Skip to content
Part 4 of 31 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Tun a cikin dare Hajiyarsu Deeni ta ke jin kamar ana kunna mata wuta a rai, don kuwa ta kasa sukunin da bacci zai iya ɗaukar ta. Hakan ne ya ƙara tabbatar mata da faruwar wani abu marar daɗi, wanda kuma ba zata iya tantance ko menene ba. Lamarinta ta miƙa ma Allah, domin Shi ne masanin abin da ke zahiri da kuma ɓoye. Sai dai duk iya ƙoƙarinta na ganin abin bai yi tasirin da zai fito fili ba sai da ya ci tura, don kuwa sukuku ta tashi, har sai da Asma’u ta lura da sauyin yanayinta a lokacin da ta kawo mata breakfast, tambayar ta ta yi “Hajiyarmu, ko jikin ne.?”

Hannunta da ke riƙe da haɓa ta janye tare da girgiza kai “A’a Asma’u, kawai bana jin daɗi ne a raina tun daren jiya”, yadda ta ƙarashe maganar cikin sanyin jiki ne ya sa Asma’u kwantar da kai, cike da ladabi da kuma lallashin mahaifiyarta ta zauna gabanta tare da faɗin “Khairan Insha Allahu Hajja, ki yi breakfast ɗin toh, zaki samu sauƙi a ranki Insha Allah.”

Zuba mata kunun alkamar da ta damo a cup ta yi tare da miƙa mata, karɓa ta yi ta sha haɗe da ƴar wainar ƙwai. Ko dama can ita ba sosai take cin abinci ba, bare kuma yanzu da take jin firgici a ranta, bayan ta gama ne Asma’u ta kai ragowar kitchen.

Dawowa ta yi ta zauna domin rage ma Hajiyar damuwa, suna cikin hira ne suka jiyo sallamar Hajiya Umma ita da Salma, cike da murna Asma’u ta fito ta tarbe su.

Ko kusa Asma’u bata lura da yadda suke jirin-jirin ba, duk da babu wannan ƴar tsokanar da suke mata a matsayinta na autarsu, sannu da zuwa ta yi musu, bayan sun amsa ne suka ƙarasa cikin ɗakin.

Hajiyarsu kuwa sosai ta yi murna da zuwan su, domin ganin su zai taka muhimmiyar rawa wurin sanya mata nutsuwa a zuciya. Guiwa har ƙasa suka gaishe da ita, bayan ta amsa ne ta ɗaura musu da tambayar “Daga ina haka a tare.?”

 Salma da ta ida miƙe kafafunta a gaban Hajiyar ta ce “Daga gida”, Hajiya Umma kuwa cikin ɗan ƙanƙanen lokaci ta karanci yanayin mahaifiyarsu, daga kan kujerar da ta zauna ne ta ce “Hajiyarmu wai jikin ne?”, amsawa ta yi “A’a dai”, a marairaice Hajiya Umma ta ce “Kuma na gan ki sukuku?”, Amsa ta bata da “Kawai yanayi ne Umma, amma da sauƙi fa, tunda ina shan magani ba fashi”, kusan a tare suka haɗe baki wurin faɗin “Toh Allah ya ƙara lafiya”, ta ce “Amiiin.”

Dawowar Asma’u ɗakin ne ya maida hankalin Salma a kanta, cike da zolaya ta ce “Uhmm, Auta wai yaushe saurayin naki zai fito ne mu sha biki?”, dariya Asma’un ta yi, da ƴar kunya ta ce “Kai Aunty Salma, duka ni ɗin guda nawa ce?” Hajiyarsu ce ta ce “Da wannan rashin kunyar da take miji zai fito? Ai so nake ta samun wanda zai gyara mata zama”, baki Asma’un ta turo tana dariyar shagwaɓa.

Hajiya Umma na dariya ta ce “Ke auta ki gyara halinki, mazan yanzu da kike gani bassu da kirki”, Salma ta ce “Na rantse kuwa, tsaf namiji zai goge maki hadda.”

Sallamar Yaya Asiya ce ta katse musu maganar. Cike da murna Asma’u ta ruga ta rungume ta tana faɗin “Oyoyo ga Yaya Asiya”, itama Yaya Asiyar da murnar basaja ta ce “Ƙanwata ta kaina”, bayan sun saki juna ne Asma’u ta ce “Yau gidan cike da baƙi, su Aunty Salma ma sun zo”, tamkar bata san da zuwan su ba ta ce “Da gaske?”, Asma’u ta ce “Allah kuwa.”

Cikin ɗakin suka ƙarasa, Hajiyarsu ta ce “Amma kun tsara zaku zo ko?”, Yaya Asiya na dariya ta ce “A’a, kowa zuwanta daban”, baki kawai Hajiyar ta ɗan taɓe “Umm”, don ba yau suka saba haɗo baki su zo tare ba.

Guiwa har ƙasa itama Yaya Asiya da gaishe da mahaifiyarta da kuma ƴan uwanta, bayan ta zauna gefen gado ne Asma’u ta tambaye ta “Wai ina Adeel? Duk kun zo ba tare da yaro ko ɗaya ba”, amsa ta bata da “Yana tare da Nannyn sa”, cike da son yara Asma’u ta ce “Maimakon ki zo da shi”, kasantuwar gidan ba wani ƙaramin yaro, jikokin gidan kuma sai hutu ake ganinsu, gashi kuma yanzu school ake zuwa.

Yaya Asiya ta ce “Kin san dai ba zama yake ba, ni kuma ba dalilin da zai hana ni sakewa a gidanmu”, ɗan rausaya kai Asma’u ta yi “Ai shikenan”, tare da maida hankalinta ga Hajiya Umma da har yanzu take jin ba’asin lafiyar mahaifiyarsu, saboda ta kasa gamsuwa da yanayinta, bare kuma su faɗa mata sabuwar masifar da suka zo da ita. 

Domin tabbatar musu da sauƙin da Hajiyar ke samu ne Asma’u ta ce “Jikin fa da sauƙi sosai, kawai dai abinci ne bata son ci, kuma wai yau duk ba daɗi a ranta.” 

Kallon juna suka yi, wanda ke tabbatar musu da tana jin ciwon Deeni a jikinta, Hajiya Umma da take jin ta fi kowa tausayinta ta ce “Ɗan Allah ki daure ki riƙa cin abinci, kin ga ulcer nan idan ta taso maki bata yi maki da sauƙi, kuma ko ita kaɗai ai sai ta hana ki daɗin rai.”

Indai a kan lafiya ne bata yin jayayya da su, ko da kuwa ba zata yi abin da suke so ba, cewa ta yi “Toh, Insha Allah zan riƙa ci.”

Hira suka dasa sosai, duk da ransu cike yake da ƙunci, ita kuwa a lokacin da za a tambaye ta ina wannan fargaba? Toh zata ce bata san inda ta nufa ba a dalilin ganin ƴaƴanta mata huɗu reras a gabanta.

Can ba da jimawa ba kuma sai ga Lalu a gaba, Deeni da Deena suna biye da shi a baya, ba Hajiyarsu da ke dattijuwa ba, hatta Asma’u da ke yarinya sai da gabanta ya faɗi, duba da yau ranar aiki ce, duk rintsi kuma Deeni baya wasa da aiki.

Duk wata alama ta farat ɗaya da Hajiyar zata gane Deeni baya gani sun toshe ta, sai dai hakan bai hana jefa mata ayar tambaya a rai ba, saboda Deeni baya saka Gilashi sai a office kaɗai, sannan hannunsa cikin na Deena har ya zauna kan kujera a gefen Hajiya Umma. Uwa uba kuma yadda gabaɗayansu suka miƙe tare da shan jinin jikinsu ya ƙara firgita mata zuciya.

Kasa danne faɗuwar gaban dake ranta ta yi ta ce “Yau wannan taron na lafiya ne kuwa?”, Don jikinta ya gama bata matsaloli sun auku, wanda in dai suna da sabuwar magana da ita, to irin wannan haɗuwar suke.

Murmushin yaƙe kaɗai su duka suka yi. Gaisawa ta yi da Deeni tare da tambayar shi “Aikin fa”, cewa ya yi “Na ɗan ɗauki hutu”, da mamaki ta ce “Hutun me?”, Kasa magana ya yi, sai dai Lalu da ke zaune kusa da Yaya Asiya a gefen gado ya ce “Aikinsa ai yana bukatar hutu”, kai kawai ta jinjina tare da maida dubanta ga Deena da ita kuma take zaune a tsakanin Salma da Asma’u a ƙasa “Madinatu, ya jikin.?”

Kan Deena na ƙasa ta ce “Da sauƙi Hajja”, su kuwa kallon tausayi suka riƙa yi ma Deena da kuma Deeni, in banda Asma’u da bata san wainar da ake toyawa ba.

Yasu-yasu suka gaisa da juna, daga nan ɗakin ya yi shiru na wuccin gadi, kowa da abin da yake saƙawa a ransa. Shi dai Deeni da ƴan’uwansa kusan tunanin duk ɗaya ne, fatansu Allah ya sa mahaifiyarsu ta iya ɗaukar wannan jarabawa cikin sauƙi.

Ita kuma gani take anya ba ganin bankwana ƴaƴanta suka zo yi mata ba? Don kuwa irin haka ta sha faruwa, sai ƴaƴa sun zo gidansu zumunci, kwatsam washegari sai dai su ji labarin babban rashi na Uwa ko Uba, “Toh! Ko dai mutuwar ce Allah ya sa mu cika da Imani”, ta faɗa a ranta.

Asma’u kuwa ƴar damar tsokanar Deeni ta samu ta ce “Yaya Likita, yaushe ka fara saka Gilashi?”, ta ƙarashe maganar tana ƴar dariya.

“Toh uwar gulma, ina ruwanki da gilashin da ya sa”, Lalu ya gwalashe ta murya a murtuke, kamar kuwa tana jiran shi ta ce “Toh kai na tambaya da zaka sa mani baki a magana?”

Sanin tsaf zasu saida hali Hajiyarsu ta dakatar da su “Toh sababbi, kada in sake jin muryar kowa a cikinku”, idanunta a kan Asma’u ta ce “Dalla tashi ki je ki ga me gidan ke buƙata.”

Baki kamar ƴaƴan zoɓo Asma’u ta tashi, da idanu suka bi ta har ta fice daga ɗakin, Hajiya Umma ta ce “Allah ka shirya yarinyar can”, Lalu ya ce “Amiin dai”, don kuwa ya fi kowa sanin halin ta.

Taƙarƙarawa Deena ta yi ta bi bayanta, don ji take duk sun yi mata kwarjini, a kitchen ta tarar da ita wurin zink tana haɗa kwanukan wanke-wanke. Su ɗin ƙawayen juna ne a Islamiyya, kuma a sanadin Asma’u ne Deeni ya ga Deena ya fara so, har Allah ya sa ta zama matarshi.

“Wai ƙawa yaushe zaki chanja ne dan Allah, ke kullum ki yi ta ma Lalu rashin kunya?”, Deena ta faɗa cike da son nuna mata illar wannan masifaffen halin nata marar kyau, a ɗan tsiwace Asma’u ta ce “Ke ki bar ni da shi, ya mugun raina ni ne, kuma kin san ni ba zan lamunta ba.”, Kallon samun ƴan’uwan kika yi, da har kike musu rashin kunya Deena ta yi mata, don kuwa Deena bata da Yaya, balle ƙane, ita kaɗai ce a wurin mahaifanta, kuma tunda ta fara wayau take jin ina ma tana da ƴan’uwa, sai da ta yi aure ne ta rage jin wannan damuwar, saboda ƴan’uwan Deeni sun zame mata uwa ɗaya uba ɗaya.

Kawar da maganar faɗan Deena ta yi tare da faɗin “Hmm, kike ta masifa ba tare da kin san me ya kawo mu ba”, gabaɗaya Asma’u ta maida dukkan hankalinta ga Deena “Me ya kawo ku dan Allah?”, Saboda itama ta fara ji a jikinta ba dai lafiya ba.

“Yaya ne fa ya makance?”, Deena ta bata amsa cikin raunin murya, ɗif! Wutar Asma’u ta ɗauke har mug ɗin dake hannunta ya kai ƙasa tare da tarwatsewa ba tare da ta sani ba, domin kuwa ta ga dukkan shaidar da bata bukatar sake tambayar Deena idan da gaske ne abin da ta ji.

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”, ta shiga faɗi, lokaci ɗaya kuma ta lumshe idanunta, sakamakon tashin hankalin da ya game dukkan illahirin jikinta, wanda za ta iya kwatanta shi da irin wanda ta ji a lokacin da saƙon mutuwar mahaifinta ya riske ta a makaranta.

Jiri na ɗibarta ta ratsa cikin fasassar kwalbar mug ɗin ta wuce, sauƙinta ma tana da takalmi a ƙafarta, da ba abin da zai hana ta jin ciwo.

Mara mata baya Deena ta yi tana dakatar da ita, saboda bata son Asma’u ta je da reaction ɗin da za a gane ta faɗa mata abin da ya faru, sai dai sam Asma’u bata jin me take faɗa har ta shiga ɗakin.

Taraswa ta yi ɗakin ya rikice, su Hajiya Umma suna ta kuka, wanda ke nuna maganar ta fasu kenan, Deeni kuma ya dawo a gefen mahaifiyarsu ya haɗe kai da guiwa yana ta kuka shi ma, hannun Hajiyarsu kuma dafe da bayansa tana faɗin “Allahn da ya ɗaura maka, shi ne kuma zai yaye maka Deeni.”, Idanunta na fitar da hawayen tausayinsa ta ƙarashe maganar.

Ji Asma’u ta yi kamar ana yamutsa mata ƙwalwa, a hakan ta ƙarasa tare da durƙushewa gaban Deeni, magana take son yi, amma sai iskokin dake shirin takawa a kanta suka riga ta, wata irin ƙara ta fasa, wadda tsananin gigitar da kowa ya yi sai da ɗan cikin Deena ya juya.

Daga inda take ta malale ƙasa tana shure-shure da ihu. A kiɗime Deeni ya bi sautinta zai riƙe ta, dakatar da shi Hajiyarsu ta yi “Yi zamanka tunda ga Faruƙu nan”, jiki a sake ya koma ya zauna.

Nan Lalu da su Hajiya Umma suka rirriƙe ta, suna mata addu’a, ita kuwa sai gunji take, lokaci ɗaya kuma wata irin murya ta riƙa faɗin “Ba zai yiwu ba, maƙiya ne suka yi ma Deeni haka, don haka dole mu ɗaukar masa fansa.”

Babu wanda ya bi ta kan abin da take faɗa, ƙoƙarinsu kawai su ga ta samu nutsuwa, addu’a suka cigaba da yi mata a ruwa suna watsa mata, a hankali ta fara rage gunjin, su kuwa basu fasa ba sai da suka ji ta yi shiru.

Wannan rana tana ɗaya daga cikin ranakun da har abada ba zasu manta ba, don kuwa ciwon iskokin Asma’u kaɗai bala’i ne mai zaman kansa, wanda Hajiyar ta fi kowa tsanar sa.

Nannauyar ajiyar zuciyar da ta sauke ne Salma ta samu damar kiran sunanta, a hankali Asma’u ta buɗe idanunta da suka ƙanƙance, sannu suka riƙa yi mata, tare da taimaka mata ta tashi zaune.

Ƙuri ta yi ma Deeni, cikin ranta tana jin dama mafarki take, don kuwa naƙasar Deeni tamkar naƙasarsu ce.

“Allah ya baka lafiya Yaya Deeni”, ta faɗa tare da fashewa da kuka, a hankali Deena ta ɗangyaso ta zo gefenta ta zauna, kuka kaf ɗakin suka cigaba da yi. Ita kuwa Hajiyar zuciyar har ta bushe saboda bala’i, sannan wannan kukan da suke juya mata kai yake, cikin ɗaga murya ta ce “Haba! Wai idan mutuwa ya yi fa? Wannan kukan da kuke ya isa haka, addu’a da neman lafiya zamu taya shi.”

Deeni ya ji daɗin wannan tsawatarwar, don shi ya ma rasa ya zai yi, tsagaita kukan da suka yi ne ya ba shi damar fara magana, inda ya ce “Dan Allah ku sa ma zuciyarku salama, ni kaina da lalurar ke a jikina na ɗauki wannan a matsayin jarabawar Ubangiji. Sai mu yi fatan Allah ya bamu ikon samun nasara a kan ta.”

Nasiha sosai ya yi musu a kan kada su bari wannan damuwar ta yi tasirin da zata hana su walwala, sannan ya tabbatar musu da shi dai ba zai fasa komai na mu’amalar rayuwarsa ba ko ya warke ko bai warke ba, duk da ya san akwai challenges da yawa a gabansa.

Hajiyarsu ma sosai ta danne uƙubar da take ji a ranta, don tun a karon farko ta fahimci tsoron tashin hankalin da zata shiga suke, shi ya sa sai da suka yi ta ƴan kwanaye-kwanaye, sannan daƙyar Lalu ya faɗa mata. Nasiha ta yi musu sosai a kan su sani yanzu amanar Deeni na kansu, ya zama wajibi su taimake shi da ƙarfinsu da kuma dukiyarsu wurin ganin ya samu lafiya.

Wannan maganar ce ta sa Yaya Asiya faɗin saƙon mijinta da ke Lagos yana aiki, cewar a fara magani kafin ya dawo nan da two weeks, saboda ya san mutanen da zasu haɗa shi da mabanbantan masu maganin cutar idanu sosai a Nigeria. Godiya suka yi mashi, sannan ɗakin ya ɗan yi shiru tare da dasa magana a zukatansu.

Maganar da ke ran Hajiya Umma tana bukatar privacy, mafarin ta dubi Asma’u “Ki ɗan je waje kin ji Aunta”, ba musu ta miƙe, duk da ba a ambaci Deena ba, amma ta tashi zata fita.

Har ta kai baƙin ƙofa ne suka ankare da ɗingishi take, “Deena, me ya same ki kike tafiya a haka?”, Hajiya Umma ta tambaye ta da hanzarin gaske.

Gaban Deeni ne ya faɗi, bai san lokacin da ya kasa control ɗin tsananin kulawarsa ga Deena ba ta hanyar faɗin “Ɗingishi kuma.?”

Daga bakin ƙofa Deena ta basu amsa “Daɗewar da na yi a zaune ne, sai ƙafata ta riƙe”, kai suka jinjina, Salma ta ce “Allah ya sauƙe, ki bi a hankali to”, Deena ta ce “Toh”, sannan ta fice.

Maido hankulansu wuri ɗaya suka yi, domin jin me ke ran Hajiya Umma, ita kuma kamar ta san jiran ta suke ta ce “Dama maganar Deena ne, kuna ganin mahaifiyarta zata yadda ta zauna da Deeni a halin da yake ciki? Kun ga tuni matar nan ke neman hanyar da zata raba aurensu.”

Sosai suka jinjina maganar ta, Hajiyarsu da ta daina shakkar halin Maman Deena ta ce “Toh idan ma ta ɗauki ƴarta ai ba wani abu bane, Allah na nan, da sannu zai ba Deeni mafita a rayuwa.”

Lalu kuwa cewa ya yi “Ni tausayi ma Deenar take ba ni, ko kaɗan bata da damuwa.”, kusan a tare suka ce “Wallahi kuwa.”

Deeni ya fi kowa fargabar yadda lamarin zai kasance, cewa ya yi “Ai har yanzu ma bata san bana gani ba”, Hajiyar ta ce “Ya kamata kuwa a faɗa mata”, Hajiya Umma ta ce “Gaskiya ne.”

Daga can kitchen kuwa jugum Asma’u ta yi, ga uban aiki a gabanta, amma ta rasa ta ina zata fara, sai da Deena ta fara wanke kwanuka ne ta ankare tare da yi mata ɗauraya.

A hankali Asma’u ta ɗan fara soko magana inda ta ce “Dee-dee, wai ya kika ji a ranki lokacin da kika ga Yaya baya gani.?”

Dakatawa da wankin plate ɗin hannunta ta yi ta ce “Ai baki ba zai iya fasalta irin tashin hankalin da na shiga ba, amma sai da na ji dama mutuwa na yi kafin in ga wannan bala’i, har a yanzu haka nake ji, kawai ina danne ma raina ne saboda na san Yaya ya fi ni jin haka, tunda shi lalurar a jikinsa take.”, cikin muryar kuka ta ƙarashe maganar.

Asma’u kuwa tuni tausayi ya sanya ta hawaye, kafaɗar Deena ta dafa, “Allah Sarki Dee-dee, Allah ya ba Yaya lafiya, ni ma na rantse ji nake a raina kamar na mutu, Yaya yana bani tausayi sosai”, kukansu suka ɗan sha, bayan sun gama ne suka cigaba da wanke kwanukan, lokaci ɗaya kuma suna tattauna wannan jarabawa cikin jimami.

A ɗaki kuwa suna cikin magana ne wayar Deeni da ke gaban aljihu ta ɗauki ruri, fiddo ta ya yi, cikin hasashe ya so answer call ɗin, sai dai bai san upside down wayar take ba, sai da Salma ta karɓa ta gyara mashi, wannan kaɗai sai da ya sa dukkansu ƙwalla, kuma hakan ya ƙara tabbatar musu da Deeni na bukatar taimako, tunda waya ma ya kasa control ɗinta, ina kuma ga sauran ayyukan yau da kullum.

Tsit suka yi suna sauraron wayar da Deeni ke yi, daga can cikin wayar wancan ya ce “Lallai ka samu lafiya tunda har iya fita.”

Murmushin yaƙe Deeni ya yi “A’a da sauƙi dai, after magrib idan ka samu dama ka shigo gidana”, daga can ya ce “Toh bari mu gani, ka san hidimar gabana yawa ne da ita, ba lallai ne ka ganni ba.”, Ɗan rausaya kai Deeni ya yi “Ok, ba damuwa, thanks for calling.”

Bayan ya gama wayar ne Hajiyarsu ta tambaye shi “Waye wannan ya kira ka?”, cikin ɗacin rai ya ce “Colleague ɗina ne”, Salma ta ce “Ji yadda yake magana a galatse, kamar bai so fitar taka ba ma”, guntun murmushi Deeni ya yi “Allah dai ya sauƙe”, saboda ya san ko da mutuwa ya yi, toh Dr. Bello na cikin masu farinciki, kawai Deeni na pretend ne, saboda aiki ya haɗa su tare.

Cike da ɓacin rai suka yi ta maganar, har suka zo inda Hajiya Umma ta ce “Ai batun maganar aljannun Auta, a ce haka kawai mutum baya gani, anya ba hada maƙiya ba..?”

******

Godiya ta musamman ga masu bibiyar wannan littafi na MUTUWAR TSAYE, Allah ya bar ƙauna Amiiin.

Sannan kada ku manta da danna star 🌟, comments da kuma sharing. Uwa Uba kuma ku yi subscribe a bakandamiya hikaya, ta haka zaku cigaba da samun ƙayatattun litattafai daga fasihan marubuta.

Taku ce a har kullum wato HADIZA ISYAKU, n maku fatan Alkhairi.

<< Mutuwar Tsaye 3Mutuwar Tsaye 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.