Tun a cikin dare Hajiyarsu Deeni ta ke jin kamar ana kunna mata wuta a rai, don kuwa ta kasa sukunin da bacci zai iya ɗaukar ta. Hakan ne ya ƙara tabbatar mata da faruwar wani abu marar daɗi, wanda kuma ba zata iya tantance ko menene ba. Lamarinta ta miƙa ma Allah, domin Shi ne masanin abin da ke zahiri da kuma ɓoye. Sai dai duk iya ƙoƙarinta na ganin abin bai yi tasirin da zai fito fili ba sai da ya ci tura, don kuwa sukuku ta tashi, har sai da Asma'u ta lura. . .