Malam Yahuza ya ce “Idan Allah ya ga dama zai iya komawa aikinsa mana, tunda lamarin a hannun Allah ya ke, ba a wurinmu ba”, kan ka ce me kuwa Bello ya ƙara rikicewa, saboda tunda har idanun Deeni suka buɗe, toh abu ne mai sauƙi a wurin Allah kamar yadda Malam Yahuza ya faɗa, duk da shi Bellon bai cika kai kukansa wurin Allah ba, ya fi tafiya wurin Malamai, waɗanda su ma a wurin Allahn suke nema, toh amma ya san Allah zai iya komai.
“Malam dan girman Allah ka taimaka mani, don muddin Deeni ya karɓi kujerarsa na shiga uku”, kamar Bello zai yi kuka ya riƙa yi ma Malam Yahuza magiya, saboda ya san ta’asar da yake shukawa a asibitin, kuma muddin Deeni ya dawo, toh kashinsa ya bushe, duk da dai Deeni na da sauƙin kai, toh amma ba zai ga almundahana ba ya yi shiru, kuma wannan tonawar ko shakka babu sai ta zama silar barin aikin Bello, shi kuma da ya bar aikinsa, gwara ma ya mutu, don bai dogara da komai ba sai wannan aiki, shi ya sa duk inda handama da babakere suke to da hannunsa a ciki, burinsa kawai ya wadata kansa ta yadda ba zai yi talauci ba, ya manta kuma wanda ke cin haram ba shi da wani matsayi a wurin Allah.
Ƙuri Malam Yahuza ya yi mashi, duk da cewar shi Malami tsibbu ne, amma yana mamakin irin muguntar Bello, saboda a iya binciken da yayi ma Deeni, ya fahimci shi ɗin ba mugu bane, bare har wani ya ce zai ɗauki fansa a kansa, asali ma burinsa shi ne duk wanda ke tare da shi ya yi farinciki. Tambayar Bello ya yi “Yanzu ya kake so a yi?”, Kamar zai yi kuka ya ba shi amsa “So nake na dauwama a kan kujerata”, Malam Yahuza ya ce “Ai babu mai dauwama a kan kujerar mulki sai Allah”, Bello ya ce “Na sani ai, ina nufin na daɗe ina iko akan kujerar, kuma ko da wani zai karɓa, toh ya kasance wani ne ba Deeni ba”, Malam Yahuza ya ce ” Saboda me shi Deenin baka so ya karɓa”, Bello ya ce “Ka sani ai Malam, ni bana son shi ne, na tsane shi, ban ƙi ba ma ya mutu in huta.”
Dariyar mugunta Malam Yahuza ya yi “Toh an gama, zan maka aiki…”, tarbar numfashinsa Bello ya yi yana ƴar dariyar jin daɗi, don ya san Malam Yahuza cika aiki ne, cewa ya yi “Yauwa Malam, a taimaka don Allah”, Malam Yahuza ya ce “Na ce baka da matsala, yanzu nutsuwarka nake so.”
Tamkar ƙaramin Yaro haka Bello ya gyara zama tare da harɗe ƙafafu, tattaro dukkan nutsuwarsa ya yi haɗe da sauke ji da ganinsa a wurin Malam Yahuza, burinsa kawai ya ji me zai faɗa.
“Zan yi maka aiki kamar yanda na faɗa”, Malam Yahuza ya faɗa, lokaci ɗaya kuma yana ɗan duba ƙasar nan da ke zube a gabansa, shi dai Bello bai ce komai ba, sai dai ya ci-gaba da sauraron sa lokacin da yake faɗin “Sai dai a wannan karon ba aikin makaranta ne zamu yi ba, ka fahimce Ni?”, Kai Bello ya ɗaga tare da faɗin “Eh Malam, sai dai ba sosai na fahimta ba”, jinjina kai Malam Yahuza ya yi, “A wannan karon aikin na surkulle ne”, karɓe shi Bello ya yi “Ai Malam ko na ƙulumboto ne zan iya kashe ko nawa ne in dai buƙatuna zasu biya.”
Dariya sosai maganar Bello ta ba Malam Yahuza, saboda a ƙasan ransa shirin haƙa masa tarkon cin kuɗinsa yake, duk da dagaske ne zai yi masa aikin, cewa ya yi “Ai da surkulle, da ƙulumboton duk ɗaya ne a wurinmu, don ba wanda mutum zai ji daɗi idan mun yi masa shi”, ran Bello cike da farinciki ya ce “Yauwa Malam, ina sauraron ka.”
Malam Yahuza ya ce “Abin farko da zan yi maka shi ne, za a cire tunaninsa a zukatan duk wasu masu faɗa a ji na asibitinku, ma’ana za a mantar da su shi, tunda ai sai yana ransu ne har zasu kawo maganarsa ko?”, jinjina kai Bello ya yi “Ƙwarai Malam, musamman former MD ɗin mu”, Malam Yahuza ya ce “Shi ne farkon wanda zan fara kamawa ai, don zai iya baka matsala wannan mutumin da kake gani”, Bello ya ce “Na sani Malam, mutumin nan baya ƙauna ta”, Malam Yahuza ya ce “Za a yi maka maganin sa da iznin Allah”, russuna kai Bello ya yi “Godiya nake Malam”, Malam Yahuza ya ce “Kada ka damu, shi kuma zamu sakar masa matsaloli, waɗanda zasu shagaltar da shi daga aikinsa, ga lafiyar, amma yana cikin damuwar da ba ta aikin yake ba”, wannan magana ta yi ma Bello daɗi ba kaɗan ba, cewa ya yi “Allah ya taimaki Malam, ina godiya fa”, kan Malam Yahuza na ƙara girma ya ce “Ai sai ka ji na ukun ma tukuna zaka yi godiya”, gyara zama Bello ya yi”Ina jin ka Malam”, Malam Yahuza ya ce “Wannan aikin akan kujerar ne zamu yi, zamu asirce ta, ta yadda duk wanda ya yi gigin hawan ta idan ba kai ba, toh mutuwa ce zai yi.”
Daɗi kamar zai kashe Bello, saboda ko kaɗan ba imani a tare da shi, cewa ya yi “Toh Malam wannan aikin zai ci nawa?”, Malam Yahuza na jin maganar kuɗi ya murtuke fuska, ta yadda Bello zai fahimci babu wasa ko yaudara a cikin maganar “Ka ga aikin kala uku ne ko?”, Bello ya ce “Eh Malam”, Malam Yahuza ya ce “Toh a faɗa maka kayan aikin zaka siyo?”, girgiza kai Bello ya yi “A’a Malam, a faɗi kuɗin dai, zan bada ko nawa ne”, ɗan shiru Malam Yahuza ya yi yana lissafi a ransa, daga bisani ya ce “Dubu ɗari huɗu da saba’in ne, saboda za a siyi rago da kaji birci na sadaka, ga tauraruka da ƴan binne-binnen da za a yi, ina fatan ka fahimta”, Bello ya ce “Na fahimta Malam, toh kuɗin aikin fa?”, Malam Yahuza ya ce duka da aikin da kayan aikin ka kawo dubu ɗari biyar da Hamsin”, ko ɗar Bello bai ji ba a ransa, saboda ya zata aikin ma ya fi haka, saboda ya san waye Malam Yahuza, mata da ƴan siyasa sun ɓata shi da son kuɗi.
“Toh ba damuwa Malam, a turo ta asalin bakinka da nake da shi?”, Malam Yahuza na murna a ransa ya ce “Eh Dr, ka turo”, waya bello ya zaro dake aljihun gaba ya shiga daddanawa, cikin ƙasa da minti biyar Malam Yahuza ya ji dirar alert a wayarsa, Bello ya ce “Gasu nan Malam”, da ɗan sauri Malam Yahuza ya duba, alert ne guda biyu, ɗaya dubu dari uku, ɗayan kuma dubu ɗari huɗu, total balance na wanda Bello ya turo mashi ya kama dubu ɗari bakwai, da hanzari ya dubi Bello “Na ga ɗari bakwai”, Bello ya ce “Eh Malam, idan wasu kuɗin sun shigo zan ƙaro maka uku”, Malam Yahuza ya ce “Million ɗaya kenan fa”, Bello ya ce “Ai ka wuce haka”, Malam Yahuza ya ce “Nagode Dr. Allah ya sa mu fita kunyar juna”, Bello ya ce “Amiiiiin Malam, ni ne da godiya.”
Hira sosai suka dasa, Bello bai bar wurin ba sai da zuciyarsa ta gamsu da ko da Deeni ya dawo, to ba zai yi tasirin da zame masa barazana ba. Ya manta da Allah ne mai kowa mai komai, idan ya yi nufin ɗaukaka darajar bawa, ko da duniya zata taru don hana bawan nan ɗaukakuwa ba za su iya ba.
Duk wanda ya rasa uwa a taya shi jaje, domin ita kaɗai ce ke da dogon nazari ga rayuwar ɗanta, musamman a kan abin da zai kawo mashi cigaba, ko kuma naƙasu. A lokacin da duk wani mai son Deeni yake murna da samun lafiyarsa, Hajiyarsu kuwa, bayan murna, toh ta shiga tunanin akwai maƙiya fa, waɗanda su kuma suna can baƙinciki suke da samun lafiyarsa, sannan a halin mugunta na ɗan adam, zasu iya yin wani abu da zai iya cutar da shi, ko da kuwa da harshe ne, duk da sai idan Allah ya nufa ne kaɗai zasu iya cutar da shi.
Sadaka maganin dukkan bala’i, a don haka ne ma ta ciri kuɗi a aljihunta domin shirya sadakar abinci, su Hajiya Ummah sun ce ta bari zasu ɗauki nauyin sadakar, amma ta ce sai dai su kawo gudunmawa a ƙara, tunda shi aikin Alkhairi ai baya yin yawa, haka kuma aka yi.
Kuɗi suka biya aka yi musu abincin tare da kimtsa shi a cikin take away, sannan aka kawo shi gidan. Shelar sadaka aka yi, aikuwa sai ga mutane kamar kiyashi, ta ko ina ɓullowa suke domin karɓar wannan jallof rice da aka shirya musu domin faranta ran mabukata. Kuma duk wanda ya karɓa sai ya ce “Allah ya biya bukata.”
Aikuwa bayan kowa ya watse ne, inda ya rage daga ita sai ƴaƴanta, sai kuma wasu ƴan kaɗan a danginsu ne ta ce “Toh mu yi addu’a ko?”
Hannu duk suka ɗaga sama, daga kan kujerar da take ta jagorance su a addu’a ta hanyar faɗin “Alhamdulillah, Tsira da aminci su ƙara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, Ya Allah, ina tawassuli da sunayenka tsarkaka, waɗannan da muka sani, da ma waɗanda bamu sani ba, da ƙara mana lafiya da zama lafiya….”
Deeni na zaune Salma ta kira a wayar Lalu da bar masa, tare da ce mishi ya duba saƙo, ko da dai baya gani sosai, amma tuni ya saita baƙin gilashin da aka ba shi a hospital ɗin, WhatsApp ya shiga duk a wayar Lalu, vedios ne ya gani guda biyu, yana playin ya ga yadda mutane ke ta shige da fice suna karɓar abinci, kuma kowanne fuskarsa ɗauke da fara’a.
“Masha Allah”, ya faɗa a ransa, ɗayan vedion ya buɗe, Hajiyarsa ya gani mutane zagaye da ita, ta ɗaga hannu tana yi mashi addu’ar neman kariya a wurin Allah.
Wasu ƙwallah ne suka ɓulɓulo a idanunsa, a bayyane ya ce “Uwa mai daɗi”, cikin ransa yana ƙara gode ma Allah da ya sa mahaifiyarsa na da rai, kuma ƙarfin addu’arta na daga cikin abin da ya sa ya samu lafiya.
“Allah ka saka ma mahaifiyata da Alkhairi Amiin, sannan ka ƙara mata lafiya da nisan kwana masu albarka Amiin.”
Kiran Salma ya yi ta voice call, bayan ta ɗaga ne ya ce “Na ga ƙoƙarin Hajiyarmu Salma”, daga can Salma ta ce “Ya ka ji a ranka?”, ya ce “Na yi farincikin da baya misaltawa Salma, haƙiƙa duk wanda ya rasa uwa a yi masa jaje” ta ce “Wallahi kuwa Yaya, ai baka ga yadda take ta murna ba”, ya ce “Na san zata yi murna sosai, Allah dai ya ƙara mata lafiya da nisan kwana masu albarka”, Salma ta ce “Amiiiiin Yaya”, ɗorawa ta yi da “Sai shirin dawowa ko?”, ya ce “Eh, amma sun tsaida mu fa, saboda ba irin can ɗin nan nake gani ba, idan abu na nesa bana gani, sannan na kusan ma wani lokaci sai na riƙa gani biyu-biyu, wani lokaci kuma dishi-dishi.”
Da ƴar damuwa a ranta ta ambaye shi “Toh za a sake aikin ne?”, ya ce “Haka suka faɗa, amma gaskiya bana so Salma, hakan ma Alhamdulillah, zan yi manage, don ya fi a ce ba a gani.”
Muryar Salma a raunane ta ce “Amma Yaya da ka bari an sake aikin”, ya ce “Salma ki barni kawai, an cakuli idanuna da yawa”, ta ce “Gaskiya kuma haka ne”, ya ce “Toh kin gani, hakan ma Nagode ma Allah”, Fatan ƙaruwar lafiya ta yi nashi, bayan ya gode mata ne, ya ce kuma kada ta faɗa ma Hajiyarsa cewar ba sosai ya warke ba.
Lalu na dawowa Deeni ya miƙa masa wayar “Duba ka ga abin Alkhairin da Hajjah ta yi”, da ɗan hanzari Lalu ya ɗauki wayar, Sunan Salma ya buɗe tare da playing vedion, yana kallo yana dariyar farin ciki, kafin ya buɗe ɗaya vedion ne ya dubi Deeni “Wannan duk na moy”, Deeni ya ce “Na farinciki ne ɗanta ya samu lafiya”, Lalu ya ce “Allah Sarki, Allah ya karɓa”, Deeni ya ce “Amiiiiin Farouk.”
Ɗayan video Lalu ya kalla, aikuwa sai da ya yi kuka, bayan ya gama gani ne ya dubi Deeni “Toh da baka warke ba fa?”, Deeni ya ce “Nima tambayar da nake yi ma kaina kenan”, kai Lalu ya girgiza “Allah ya ƙara maka lafiya, ya kuma kyauta gaba”, saboda ya san yadda Hajiyarsu ta damu da lafiyar Deeni.
Batun su Asma’u ya yi mashi “Sun daɗe da tafiya?”, ya tambaye shi, Deeni ya ce “Eh”, a ɗan yamutse ya ce “Ai gwara su tafi ma”, Deeni ya ce “Saboda me ka ce haka,?”, Lalu ya ce “Toh sai wani shige ma miji take, ko kunyar mu ma bata ji”, Dariya Deeni ya yi, saboda ya fahimci Asma’u ta fara sanin daɗin miji, cewa ya yi “Kada ka ga laifinta fa, yarinya ta san daɗin mijinta”, baki Lalu ya taɓe “Uhm, toh muma Allah ya aurar da mu”, Deeni ya ce “Yauwa, haka ya kamata ka ce.”
Kamar yadda Deeni ya ce Asma’u ta san daɗin mijinta, toh haka ne, don kuwa Bashir sai da ya karanci me ta fi so a zamantakewar aure, sannan ya cigaba da bata kulawar da ta dace. ita kuwa ji take tamkar ta fi kowace mace sa’ar miji, mafarin ta fara wata ƴar ƙiba wadda bata lura da ita ba.
Shigowar Bashir a ɗakin ne ta ga ya ƙure ta da idanun tare da harɗe hannu a ƙirji, cike da takun ƙasaita ta je gabanshi, warware mashi hannu ta yi tare da shigewa a jikinsa, “Oyoyo my sweet hanny”, tamkar zai maida ta a ciki ya ce “Thank you Beb”, ɗan shiru suka yi, kafin daga bisani Bashir ya raɗa mata “Baki tambaye ni kallon me nake maki ba”, ɗago da kanta ta yi ta ce “Toh na tambaye ka Hanny”, sai da ya sumbaci lips ɗinta sannan ya ce “Na ga kin yi ƙiba ne”, idanu ta zaro “Dan Allah na yi ƙiba?”, ya ce “Da gaske mana”, ranta cike da murna ta ce “Ai kai ne ka iya kulawa”, ya ce “Ko Beb?”, ta ce “Yeah.”
Saɓarta ya yi suna dariya, bai dire da ita ko ina ba sai kan gado, rumfa ya yi mata tare da faɗin “Wai nan ma ban ba ki babbar kulawa ba ko?”, cike da kissa ta ce”Toh ba kai ne ka ƙiya ba”, cewa ya yi “A’a ke ce kike tsoro fa”, langaɓe kai ta yi “Ai na dena tsoron”, ya ce “Allah ko?”, ta ce “Uhmm”, bata ankare ba ta ji cakulkuli “To ki ba ni time, zamu haɗe..”, dariya su duka suka yi, bai bari rahar ta yi nisa ba ya sauka a kan gadon, bare har ya shiga wani yanayi, don ya ɗaukar ma ransa sai su Deeni sun koma gida ko yana yi mata irin waccan kulawar.
Marairaice fuska ta yi daga kwancen ta ce”Ina zaka je Please?”, ya ce “Zan yi wani aiki ne, ya ƙarashe maganar yana kallon system ɗinsa da ke kan table, cewa ta yi “Baka ga na yi shirin barci ba?”, duban ta ya yi, tabbas idan so samu ne, toh ya zo a kusa da ita, amma sai ya ce “Ben, yau kwanan aiki zan yi”, da yake tana saurin fushi sai ta turo baki “Shikenan, ka yi aikin”, ta ƙarashe maganar tare da gyara kwanciya a kan kafaɗarta, dariya yayi gami da hawa kan gadon, da raɗa ya ce mata “Beb, nima ina son abin da kike so, amma bana son su Yaya su gane.”
Baki ta buɗe tana kallon da kafin ta ce “Iyeeee! To sauka ka yi aikinka dan Allah, ni ban kai inda ka je ba”, sosai maganarta ta sa shi dariya. Ƙin sauka daga kan gadon ya yi har sai da suka fahimci juna. Tare suka sauka, tana ba shi labari, shi kuma yana aiki a system.