Shiru ɗakin ya yi, ba sa jin sautin komai sai na bugun zukatasu, jikinsu a mace dai suke ta kallon ɗan'uwan na su, musamman Asma'u da ke ta hasashen yadda rayuwar mahaifiyarta zata kasance idan Deeni bai warke ba, domin ita da ke tare da ita, ta fi kowa sanin illar da wannan lalurar ta Deeni ta yi mata, "Allah ko don mahaifiyarmu ka ba Yaya lafiya", a cikin ranta ta yi wannan addu'a mai cike da tausayin uwa.
Sosai Bashir da ke tsaye a gefen kujerar da take zaune ya lura da sanyin jikin Asma'u. . .