Skip to content
Part 40 of 40 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Tamkar a mafarki haka Hajjah ta ji wannan albishir na warkewar masoyin ɗanta, murna fal da ranta ta ce “Kai Farouk, da gaske, ko kuma tsokana ta kake?”, daga cikin wayar ya shagwaɓe mata ” Haba Hajiyata, ta ya zan tsokanar ki, na rantse kuwa ya warke”, cike da rikicewar murna ta ce “Ina Deenin?”, tana jin lokacin da Lalu ya miƙa ma Deeni wayar, sallamar sa ta ji cikin sanyin murya, bayan ta amsa ne ta ce “Aiki ya yi kyau ko?”, ya ce “Eh Hajjah”, sai dai bai faɗa mata ba sosai yake gani ba, duk don ta samu nutsuwa a ranta, cewa ta yi “Alhamdulillah, Allah ya ƙara lafiya, ya kyauta gaba”, Deeni ya ce “Amiiiiin ya Allah”, bayan sun gama wayar ne ta ɗaga hannuwanta sama, cike da ƙasƙantar da kai ga Ubangiji ta ce “Allah na gode maka da ka sa wannan lalura ta Deeni ba mai ɗorewa bace.”

Su Hajiya Ummah na dawowa daga gaisuwar maƙwabta da suka je suka tarar da ita a haka, riga su magana ta yi da faɗin “Kai albishirinku”, Aunty Salma ce ta karɓe da faɗin “Goro”, ta ce “Toh ɗan’uwanku ya samu lafiya”, sun san ba zata taɓa yi musu ƙarya ba, amma Yaya Asiya bata san lokacin da ta ce “Hajjah da gaske?”, Hajjah ta ce “Na rantse kuwa, yanzu muka gama waya da su.”

Dukkaninsu suna da ƴaƴa, kuma sun san irin raɗaɗin da uwa take ji idan ɗanta ya shiga wani hali, toh amma Hajiya Ummah da ke da manyan ƴaƴa, da kuma tabon ɗa a ranta ta fi su sanin wannan emotion ɗin, rungume mahaifiyarta ta yi, idanunta cike da ƙwallan farinciki ta ce “Congratulations Hajjah, Allah ya ƙara mashi lafiya”, Hajjah ta fahimci hada kukan kai take, ɗan shafa bayanta ta yi “Amiiiiin ya Allah, ke ma Allah ya gyara maki naki ɗan, ya shirya maki shi”, duk suka ce “Amiiiiin.” Kiran Deeni suka yi, ɗaya bayan ɗaya suka yi magana da shi tare da taya shi murna a kan wannan nasara da ya samu, wadda take tasu ce baki ɗaya.

A can India kuma Deeni sai kallon yadda su Lalu ke ta murna yake, wannan murnar da suke yi ce kuma ta haifar masa da wata sabuwar murnar a ransa. Wani ɓangare na zuciyarsa ne ya dakatar da shi ta hanyar tambaya “Yanzu da ace ban warke ba fa, ya mahaifiyata da ƴan’uawana zasu yi?”, amsar ita ce da yanzu suna cikin ƙunci da baƙinciki, idanunsa a lumshe ya ce “Allah Nagode maka da ka sa ba zasu yi wannan baƙincikin ba.”

Mutane daban-daban Dr. Niranjana ta yi ta kawo wa domin su taya su murna su da suka yi aikin, da kuma shi da aka yi mashi aikin.

Bayan duk sun fita ne Deeni ya ce “Farouk, na ji kana faɗa ma kowa, amma baka faɗa ma Deena ba”, dariya su duka suka yi, Farouk ya ce “Tana offline ne ai, amma na ajiye mata saƙo”, ɗan rausaya kai Deeni ya yi alamar “Okay”, suka ci-gaba da magana cike da godiyar Allah. A cikin ɗan ƙanƙanen lokaci labarin warkewar Deeni ya game ƴan uwa da abokan arziki, waya da voice note kuwa har gajiya suka yi da su.

A bangaren Rahila kuwa tana cin karo da saƙon warkewar Deeni ta ji faɗuwar gaba, saboda wannan zai iya zama barazana ga buƙatarta ta son aurensa. Ta wani bangaren kuma ta yi murna saboda a matsayinta na ƴar adam mai tausayi, ko da bata san Deeni ba toh zata yi masa fatan ya samu lafiya.

Bayan sun gama vedio call da su Lalu ne ta yi jugum a office ɗinta, akwai Patients ɗin da idan so samu ne zata gansu, amma mutuwar jikinta ta hana ta komai, ringing ɗin wayarta ne ya katse mata tunanin da ke ranta, Dr. Safiyya ce ta kira ta, da hanzari ta ɗauka da sallama, bayan Dr. Safiyya ta amsa ne ta ɗaura mata da “Kin ji mutumin ki ya samu sauƙi ko?”, a wasance Rahila ta ce “Eh na ji Gwaggo, ai na taya shi murna ba kaɗan ba”, Dr. Safiyya ta ce “Ke dai bari Rahila, sai dai mu yi fatan Allah ya kyauta gaba, ya ƙara lafiya kuma”, Rahila ta ce “Amiiiiin ya Allah” damuwar da ke ranta ce ta ɗora da ita ta ce “Yanzu sai a mayar masa da matarsa ai”, Dr. Safiyya ta ce “Aikuwa ba dai Hajiya Hadiza ba”, Rahila ta ce “Saboda me Gwaggo? Na ga ya samu lafiya fa, duk da sun ce ba irin can ɗin nan ya warke ba”, Dr. Safiyya ta ce”Hajiya Hadiza ce fa, dama can ba son auren take ba, kuma kin ga kuwa tunda ta samu sun rabu kin ga sai wani ikon Allah a sake maida auren.”

Wannan maganar ba ƙaramin daɗi ta yi ma Rahila ba, cewa ta yi “Toh Allah ya kyauta”, Dr. Safiyya ta ce “Amiiiiin dai, kin san me?”, Rahila ta ce “A’a”, Dr. Safiyya ta ce “Allah kuwa ba don ina tausayin Deena ba, da sai ku fahimci juna ke da Deeni, toh yarinyar tana son mijinta, idan na haɗa shi da ke a matsayinki na ƴar ɗan’uwana ban yi mata adalci ba”, karaf Rahila ta yi “Toh me ye a ciki?”, ta ce “Ke dai ka guji abin da baka so a yi maka”, Rahila ta ce “Haka ne, Allah ya ba kowa mafita ta Alkhairi.”

Sun yi magana sosai, daga bisani suka yi sallama. Rahila tana da zurfin ciki sosai, shi ya sa bata iya faɗa ma Dr. Safiyya ba cewar tana ƙaunar Deeni, sai dai duk da haka ta ji haushin kanta sosai, tuhumar kanta ta yi da “Me ya sa ban yi insisting a kan maganar ba?”, wata zuciya ce ta ce “Toh amma fa Deena ba zata ji daɗi ba, ban ma yi mata adalci ba gaskiya”, idanu ta lumshe tare da sauke ajiyar zuciya, cike da tausayin kanta ta ce “Allah gani gare ka”, lokaci ɗaya kuma ta cigaba da nema ma kanta mafita.

Kamar yadda Rahila ta kai maƙura wurin ganin ta wace hanya ce zata mallaki Deeni, toh itama Deena bayan ta gama tsalle da murnar samun lafiyar Deeni ne ta zauna tana ta saƙawa da kwancewa a ranta, tunani ta shiga yi shin Ummanta zata bari ta koma ma mijinta tunda ya samu lafiya? Bata da wata amsa, sai hukuncin da Allah ya yanke musu.

Batun Umarar da zasu je ne ya cire mata damuwa a ranta, saboda zata je inda ake karɓar addu’a. Tanadin irin nacin addu’ar da zata yi ma Allah ta yi ta tsarawa a ranta, batun bacci dama idan ta je bata taso ba, tunda ba shi ya kai ta ba, fata ta yi Allah ya sa lokacin sun Deeni su ma sun je, tunda ya faɗa mata idan zasu dawo, toh zasu biyo ta Saudiyya.

A lokacin da wasu ke ta murna haɗe da nuna tsantsar godiyarsu a wurin Allah bisa ga lafiyar da Deeni ya samu, a lokacin ne maƙiya da mahassadansa suka kasa ko da motsi, musamman Bello da ya fi kowa tsanar Deeni, wanda kuma wannan tsana bata da hujja sai kawai don Deeni ya fi shi komai. Yana a wurin Habiba ne ya ci karo da labarin samun lafiyar Deeni a Whatsapp group ɗinsu, tsabar fargaba da baƙinciki bai san lokacin da ya ce “Bala’i” ba, hankalin Habiba a kan wayarsa ta ce “Me ya faru?”, ya lura da leƙen wayar, ɗan janyewa ya yi “Wani abu ne ya faru”, tambayarsa ta yi “Jaje ko murna?”, ya ce “Jaje ne”, cikin ƴar damuwa ta ce “Toh meye ne?” Shi kansa ya san idan ya faɗa mata farkon abin da ya sa shi faɗin haka zata zarge shi, ce mata ya yi “Rashin lafiya ne”, baki ta ɗan taɓe, saboda ta lura da ƴan kauce-kaucen da yake mata, cewa ta yi “Allah ya kyauta”, ya ce “Amiiiiin.”

Sosai ya ji ya tsani komai saboda hassada, hatta Habibar sai ya ji haushinta yake ji, faɗa mata ya yi zai tafi, da ƴar damuwa ta shashshaɓe fuska “Da wuri haka?”, ya ce “Ni ma ban so tafiya da wuri ba, uzuri ne ya taso”, ɗan rausaya kai ta yi “Ai shikenan.”

Burinsa shi ne ya bar wurin, da salon da ba zata gane bane ya lallaɓa ta har ta shige gidansu, cikin motarsa ya shiga tare da ɗaukar waya ya buga ma Malaminsa Yahuza, ko gaisawa basu yi ba ya ce “Malam mutuminka fa ya warke”, da huci ya ƙarashe maganar.

Malami Yahuza ya fahimci cikin tashin hankali yake, kwantar masa da hankali ya yi da faɗin “Toh sai me idan ya warke?”, Bello ya ce “Da matsala fa, ka san yana dawowa zai ce aikinsa, kuma wannan kujerar da nake a kai an faɗa mani tashi ce”, dariya Malam Yahuza ya yi “Ba wannan maganar”, haka kawai Bello ya ji bai gamsu da shi ba, saboda ai haka ya yi ta ce masa Deeni ba zai warke ba, yanzu kuma gashi nan sai yawo yake a status da buɗaɗɗen ido “Malam ni dai hankali na ba zai kwanta ba”, Malamin ya ce “Yanzu kana ina ne?”, Bello ya ce “Ina unguwarsu Habibah”, ya ce “Toh bayan Magrib ka shigo”, a zaƙe Bello ya ke, cewa ya yi “Yanzu fa Malam?”, ya ce “Akwai mutanen da na yi ma alƙawari, kuma suna hanyar zuwa ma”, ɗan jinjina kai Bello ya yi “Toh ba damuwa”, basu sake wata doguwar magana ba suka yi sallama.

Aje wayarsa ya yi sai maƙyaftai yake a cikin mota, gabaɗaya hankalinsa a mugun tashe yake, sai da ya yi nadamar buɗe data, don a nan ne ya ga abin da ya korar masa duk wata walwala.

Zuciya ce ta ce mashi “Toh ai gwara ma da ka sani, ta hakan ne zaka ɗauki mataki”, key ya yi ma motarsa ya bar unguwar, gidansa ya nufa, matarsa tana ganin sai huci ya ke bata bi ta kansa ba, saboda tunda ya sa sanwar auren Habiba ta ga chanji a wurinsa, da ta yi magana kuma sai ga aurenta ya fara tangaɗi, mafarin aka bata shawarar da idan ta ga ya shigo a firgice, toh ta riƙa ba shi space ya sha iska.

Duk da dai wannan shawarar ba a ko ina ta dace ba, a ƙa’ida idan mace ta ga mijinta ya dawo da fushi ba banza da shi zata yi ba, abin da zata yi shi ne ta yi amfani da salon da ya kamata wurin ganin wannan temper ta sauka, ba wai ta wofintar da shi ba, duk da wasu mazan a ƙyale su shi ya fi, toh amma dai ko an ƙyale su kamata ya yi a aikace a tsiri wani abu da zai sanya su farinciki.

Toh haka Maimunatu matar Bello ta yi, bedroom ta same sa zaune ya haɗe girar sama da ƙasa sai faɗuwar gaba yake, gefensa ta zauna “Angon Habibah, miji ga Maimunatu baban Abdallah, waye ya taɓa mana kai ne mu ɗauki mataki?”, sosai Bello yake son kirari, amma pressure yau ta sa ba abin da ke birge shi, kuma gami da yanzu duk abin da za ta yi mashi toh da wahala ta ƙayatar da shi, ƙwafa ya yi kafin ya ce “Yanayi ne kawai Uwar Abdallah, don haka kawai ki je waje ki yi hidimarki”, ko kaɗan Maimunatu bata ji daɗin gwalishe tan da ya yi ba, a ƙufule ta ke da shi, mafarin ta miƙe tare da faɗin “Allah ya kyauta”, hanyar fita ta nufa, a ranta tana faɗin “Allah ya sa gayyar banzar ma ta watse”, don abin da ranta ya bata shi ne faɗa ya yi da Habibah.

Shi kam tamkar zuciyarsa zata tarwatse saboda hassada, gani ya yi zai iya mutuwa a ɗaki, mafarin ya fito, a falo suka haɗu da Maimunatu, raɓawa ya yi ta gabanta ya wuce, yana jin Abdallah ɗansa na faɗin “Abba a dawo lafiya”, amma bai kalle sa ba, bare ya iya ba shi amsa, Maimunatu kuwa ta ji haushi “Can da yawarka”, ta faɗa tare da yi ma ɗanta maganar da zata ɗaukar mashi hankali.

Shi kuwa da ya ga zagaye-zagayen bai yi sai ya fice daga gidan, unguwarsu Malam Yahuza ya nufa da niyyar yin magrib a can, lokacin da ya isa har an fara kiran sallah, masallaci ya nufa, ana gama sallah ya kira shi tare da neman iznin zuwa, “Eh, zaka iya shigowa”, bai yi wata doguwar addu’a ba ya tashi.

Wasu mata ya gani sun fito tare da Malamin, gaisawa ya yi da su, sannan ya koma gefe. Lallai abin da zai sa Bello ya ga mata, kuma ya iya ɗauke masu kai ba ƙarami bane, ganin haka ya sa Malaminsa saurin sallamar matan suka tafi.

“Barka da zuwa Dr.”, Ya faɗa tare da miƙa ma Bello hannu, Bello ya ce “Barka dai Malam, ya aka ji da jama’a?”, Ya ce “Lafiya lau Alhamdulillah.”, ciki suka ƙarasa suna ƴan maganganunsu na masu alaƙa da juna. Bayan sun zauna ne Bello ya ce “Malam tun ɗazu na so zuwa, toh don ka ce in jira ne kawai”, Zama Malam Yahuza ya gyara a kan buzunsa tare da faɗin “Ka san jama’a, yanzu waɗannan matan da ka gani sun fi mako ɗaya suna son zuwa, toh ba zama, ga shi mutane ta ko ina zuwa suke.”

In dai a harkar Malanta ce, toh Malam Yahuza ba daga baya ba, garuruwa da dama shigowa suke don ganin sa, kuma shi Bellon ya san haka, uzuri ya yi masa ta hanyar faɗin “Ai kuna ƙoƙari Malam, sai dai mu ce Allah ya ƙara ɗaukaka”, Malam Yahuza ya ce “Amiiiiin ya Allah”, duba ya maida a kan ƙasar da ke zube gabansa cikin wani farantin katako kafin ya ce “Me ke tafe da kai?”, Sai da Bello ya tattaro dukkan nutsuwarsa kafin ya ce “Maganar Deeni ce..”, tarar numfashin Bello ya yi ta hanyar ɗaga masa hannu “Na gani, ya warke ko kamar yadda ka faɗa a ɗazu?”, cike da ƙunar rai Bello ya ce “Ƙwarai Malam, babban tashin hankalina kenan”, duban sa Malam Yahuza ya yi yana ta zare ido “Deeni yana addu’a sosai, ka san kuma addu’a tana sauya al’amura, sannan mahaifyarsa gata nan da ranta, itama kullum yi masa addu’a take, ka san kuma addu’ar uwa kamar ya kan wuƙa ne, don haka warkewarsa ba wani abun mamaki ne ba, tunda komai yana a hannun Allah, kuma shi suka roƙa.”

Jugum Bello ya yi har sai da Malam Yahuza ya kai ƙarshe, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke “Gaskiya ne, shi ɗin gwanin addu’a ne, toh amma batun aikinsa ba, zai koma..?”

<< Mutuwar Tsaye 39

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×