Skip to content
Part 42 of 45 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Aiki mai yawa Bashir ya yi, sai da ya lura da alamun Asma’u ta fara gajiya ne ya ɗan dube ta “Ya kamata mu yi barci ko?”, girgiza kai ta yi “A’a ka ƙarasa aikin mana”, matsar da system ɗin ya yi a gefe kafin ya ce “Ke dai kada na shiga haƙƙinki, aikin na da yawa sosai.”

In don ta Asma’u ne ma ba zai yi aikin ba, toh amma lura da bukatuwar aikin ne ya sa ta dagewa a kan ya gama, bai biye mata ba ya rufe system ɗin ya maida ta mazauninta, wurin Asma’u da har yanzu take zaune ya dawo, hannu ya miƙa mata “Mu je mu yi barci”, ruƙo shi ta yi, in da ya taimaka mata ta miƙe, hannuwansu cikin na juna suka ƙarasa wurin gadon, “Ki kwanta, zan shiga banɗaki”, ya faɗa tare da sakar mata hannu.

Zama ta yi a gefen gadon, yana fitowa itama ta shiga ta fito, kashe fitilun ɗakin Bashir yi sai dim light da ke kan stool. Tamkar za su mayar da juna a ciki suka kwanta, sai da suka nishaɗantu sannan suka yi barci.

Washegari da safe suna ta shirin zuwa wurin Deeni a asibiti ne Bashir ya lura da wani nishaɗi na musamman da Asma’u ke yi, jawo ta ya yi ta faɗo jikinsa “Ke, wannan sabon nishaɗin fa?”, ya tambaye ta cike da zolaya.

Amsar abin da ke ranta ta ba shi “Na samun lafiyar Yaya ne, na rasa me zan yi na Alkhairi domin nuna godiya ta ga Allah da ya warkar mani da ɗan’uwana”, tabbas ko bata faɗa ba Bashir ya san dama dole ta yi murna, toh amma bai yi zaton tana da wani ƙudiri na yi ma Allah godiya ba.

Duk abin da zai sanya ta farinciki ya ɗaukar ma ransa zai yi mata madamar bai saɓa ma Ubangiji ba, cewa ya yi “Kin san me zaki yi ma Ubangiji godiya da shi?”, idanunta cikin nashi ta ce “A’a”, ya ce “Ka’aba zaki je ki yi Ɗawafi tare da gode ma Allah”, cikin rashin fahimta ta ce “Ka’aba?”, ya ce “Eh, idan su Yaya zasu tafi, toh zamu raka su Saudiyya, idan zasu wuce gida sai mu kuma mu dawo nan India.”

Asma’u bata taɓa kawo ma ranta haka ba, da mamaki ta ce “Dan Allah da gaske kake?”, ya ce “Da gaske mana, ko ba kya son zuwa?”, sai da ta ɗan buɗe baki kana ta ce “Ina so mana”, ya ce “Toh yadda na ce haka za a yi Insha Allahu.”

Wannan shi ne cikar buri, wanda idan Allah ya so toh ba mahani, tunda gashi dai zata je Makkah da Madina, su ne manyan ƙasashen da take so bayan India, rungume shi ta yi tana faɗin “Nagode sosai Mijina da cika mani burina”, shiru ta yi saboda ƙwallan daɗi da suka cika mata idanu, “No my wife, ki bari”, ya faɗa cikin sassauta murya tare girgiza kai, kasa daina ƙwallan ta yi, sai ma ta cusa kanta a ƙirjinsa tana faɗin “Thank you my jaan, I really love you”, murmushin mai cike da ƙaunar ta ya yi kafin ya ya ce “Thanks and love you too my wife”, ƴar soyayyarsu suka sha a tsayen, daga bisani suka tafi asibitin.

Lalu na zaune daga wajen ɗakin da Deeni ke ciki ya hango su, yadda hannuwansu ke cikin na juna ne ya birge shi tare da kwaɗaita mashi son aure a ransa, ta wani bangaren kuma murna ya taya ƙanwarsa bisa ga sa’ar mijin auren da ta yi, saboda ya lura da yadda Bashir ke bata kulawa, wadda ta sanya ta kyakkyawan chanji a lokaci guda. “Allah nima ka bani mata ta gari, sannan ka ba ni ikon kulawa da ita Ya Allah”, addu’ar da ya yi ma kansa kenan.

Miƙewa ya yi lokacin da suka ƙaraso tare da miƙa ma Bashir hannu, cike da mutunta juna suka gaisa, Asma’u ma gaishe shi ta yi da “Uncle Lalu ina kwana”, yana ƴar dariya ya amsa da “An tashi lafiya”, saboda sai da suka zo India ne ta fara gaishe shi, shi ya sa ya ke mata dariya, bayan ta amsa ne suka zauna a kan kujerun da ke jere a wurin, duk da Lalu bai faɗa ba, amma sun san Doctors ne a wurin Deeni.

Hirar da Lalu ya fi so Bashir ya ɗauko mashi wato crypto, inda ya sako maganar Pi ta hanyar faɗin “Ka ga yadda Pi ya shiga market ko?”, Lalu na jin haka ya ƙara faɗaɗa fuskarsa, domin an taɓo mashi inda ya ke yi mashi ƙaiƙayi, musamman shi da ya tara Pi sama da dubu hamsin, banda wanda ya siya a hannun jama’a, cewa ya yi “Na gani, ai Alhamdulillah kawai zamu ce, don alamu sun nuna lokacin arzikinmu ya zo”, Bashir ya ce “Insha Allahu, don shi ma a harkar crypto ba daga baya ba, kuma ya samu Pi sosai.

Asma’u da ta san fafutukar da Lalu ya yi ma Pi ta ce “Uncle Lalu Dala nawa ka samu?”, ƴar harara ya wurga mata haɗe da dariya “Ba sai kin ji ba”, ta ce “Don Allah, ko don kada in ce ka bani wani abu”, Lalu ya ce “Toh dama ai ba zan baki ba, saboda kema kina da shi”, tana dariya ta ce “Ai bai kai naka yawa ba”, ya ce “Ba dai kina da shi ba?”, ta ce “Ai na rufe shi”, Bashir ne ya shiga zancen “Kin rufe da gaske?”, Lalu ne ya bashi amsa “Na three years ma don son kuɗi”, Bashir na dariya ya ce “Lallai Asma’u, da dogon buri kike”, itama tana dariya ta ce “Toh kun ga laifina?”, Bashir ya ce “A,’a, Allah ya sa rabo ne”, suka ce “Amiiiiin.”

Amsar tambayar Asma’u ne Lalu ya faɗa “A wanda na fitar a kasuwa na tsira da seven hundred USDT, kuma yana fara ƙasa na sake siyen wani”, Bashir ya ce “Da kyau, Allah ya dafa mana” suka ce “Amiiiiin.” Hirar su suka sha, a nan Har lalu ya yi reffaring ɗinsu a kan wasu airdrops da ake kyautata zaton zasu kawo Alkhairi.

Suna nan zaune Doctor Niranjana ta fito, cike da girmamawa suka gaida juna, sannan ta yi musu bayanin matakan da suke so Deeni ya bi, tunda ya kafe a kan shi ba za a sake taɓa mashi ido ba, hakan ma ya gode ma Allah. Sosai suka gamsu da zantukan ta, domin idan ya bi su, ko bai warke duka ba, toh zai samu lafiya.

Bayan ta wuce ne suka shiga ciki, zaune suka taras da Deeni, ya jingina bayansa da pillon da yake a kai, jin shigowar su ne ya sa shi buɗe idanunsa da suka ƙanƙance saboda feeling matarsa.

“Ya dai?”, Lalu ya tambaye shi, saboda yanayinsa ya bayyana damuwa a tare da shi. Ɗan wartsakewa ya yi haɗe da tashi zaune “Ƙalau nake, kawai na faɗa kogon tunani ne”, tambayarshi Lalu ya yi “Tunanin me?”, ya ce “Na matata, ina kewar ta sosai”, sosai suka yi mamakin ƙin jin kunyarsu da ya yi, tabbas toh abin ya ci tura “Allah ya sa a dawo maka da ita”, in ji Bashir da ke ta tausayinsa, Deeni ya ce “Amiiiiin ya Allah.”

Zama suka yi tare da gaisawa da juna, a nan kuma ya faɗa masu dokokin da Dr. Niranjana ta kindaya mashi cewar ya rage damuwa a ransa, domin tana kawo hawan jini, shi kuma hawan jini yana taɓa idanu, sannan ya guji kallon screen kowane iri ne ba tare da kariyar gilashi ba, sannan ya kula da magungunan da yake a kai, idan ya riƙe wannan toh zai zauna lafiya.

Sannan idan da dare ne ya kiyayi duhu, tunda ko da rana ba sosai yake gani ba, bare kuma da dare, don haka zai iya faɗa ma abin da bai kamata ba har ya cutu.

Bashir ne ya tarbi numfashinsa da faɗin “Allah kuwa Yaya da ka yarda an sake yi maka aikin, tunda ga mu a cikin Asibitin”, girgiza kai Deeni ya yi “Kai dai a bar shi kawai Bashir, na haƙura”, Bashir ya ce “Allah ya ƙara lafiya”, Deeni ya ce “Amiiiiin ya Allah” ɗorawa ya yi da faɗin “Ni gida ma nake so, na ƙagara su sallame ni”, Lalu da karɓe da “Haɗa da ni nan”, ƴar dariya Bashir ya yi “Toh mu da muka zo zama mu ce me?”, Lalu ya ce “Aikuwa ba, ai ina tausayinku, ni bana jin zan iya zuwa wata ƙasa in zauna”, Deeni ya ce “Kamawa take ai, aiki ko sana’a duk suna iya sawa mutum ya koma wani gari ko wata ƙasa da zama”, rausaya kai Bashir ya yi “Toh ka ji magana Lalu, kuma ai idan kana da aure zaka ji kewar gidan kaɗan ce, ko ba haka ba ƴar gudaliya”, ya ƙarashe maganar yana duban Asma’u haɗe da dariya.

Hararar wasa Asma’u ta yi mashi tana dariya itama, Lalu ya ce “Munafuka, kika yi shiru”, sosai maganarshi ta sa su dariya har da riƙe ciki.

Deeni ne ya shigar mata “Farouk bama son sanya ido fa”, Bashir ya ce “Rabu da shi dai, kamar gobe ne zamu rama.”

Bayan sun gama rahar ne Bashir ya tambaye shi ko sun faɗi ranar da za a sallame shi, ya ce “Eh ta faɗa, next week Insha Allah”, Asma’u na jin haka ta yunƙura da nufin yi masu albishir ta hanyar faɗin “Ka san me Yaya?”, Deeni ya ce “Sai kin faɗa auta”, tamkar ƙaramar yarinya ta ce “Idan zaku tafi har Saudiyya zamu raka ku”, da mamaki ya ce “Da gaske?” Ta ce “Allah kuwa, ko Uncle Bash”, Bashir ya ce “Kwarai kuwa Insha Allahu, zamu raka ku, daga nan mu yi Ɗawafi, mu wuce Madina mu gaida Manzo Sallallahu alaihi Wasallam.”

Amsawa su duka suka yi da “Sallallahu alaihi Wasallama”, sannan Deeni ya amsa da faɗin “Da kyau, Allah ya cigaba da shige mana gaba Amiiiin.”

A bangaren tafiyar su Deena Umarah kuwa, tuni Alhaji Lawan ya gama tsara musu tafiyarsu zuwa Saudiyya, tun da abin na masu ƙumbar susa ne, sai dai an ɗaga tafiyar sai goma ga watan Ramadan da ke tafe, idan sun je sai su ƙarasa azumin a can, zuwa bayan sallah sai su dawo idan Allah ya nufa.

Duk da tafiyar ta fi falala a cikin watan Ramadan, toh amma son ta haɗu da Deeni ne ya sa ta ji dama a yi tafiyar a yanzu, sai dai bata da wannan damar, tunda nauyin tafiyar ba a hannunta yake ba. 

Ta so ta yi ma Deeni maganar, amma bata samu dama ba sai da dare, sakamakon shige da ficen da suka yi a kan makarantar ta da zata koma. Bayan ta tabbatar da barcin Raihan ne itama ta rage hasken fitilar ɗakin zuwa dim light, saboda bata iya barci cikin duhu, kishingiɗawa ta yi a kan gadonta tare da Bismillah a bakinta, wayarta da ke a hannu ta danna power tare shiga WhatsApp kai tsaye, inda dama tuni fatar wayar a kunne take.

“Ina kika shige ne?”, saƙon voice na Deeni kenan da ta ci karo da shi, banda jerin missed calls ɗin da ya jera mata.

Bata tsaya ɓata lokaci ba wurin yi masa reply da voice note, calling ɗinsa ta yi, aikuwa kamar wanda ke zaman jiran ta ya ɗaga kiran daga yin sallama ya ɗora da tambayar “Ina kika shige ne?”, wani irin sanyi ta ji a ranta, domin haka take so ta ji yana kewar ta, sai da ta narke a jikin pillow kana ta ce “Na je registration na JAMB ne”, daga can ya ce “Masha Allah, kin yi ko?”, ta ce “Eh, tare da Mommah muka je, daga can muka je unguwa”, ya ce “Okay, ai na yi missing ɗinki fa”, ta ce “Koh?” ya ce “Sosai ma, ɗazu tunaninki ya hana ni fahimtar me doctor take faɗa, sai ta yi surutun ta gaji sai in tambaye ta me ta ce?, aikuwa ta rufe ni da faɗa kamar ita ce Hajiyarmu.”

 

Sosai Deena ta yi mashi dariya, ya ce “Au dariya kike mani?”, ta ce “Faɗan da ka ce ta yi maka ne ya sanya ni dariya”, yana dariyar shima ya ce”Na rantse kuwa, ni ma sai da na yi ma kaina dariya”, Deena ta ce “Matar tana ƙaunar ka, bata son ka sake shiga damuwa”, Deeni ya ce “Gaskiya haka ne”, zolaya ya ɗaura da ita ta hanyar faɗin “Kin ga da zata bani ƴarta, sai in yi maki ƙanwa mu dawo Nigeria da ita”, dariya ta tuntsire da ita, saboda ta san abun ba mai yiwuwa ne ba, da mamakinsa ya ce “Dariya kike ko?”, saboda ya san halinta na kishin tsiya, ta ce “Toh me zan yi idan ba dariya ba”, yana dariya ya ce “Muguwa, don kin san abin ba zai yiwu ba ko?”, ta ce “Idan ma zai yiwu ayi mu gani”, ya ce “Me kika taka?”, ta ce “Ba sai ka ji ba”, ya ce “Ban san ki da bin Malamai ba fa Deedee”, ta ce “Ai ni Malamina shi ne Allah”, ya ce “Gaskiya ne my Dee, shi ya sa nake ƙaunar ki sosai.”

Bayan sun gama rahar ne ya tambaye ta maganar tafiyarsu Umara, faɗa mashi ta yi an ɗaga, sai goma ga watan Ramadan idan Allah ya kai mu, ya ji daɗi kuwa sosai, domin shi ma plan ɗinsa kenan idan sun je Saudiyya shi ma sai bayan Sallah, cewa ya yi “Zamu haɗu kenan”, ta ce “Insha Allahu, ai duk inda kake sai na nemo ka”, ya ce “Idan Mommah ta bar ki ko?”, ta ce “Ai na rantse ko bata bari ba”, ya ce “Bari rantsuwa fa”, ta ce “Na rantse, baka san me na taka a kanka ba ne shi ya sa”, sai da ya gama dariyarsa sannan ya ce “Deena! Yaushe kika zaburen ne haka?”, itama dariyar ta yi kafin ta ce “Ni ma ban sani ba, amma zan iya tuna raba ni da kai da aka yi ne ya fara ƙeƙasar mani da zuciya”, cikin sanyin murya ta ƙarashe maganar.

Tana jin yadda ya sassauta murya kafin ya ce “Gaskiya ne Deena, Insha Allahu zamu sake yin aure”, ta ce “Allah ya sa”, ya ce “Amin my Dee.”

Shiru suka ɗan yi, Deena ta ce “Ka san na ɗan fara ƴar ƙiba, sai Mommah ta ce na samu lafiya, bata san murnar zan haɗu da kai a Saudiyya ne ya sa na rage damuwa ba”, shiru ta ji ya yi, ɗan duba wayar ta yi ko kiran ya tsinke, amma ta ga yana tafiya “Yaya”, ta ambaci sunansa.

Amsawa ya yi da “Ina jin ki”, ta ce “Ka yi shiru ne”, ya ce “Kin san me ya sa na yi shiru?”, daga kwancen da girgiza kai “A’a”, ya ce “Tausayin ki ne, yanzu haka ƙwalla ke fita idanuna”, mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, take itama hawaye suka ɓuɓɓugo mata a idanu, murya a sarƙe ta ce “Allah Sarki Yaya, ina ƙaunar ka”, ya ce “Ni ma ina ƙaunar ki Dee ɗina, Allah ya bamu mafita ta Alkhairi”, ta ce “Amiiiiin ya Allah”, sun sha hira sosai, daga bisani suka yi sallama, Deena na aje waya ta sauko daga kan gado, banɗaki ta shiga ta yi alwala, tana fitowa ta shimfiɗa prayer mat ta kabbara sallar Nafila.

 

 

 

 

 

 

 

<< Mutuwar Tsaye 41Mutuwar Tsaye 43 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×