuma hotuna daga waje, tare da aika ma ƙwaƙwalwa domin tantacewa. Retina ita ce shimfiɗar, detachment kuma shi ne ɗagowar shimfiɗar, a dunƙule shi ne (Retinal detachment.)

Toh idan wannan shimfiɗar ta ɗago ne, sai ta danne jijiyoyin idanun da ke harba jini, daga nan sai a samu makancewar idanu, wani ya kan zo da alamun faruwar ciwon, shi ya sa ake son da mutum ya ji changes a idanunsa ko yaya ne ya je ya ga likita.

Ba wai retina scope ne tool ɗin kaɗai ta yi amfani da shi ba, kusan duka tools ɗin da ake examine eyes sai da ta yi amfani da su, domin ganin ko akwai wata matsalar, cikin ikon Allah kuwa babu wata matsala sai asalin wadda yake da ita. Bayan ta gama ne ta ce toh abin da ya dace shi ne a yi gaugawar sake surgery, domin dama a ƙa’idar wannan lalura shi ne aiki na gaugawa.

Kwana biyu ta ba su, cewar jibi za a yi mashi aikin, don ba za a tsaya ɓata lokaci ba, idan Allah ya so sai ya warke.

Bashir ne ya kama mashi hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma riƙe da sandarsa suka fita. Asma’u kuwa dama ta gaji sosai, ƙagare take su fito, shi kuwa Lalu ya zage sai hira yake da Akshay, kamar dama sun daɗe da sanin juna.

Su Deeni basu wani zauna ba suka ɗunguma, a motar Akshay suka tafi hotel ɗin da suka sauka, wanka da Sallah suka yi, suka ci abinci, kana suka gaisa da ƴan’uwansu a waya.

A can gida kuwa Hajiyarsu Deeni ce da su Hajiya Ummah a ɗaki suna ta tauna kewar su Deeni, musamman idan Hajiyar ta tuna Asma’un zata daɗe bata dawo ba sai hankalinta ya tashi, amma sai ta danne ma ranta, ta kuma yi musu addu’ar zaman lafiya.

Batun sake yi ma Deeni surgery ne ya ɗan tsaya mata a rai, lokacin da ɗakin ya rage daga ita sai Hajiya Ummah ne ta ce “Yanzu sai an sake taɓa idanun Deeni, ni bana son ayi ta cakular masa ido fa”, ran Hajiya Ummah cike da ƴar damuwa ta ce “Insha Allahu za a dace Hajja, kawai addu’a ce za a yi”, ta ce “Gaskiya ne, fatana ya warke, ya dawo a bakin aikinsa, bana son zaman gidan da yake”, Hajiya Ummah ta ce “Ai ko da lafiya zaman gida damuwa ne, bare kuma ba lafiya.”

Ba Hajiyarsu Deeni ba, duk wani wanda yake son shi da kuma ƙaunar shi yana yi masa kyakkyawan fatan ya koma aikinsa, musamman MD, wanda burinsa Deeni ya gaje shi, saboda a karshen shekarar nan Governor zai rantsar da su akan wani appointment da aka ba shi, kuma a ƙa’ida dole sai ya aje aikinsa, shi ya sa ya matuƙar damu da Deeni ya fita ƙasar waje, toh amma akwai yiwuwar burinsa ba zai cika ba, domin tun kafin ya bar office aka buƙaci ya bada sunan wanda zai wakilce shi, ba don ya so ba dole ya bada sunan Bello.

Zaune yake a office shi da sauran staff domin handing over na office ɗin ga Bello, bayan office ɗin ya yi shiru ne ya ɗaura da cewa “Maƙasudin wannan meeting ɗin shi ne mu yi cikakken bankwana ni da ku, sannan na hannata office ɗin nan ga MD mai jiran gado wato Dr. Bello.”

Tafi office ɗin ya kaure da shi, shi kuwa Bello sai ɗage hanci yake sama yana ta murmushin jin daɗi, domin burinsa na mamaye asibitin ya yi. A ganinsa wannan nasarar ta fito daga hannun malaminsa ne, ya manta da Allah ne mai Mulki, sannan yana bada mulki ga wanda ya so, domin ya jaraba shi.

Kamar yadda MD bai so Bello ya gaje shi ba, haka ma mafi yawancin staff, kawai suna pretending ne. Sosai kuma suka nuna damuwarsu a kan tafiyar MD, domin suna jin daɗin aiki da shi a matsayinsa na shugaba, “Yallaɓai, mu kam bamu so tafiyarka ba, duk da promotion ne ka samu”, in ji Dr. Abdallah, sosai MD ya fahimce shi, dariya ya yi kafin ya ce “Ni ma ba don ina so zan barku ba, sai mu yi fatan Allah ya sa haka ya fi alkhairi”, suka ce “Amiiiiin.’

Dr. Bello kuwa dariyar yaƙe kawai yake ma MD, domin yana cikin mutanen da ya tsana saboda MD na ƙaunar Deeni, kuma da bakin MD ya faɗa masa wannan kujerar ta Deeni ce, ya ɗauka kamar riƙon ƙwarya aka ba shi, don haka duk ranar da Deeni ya dawo zai ba shi kujerar shi, ɗaukar ma ransa ya yi ko za a mutu ba zai bada kujerar nan ba, wuyarta dai ya shiga office ɗin.

Kamar MD ya san me Bello ke saƙawa a ransa, sunan Deeni ya faɗa kamar haka “Na so a ce Deeni nan zan bar asibitin nan, domin ya gaje ni, na san zai yi aiki fiye da ni, toh amma haka Allah ya so..”

Tamkar an soka ma Bello wuƙa a rai saboda an ambaci dodonsa, “Deeni kuma dai?”, ya faɗa ba tare da ya san ya faɗa ba, Dr. Abdallah da ke kusa da shi ne ya ce “Ai ya cancanta, kaf hospital ɗinnan babu mai ƙoƙari irin nasa”, sosai Bello ya ji kamar magana ce ya yaɓa mashi, gyara maganarsa ya yi da faɗin “Toh ai baya ƙasar ma ko?”, bai samu amsa a wurin Abdallah ba, saboda hankalinsa na wurin MD inda yake faɗin “Ina fatan Allah ya ba Deeni lafiya, shi kuma Bello Allah ya ba shi ikon aiki tuƙuru Amiiin.”

Duban Bello ya yi tare da ba shi umrnin miƙewa ya karɓi aiki, tasowa Bello ya yi, inda ya MD ya miƙa masa wasu files, bayan ya karɓa ne office ɗin ya sake kaurewa da tafi, signing yayi na kama aiki tare da ƴan bayanai na godiya.

MD kuwa ya ga ƙauna, kyautuka masu yawa ya samu a wurin staff, sannan suka yi mashi albishir ɗin kawo masa ziyara haɗe da goyon baya a cikin muƙamin da ya samu.

Bello kuwa yana barin hospital ɗin ya zarce wurin Malaminsa a kan maganar barin kujera idan Deena ya warke, kai tsaye Malamin ya ce mashi “Abin da zai hana ka dauwama a kan wannan kujera fa shi ne mutuwa, ba wani Deeni makaho ba, don haka ka ja bakinka ka yi shiru”, Ran Bello a ɓace ya ce “Ai na ga yana son yi mani wala-wala ne”, ya ce “Na ce ka kwantar da hankalinka fa, babu wanda zai zauna wannan kujerar sai kai, idan ma an ɗaura wani toh da kansa zai tashi ya bar maka kayanka”, Bello ya gamsu da maganar, don haka ya samu ƴar nutsuwa a ransa.

Maganar bazawararsa ya yi mashi “Malam yau zan je wurin mutuniyar, me za a ba ni wanda zan ƙara mallake zuciyarta?”, dariya Malamin ya yi, gefensa ya duba tare da fiddo ƴar kwalbar turare a wata jaka ta fata, miƙa ma Bello ya yi “Ka shafa wannan turaren a jikin kuɗi sannan ka bata, tana karɓa zaka dawo ka ba ni labari”, hannu bibbiyu Bello ya damƙe turaren, kuɗi ya fiddo bandir na ƴan two hundred ya ba shi, Malamin na washe baki ya karɓe, lokaci ɗaya kuma ya ce “Dr. Baku gajiya dai”, Bello ya ce “Ai ka wuce haka Malam, aikinku na da kyau.”

A gaggauce Bello ya tashi ya nufi gida, wanka ya yi tare da cin abinci, yana yin sallar la’asar ya fito, turaren da malamin ya ba shi ne ya fiddo bandir na five hundred ya shafa mawa, sannan ya ja motarsa sai gidansu Habiba.

Ko da isar sa ƙofar gidansu ya kira ta cewar ya zo, bayan ya faɗa mata ne ya kafe a motar, idanunsa ƙyam a gate ɗin gidan yana jiran fitowar ta, aikuwa ba a daɗe ba sai gata ta fito, tamkar ya fita ya ruƙo hannunta, amma ya danne ma zuciyarsa, yana ta kallon ta har sai da ta zo dab da motar ne ya buɗe mata, cike da kissa ta shigo motar da sallama.

Amsawa ya yi da “Wa’alaikumu ssalam Habibaty”, dariya ta yi haɗe da gaishe shi, gaishe ta shima ya yi haɗe da ƴar tsokanarta tana dariya.

Habiba bazawara ce mai ji da kanta, duk namijin da ya ganta ya san ba matar yara bace, don kuwa ta ci man bleaching da supplement ta yi fari da ɓul-ɓul, Ko da Bello ke taƙama da shi likita ne, to akwai waɗanda suka fi shi kuɗi da matsayi suna zuwa wurinta, shi ya sa sai da ya haɗa da bin Malamai wurin neman zuciyarta, saboda wahalar da shi take. A yanzu ma da take ɗan kula shi wayau ne take yi mashi tana ta karɓe mashi kuɗi, shi kuma a ganin sa aikinsa ne ke ci, ita da shi suna ta yi ma juna kallon biri da ayaba.

“Yadda kika san in tuƙa motar nan mu tafi gida”, ya faɗa cike da zolaya, wani irin kallo ta yi mashi kafin ta ce “Saurin me kake ne?”, ya ce “Ko?”, ta ce “Eh mana”, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce “Allah ya nuna mana mun zama abokan rayuwa.”

Kasa cewa Amiin ta yi, don har a ranta bata yi niyyar aurensa ba, sai dai ta bi shi da dariyar yaƙe, idanunsa a makance suke, don haka baya gane wasu manufofi nata, shi dai tunda tana fitowa idan ya zo, sannan tana sakar masa fuska bukatarsa ta biya. Sun sha hira sosai, da zai tafi ne ya fiddo kuɗin da ya shafe da turare ya dube ta, “Habibaty”, da yake lashe money ce tana ganin kuɗi ta ƙara faɗaɗa fara’arta, “Na’am Habiby”, idanunsa cikin nata ya sakar mata murmushin mugunta, a ransa ya ce “Kin zo hannu yarinya”, a zahiri kuma cewa ya yi “Karɓi wannan, kya siyi alawa”, maƙe hannu ta yi, ya ce “Ki karɓa mana”, hannun ya damƙo ya manna mata, manufar hakan ita ce domin asirin da ke jikin kuɗin ya kamata, ita kuwa tana jin kuɗi a tafin hannunta ta damƙe su tana dariyar zuci.

“Toh Nagode Habiby, Allah ya ƙara rufa asiri”, ya ce “Amiiiiin Habibaty.”, tare suka fita motar, inda ya raka ta har bakin gate ɗin gidansu, “Ki shiga gida toh”, abin mamaki sai ya ji ta ce “A’a, bazan shiga ba sai ka tafi”, idanu ya ɗan zaro tare da faɗin “Da gaske?”, ta ce “Ƙwarai”, kai ya jinjina, a ransa ya ce “Aiki ga mai ƙare ka”, domin ko shakka babu aiki ya fara ci.

“Toh bari na tafi, kada na gajiyar da ke da tsayuwa”, murmushin da bai taɓa ganin irinsa a fuskarta ba ta sakar mashi, idanu ya kashe mata sannan ya tafi, kafin ya kai motarsa sai da ya waiwaya sau biyu don tabbatar da idan tana nan tsaye, yana shiga motarsa kuwa ya cake ta tare da faɗin “Yes! Tarkona ya kama kurciya”, domin kuwa tana nan tsaye kamar an kafe turken awaki. Key ya yi ma motar tare da wucewa ta gaban gidansu suna ɗaga ma juna hannu.

Da idanu Habiba ta raka bayan motarsa, har sai da ya ɓace ma ganinta sannan ta tura ƙofar gate ɗin gidansu, tamkar wadda aka yi ma kyautar duniya ta shiga ciki tana murna, kai tsaye ɗakinsu ta shige wanda suke rayuwa ita da Sister ta mai suna Samha, kan gado ta jefar da kuɗin tare da zama gefe, Samha na fitowa daga ban ɗaki ta ga kuɗi yashe a kan gado.

Tambayar ta tayi “Wannan fa?”, amsa ta bata da “Bello ne ya ba ni”, baki ta buɗe “Aaa! Kin gode”, Wannan ba sabuwar kyauta ce a wurinsu ba, shi ya sa Samha bata damu ba, don suna da kuɗin da suka fi waɗannan a gida da kuma banki.

Ganin Habiba sai juya kuɗin take tana murna ne ta ce “Wai sai murna kike kamar wannan ne karon farko da aka taɓa yi maki kyautar kuɗi”, duban ta Habiba ta yi “Ba kuɗin ne a gabana ba, wanda ya bani kuɗin ne a gabana”, idanu Samha ta ware “Yau ke ce ke faɗin haka a kan Bello?”, sai da Habiba ta sauke ajiyar zuciyar ƙaunar Bello kafin ta ce “Nima na yi mamaki”, Samha ta ce “Allah ya sa ba asiri ya yi maki ba, don wannan son na rana ɗaya da mamaki, nan kafin ki fita sai da kika gama zaginsa fa”, girgiza kai Habiba ta yi tare da lumshe idanu “Bana tunanin Bello yana asiri, idan ma shi ya yi mani, toh ya taimake ni, don ina tsanin ƙaunarsa”, hararta Samha ta yi tare da miƙewa daga gaban mirror, wardrobe ta buɗe bakinta na faɗin “Dole mu yi gaugawar nema maki maganin asiri, don wannan ɗimaucewar ba banza ba…”

<< Mutuwar Tsaye 35

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×