Deena ta yarda sallar Nafila na maganin dukkan damuwa, shi ya sa ta riƙe ta sosai, ba dare ba rana take yin ta, kuma cikin ikon Allah tana samun mafita sosai a cikin lamuranta, don ko wannan Umarar tana kallon ta ne a matsayin warakar dukkan damuwarta, domin can ne wurin mai magaryar tuƙewa.
Raka’a biyu ta gabatar, wadda ta saka ta a jerin Nafilolin da take a kowace rana, tana yin wannan sallar ne kafin ta yi barci, idan ta gama sai ta karanta Suratul Mulk, haɗe da Suratul Iklas ƙafa goma, daga nan sai ta yi addu’a ta kwanta, Deeni ne ya koya mata wannan nafilar, kuma da ta riƙe ta sai gashi ta daina kwana da damuwa a ranta, da ta faɗa masa irin falalar da fahimci sallar na da ita sai ce mata ya yi “Kada ki manta da cewar ambaton Allah yana maganin dukkan damuwa, don haka ki kada ki sare”, aikuwa gashi nan yanzu ta yi bankwana da damuwowi masu yawa.
Bayan ta gama sallar ne ta yi adduo’in da ta saba, sannan ta koma kan gadonta, tada Raihan ta yi ta bashi Mama ya sha, sannan ta rungume shi suka yi barcinsu mai cike da nutsuwa.
Deeni kuwa bushewa idanunsa suka yi, damuwar da ba a son ya shiga ce ya samu kansa ba tare da ya sani ba, tsoro ne cike da ransa, don ba shi da tabbacin zai sake rayuwa da matarshi ko kuwa a’a, samun lafiyarsa ne yake gani shi ne mafita, toh amma da ya yi dogon nazari sai ya ga ba mafita bane, domin a lokacin da yake da cikakkiyar lafiya Maman Deena ma ba ƙaunar sa take ba, bare kuma kuma yanzu da ya nakasa.
Ajiyar zuciya ya sauke sakamakon mutuwa da jikinsa ya yi, “Allah ka sani ba ni da wayau, bani da wata dubara, sai yanda ka yi da ni ya Allah”, Lalu da ke kwance a kan doguwar kujera yana jin sa, bacci cike da idanunsa ya tashi zaune tare da tambayarsa “Yaya lafiya dai ko?”, idanun Deeni a lumshe ya ce “Ka san in dai ina tuna Deena toh bani da sauran lafiya”, wani irin kallo Lalu ya yi masa, wani lokaci ko ya yi niyyar jin haushinsa sai ya fasa, saboda so ya wuce tunanin mai tunani, cewa ya yi, toh amma duk da haka yana da kyau ya riƙa jurewa tunda dai ba lafiya gare shi ba, cewa ya yi “Dan Allah yaushe zaka koyi juriya ne? Abin nan wata da watanni amma kullum ka tuna sai an ga alamun damuwa a tare da kai, ga wannan halin da kake ciki, haba don Allah.”
Duk da Lalu ƙaramin ƙanensa ne, amma in dai yana faɗa toh shiga taitayinsa yake, saboda gaskiya yake faɗa, lamo Deeni ya yi yana sauraronsa lokacin da yake faɗan, shi kuwa Lalu haushi ne ya ƙara ƙule sa, don ko irin ɗan kare kansa ɗin nan bai yi ba, a ƙufule Lalu ya ce “Tunda ka fi son mu yi ta fama da jinya shikenan, kai ne da ciwo, mu ne da jinya ai.”
Deeni na jin haka ya buɗe idanunsa da suka ƙanƙance, yunƙurawa ya yi ya tashi zaune tare da jingina jikinsa da gado, idanunsa basa ganin Lalu, sai hasken wayarsa kaɗai, saboda sun kashe fitilar ɗakin, shi kuma baya gani da dare. Tabbas ya san damuwarsa ta shafi ƴan uwansa, tunda kowane hali ya samu kansa su ne ke tsayuwar daka wurin ganin ya fita a wannan hali, don haka adalcin da ya kamata ya yi masu shi ne ya guji duk abin da zai jefa shi a matsala. “Farouk, tabbas duk halin da nake ciki tare muke shan wahalar da ku, kuma na daɗe ina yi ma kaina faɗan bai kamata a ce ina tsirar duk wani abin da zai cutar da mu baki ɗaya ba, don haka Insha Allahu zan kiyaye, duk da abin ba mai sauƙi bane Lalu.”
Yadda ya kama kansa ne ya sa Lalu sassauta fushinsa, cewa ya yi “Tabbas kam ba daɗi yanayin da kake ciki, toh amma ka koyi haƙuri, Allah da ya ɗora maka wannan damuwar, da sannu zai yaye maka ita Insha Allahu”, Deeni ya ce “Allah ya yaye mana”, Lalu ya ce “Amiiiiin.”
Dukkaninsu komawa suka yi suka kwanta, bacci ne dama a idanun Lalu, cikin ɗan ƙanƙanen lokaci ya yi awon gaba da shi, Deeni kuwa sai dai ya cigaba da ambaton Allah, domin samun nutsuwar zuciyarsa. A wannan daren ne kuma ya ji ya gaji da India ma gabaɗaya, Saudiyya yake so kawai, domin a can ne yake da yaƙinin warakar damuwarsa ta fili da ta ɓoye.
Ɗaukar ma ransa jajircewa ya yi tare da sanya ma zuciyarsa ƙarfi, cikin ikon Allah kuwa sai gashi har lafiya ya samu.
Doctor Niranjana tana ganin haka ta yi magana da sauran Doctors, ana checking ɗinshi aka ga ya cancanci Sallama, aikuwa ya ji daɗi sosai.
A ranar da ya fito asibitin ji ya yi tamkar a wata duniya yake, domin kuwa ya ga cikakkiyar fassarar karin maganar nan da ake cewa “Allah ɗaya gari ban-ban”, tun a wurin gine-gine ya san ba ɗaya bane, godiya ya yi ma Allah a fili da kuma ɓoye, domin shi ne mai sauya al’amura, suna komawa hotel ɗinsu ya kira Hajja Vedio call, tana ɗagawa ta ce “Har an yi sallamar kenan”, saboda ta lura background ɗinsa, amsa ya bata “Eh Hajjah”, ta ce “Masha Allah, godiya ta tabbata ga Allah Subhanahu wata’ala, na yi murna sosai Deeni, Allah ya ƙara maka lafiya”, ya ce “Amiiiiin Hajjah, Nagode sosai da addu’oinki.”
Tambayar shi ta yi”Ina Farouk?”, Asma’u da ke gefe tana ji ta leƙo “Hajjah ni ba zaki tambaye ni ba?”, dariya Hajjah ta yi kafin ta ce”Toh neman me zan maki tunda kina da mai kula da ke”, Bashir na zaune a kan kujera ya yi dariyar jin daɗi, saboda yabon sa ne aka yi, Lalu ya ce”Rabu da ita Hajjah, kishi take”, Hajjah ta ce “Kishi ne fa, ta ga ka maye mata gurbin Auta”, dariya sosai suka yi, bayan sun gaisa hada Bashir ne ta ce “Toh Allah ya yi maku albarka”, suka ce “Amiiiiin.”
Da ta yi musu maganar dawowa, Deeni ya ce zasu ƙara sati ɗaya a India, saboda zai riƙa zuwa checkup, daga nan sai su wuce Saudiyya, cewa ta yi “Sai cikin azumi dai”, Deeni ya ce “Eh Hajjah”, ta ce “Me zai hana ku tsaya nan a kammala azumi”, Deeni ya ce “Haka muka tsara, faɗa maki ne bamu yi ba”, da yake tana yi musu kwaɗayin dacewa da falalar ta ce “Toh Allah ya taimaka.”
Asma’u ce ta leƙo “Hajjah muma zamu je Saudiyyar, tare da su Yaya zamu je”, cike da jin daɗi ta ce “Ke don Allah?”, ta ce “Allah kuwa Hajjah”, ta ce “Masha Allah, na taya ki murna Auta, Allah ya ƙara zaunar daku lafiya Asma’u”, ta ce “Amiiiiin Hajjah”, Addu’oi ta yi ma ƴaƴanta, sannan suka yi sallama.
Shiru Lalu yayi yana nazari, ya san dai ko shakka babu Hajiyarsu na kewars u, bata ƙi ba a ce sun dawo yau ma, kawai dai ta yi masu kawaici ne, kuma hada ganin Saudiyya ne, wuri ne da kowa ke fatan ya je, ba zata hana su ba.
“Toh wai me zai hana mu yi mata visa, sai mu haɗe, tunda dai muna da ikon nan”, abin da zuciya ta ruwaita mashi kenan, bai yi wata-wata ba ya fito da sirrin zuciyar shi, saboda babu buƙatar ɓata lokaci a wurin yi ma mahaifiya hidima.
Sai dai bai yi magana ba, sai da ya rage daga shi sai Deeni a ɗakin, gefensa ya zo kan gado ya zauna “Yaya, ka san wata shawara da na yi da zuciyata?” Deeni ya ce “A’a”, ya ce “Na yi nazari, na ga Hajjah zata so mu dawo gida, idan muka ce sai nan da kwana talatin zamu koma lallai ta cutu da yawa”, tarbar numfashinsa Deeni ya yi, saboda shi ma abin ya tsaya mashi rai, cewa ya yi “Gaskiya ne Farouk, nima na yi wannan nazarin, amma me kake ganin shi ne mafita?”, Lalu ya ce “Abin da nake ganin zamu yi, me zai hana a biya mata ta yi Umara, idan ya so sai mu dawo tare.”, cike da gamsuwa Deeni ya jinjina kai “Wannan shawara ta yi Farouk, ina da yaƙinin zata yi farinciki”, Lalu ya ce “Gaskiya ne, yanzu sai mu ji nawa ne kuɗin zai kama, sai ayi da wurwuri, tunda ka ga Azumi ne, visa zata yi wahalar samu”, Deeni ya ce “Gaskiya hakan ya yi, ai kana da mutane a wannan harkar ko?”, Farouk ya ce “Eh”, number wani abokinsa da ke aiki a wani traveling Agency, bayan sun gaisa ne ya tambaye shi idan mutum zai je Umara visa da komai nawa ne, sannan za a iya samu, wuri bai cike ba kuma.?
Lalu mutum ne mai jama’a, shi ya sa duk Alfarmar da ya nema cikin ikon Allah yana samun ta, tabbacin samun visa aka yi mashi, aikuwa take suka ƙarƙare magana, cewar Hajiyarsu za a yi mawa.
Wani hanzari Deeni ya kawo ta hanyar faɗin “Sai dai ka san me?”, Farouk ya ce “A’a”, Deeni ya ce “Kana ganin Hajiya zata iya zuwa ita kaɗai?”, shiru Farouk ya yi yana nazari, tabbas ba zata iya zuwa ita kaɗai ba tunda ba ma lafiya gareta ba, “Toh amma ya za a yi yanzu?”, ya tambayi Deeni, cewa ya yi “Toh mafita ita ce a samu wanda zasu yi tafiyar tare na kusa, ka ga da muna da iko sosai, sai itama Hajiya Ummah a biya mata, toh sai a hankali”, jinjina kai Lalu ya yi “Gaskiya kam bamu da iko, amma mu tuntuɓe su mu ji, ko Yaya Asiya, tunda na ji itama tana son zuwa Umara.”
Shawarar Lalu aka bi, inda aka tuntuɓe Hajiya Ummah, kasantuwar ta na babba, bata wahalar da shari’a ba tunda bata da iko. Yaya Asiya suka yi ma magana, baki biyu ta basu, cewar tana da iko, amma sai ta nemi iznin mijinta, idan ya amince shikenan. A kan wannan magana suka tsaya, kafin su tashi wurin sai gashi ta kira su, tare da basu tabbacin da ita zasu yi tafiyar. Sun ji daɗi kuwa, musamman da ya kasance ita ce, saboda acikin ƴaƴan Hajiyar ita ta daban ce, tana da jin ƙai sosai.
Saƙon na je ma Hajiyarsu fashewa ta yi da kukan murna, a fili ta ce “Lallai ba arzikin da ya kai mutum ya haifi ƴaƴa masu albarka”, Gwaggo Salame ta ce “Wallahi kuwa Hajiya, ai kin yi sa’ar ƴaƴa, daga mazan har matan kuwa”, domin a kan idanunta su Hajiya Ummah ke aiko mata da Alkhairori, sannan a kullum sai su yi waya fiye da biyu ko uku, kuma magana ce ta don jin ya mahaifyarsu take. Hajjah ta ce mata “Ai Alhamdulillah Salame, yi masu addu’a ce kawai abin da ya rage, sai mu yi fatan Allah ya bamu iko Amiiin.”
Yaya Asiya kuwa shirin tafiyarsu ta fara yi, inda ta ɗinko musu Hijabai da riguna na gani na faɗa, sannan ta siyi sabon akwati ta tsara ma Hajjah nata a ciki ta kawo mata. Tun a shigowar Yaya Asiya da akwatin Hajjah ta tambaye ta “Daga ina haka?”, aje shi ta yi a gabanta “Kayan tafiyarki Umara ne”, da mamaki Hajjah ta tambaye ta “Duk a nan ciki?”, saboda akwatin ya tsaru sosai, Yaya Asiya na dariya ta ce “Eh Hajjah, gwara a fara shiri da wuri ko?”, Hajjah ta ce “Ƙwarai kuwa Asiya, Allah ya yi maku albarka”, Yaya Asiya ta ce “Amiiiiin Hajjah”, gefenta ta zauna a kan carpet tare da jawo akwatin ta buɗe, ɗaya bayan ɗaya ta fito da kayan tana gwada ma Hajjah, bayan ta gama ne cike da jin daɗi Hajjah ta ce “Duk ni kaɗai waɗannan kaya?”, domin aƙalla ta kashe sama da dubu ɗari wurin haɗa wannan akwatin, Yaya Asiya ta ce “Naki ne Hajjah, idan an samu dama kafin mu tafi sai a ƙara siyen wasu”, kai Hajjah ta girgiza “A’a Asiya, hakan ma sun Isah, Nagode sosai, Allah ya yi maku albarka Amiin.”
Kafin a maida kayan ne ta ce a ɗauko mata wata jallabiya da ta daɗe tana ɓoyo, asalin ta kuma Babansu Deeni ne ya yi mata tsarabar ta a Umararsa ta ƙarshe, hakan ya sa ta ɓoye ta saboda rigar na tuna mata abubuwa masu yawa. Ɗaga rigar Yaya Asiya ta yi “Rigar nan na da kyau Hajjah”, Sai da ta yi dariya mai cike da kewar mijinta ne ta ce “Ai babanku ya iya siyen kaya”, Yaya Asiya ta ce “Na rantse kuwa Hajjah, ni dai ban taɓa ganin irin kayan da Abbah ke siya mana a wurin wasu ba, ga shi komai na sa unique ne”, Hajjah ta ce “Ai Allah dai ya jiƙan maza, ya sa mu iske su da Alkhairi”, Yaya Asiya ta ce “Amiiiiin.”
Naɗe rigar ta yi tare da jera ta a cikin akwatin, saboda ta ce da ita zata yi ɗawafin farko idan sun je, hannun Yaya Asiya a kan rigar dube ta a marairaice”Hajjah don Allah ina riƙon rigar nan”, cike da wasa ta ce “Anya kuwa Asiya zan iya baki ita?”, a marairaice ta ce “Don Allah, ina son ta sosai.”
Duk abin da ƴaƴanta ke so zata iya mallaka musu shi, cewa ta yi “Toh zan baki, da mun dawo ki ɗauke ta na baki duka Asiya”, Aikuwa don murna Yaya Asiya bata san lokacin da ta maƙalƙale ta ba “Nagode sosai Hajjah, Allah ya ƙara maki lafiya da nisan kwana masu albarka”, Hajjah ta ce “Amiiiin ya Allah.”
Haɗa akwatin aka yi sannan Asiya ta ɗauke shi, a gefen gado daga jikin bango ta ajiye shi, “Wai ina Gwaggo Salame? Tunda na shigo ban ganta ba”, Yaya Asiya ta tambayi Hajjah lokacin da take ƙarasowa inda take, amsa Hajjah ta bata da “Ta je kasuwa ne”, Yaya Asiya ta ce “Auho”, zama ta yi suka ci-gaba da hira da Hajjah, ana nan zaune sai ga Gwaggo Salame ta dawo.
Sosai take son Yaya Asiya saboda tun tana garinsu take aika mata kayan sawa, da ta dawo wurin Hajjah kuwa ba abin da Yaya Asiya bata yi mata na kyautatawa, shi ya sa take ƙaunar ta.
A ƙasa ta rashe tare da washe baki ta ce “Sannu da zuwa Uwar ɗakina”, Yaya Asiya bata son girman da Gwaggo Salame ke bata, a ganin ta ya yi yawa, cewa ta yi “Yauwa Gwaggo, na shigo aka ce kin tafi kasuwa ai”, ta ce “Aikuwa ba, na yo cefane ne”, Yaya Asiya ta ce “Ayya, sannu da dawowa.”
Hajjah ce ta ce Asiya ta ɗauko mata akwatin kayan tafiya, bayan an ɗauko ta gani ne ta ce “Allah Sarki Uwar ɗakina, Allah ya albarkace ku”, Yaya Asiya ta ce “Amiiiiin Gwaggo.”
A kullum Gwaggo Salame ta ga yadda ƴaƴa ke ji da iyayensu sai ta tuna ɗanta ɗaya da ta rasa, wanda dama shi kaɗai ne ta haifa, sai da ya girma, har ya haifi yara biyu ya rasu, ga yaran ƙananu ne kuma suna wurin mahaifiyarsu, cikin kewar ɗanta ta ce ma Hajjah “Har na tuna da Haruna, haka nima yake kula da ni kafin ya rasu.”, wani irin tausayin ta ne ya kama Hajjah, cike da tausayinta ta ce “Allah Sarki, Haruna ai yaron kirki ne, Allah ya gafarta mashi”, Yaya Asiya ta ce “Ai idan na tuna yana da yara daɗi nake ji, wata rana su ne za su maye gurbinsa”, Hajjah ta ce “Gaskiya ne, Allah ya kyautata bayansa”, suka ce “Amiiin.”