Tunda su Deeni suka bar Nigeria Hajiyarsu da ƴan'uwansa hankalinsu bai kwanta ba, kullum cikin fargarbar zai warke, ko ba zai warke ba, tunda dama ɗayan biyu ne, ko a yi nasara, ko kuma akasinta, shi ya sa kullum cikin yi masa addu'a suke ta hanyar yin sadakoki da kuma salloli, domin samun lafiyar Deeni tamkar samun lafiyar zukatansu ne, haka gazawar lafiyarsa daidai take da gazawar su, kasantuwarsa na tamkar Uba, kuma bango abin jingina a gare su.
A yau kuwa da ya kasance ranar da za a yi masa aiki ne Hajiyarsu ta ƙara ƙaimi a. . .