Skip to content
Part 45 of 45 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Da farko sallama ce Deena ta yi ma Rahila haɗe da Barka da shan ruwa, daga nan kuma ta ɗora faɗin “Yaya na ta shan addu’aoinku, Allah ya saka da Alkhairi Amiin”, tabbas dama Rahila ta san Deena ba zata yi mata wulakanci ba tunda wayayyiya ce, amma kuma bata yi zaton maganar zata zo da taushi haka ba, don ta lura da yadda Deena ke matuƙar kishin mijinta. Ajiyar zuciya Rahila ta sauke kafin ta yi mata reply da “Masha Allah, ai Dr. Ya cancanci addu’ar kowa, Allah ya ƙara masa lafiya”, da rawar murya ta naɗi voice ɗin, mafarin bata gama magana ba ta tsinke, saboda kada Deena ta gane cikin fargaba take. Wani sabo ta naɗa tana tambayarta Raihan.

Maimakon Deena ta maido mata voice, sai ta yi mata typing da “Masha Allah, mun gode sosai”, a voice ɗin Raihan ma ta rubuta “Lafiya lau yake, yana gaida ki.”

Rahila na da wani abu, ta fi son idan da voice ta fara magana da mutum a chat, toh a ƙare ta da voice, idan aka koma typing, toh ta kan ji ba daɗi. Toh a nan kuma kama kanta ta yi, sai ta ga kamar duk haushi ne ya sa Deena yi mata typing, a taƙaice ta rubuta mata “Ina amsawa, a shafa mani kansa”, Deena na zuwa ta danna mata reaction na like.

Jikin Rahila a mace ta ja dogon numfashi tare da sauke shi, Fadila da ke kwance a gefen gado tana danna waya ta tambaye ta “Wannan dogon numfashin fa?”, ba tare da Rahila ta ɗauke idanunta a kan waya ba ta ce “Gajiya ce kawai, so nake in kwanta”, Fadila ta ce “Da wuri haka?”, duban agogon waya Rahila ta yi ta ga Ƙarfe sha-ɗaya, tambaya ta maido mata da “Idan mutum bai yi barci ba yanzu, toh sai ƙarfe nawa zai yi?”, Fadila ta ce “Ina fa zan sani, ni fa idan muna chat da Ya Malik zan iya kwana zaune”, ta ƙarashe maganar tana duban Rahila da har yanzu jikinta a mace yake.

Baki Rahila ta taɓe haɗe da faɗin “Uhm, aiki ya same ki”, Martani Fadila ta mayar mata da “Ke ma da ya same ki zaki gane ba laifi muke ba ni da Ya Malik”, har a cikin ran Fadila bata faɗi haka da nufin yaɓa ma Rahila magana ba, saboda ko ba komai Yayarta ce, sai dai abin da bata yi zato ba shi ne maganar ta ƙona ran Rahila, don kuwa ji ta yi kamar ta yanke ta, cikin fushi ta ce “Fadila ni zaki faɗa ma haka? Wato kina nufin ni ban san daɗin soyayya ba tunda bani da saurayi ko? Toh na gode sosai.”

Aikuwa zumbur Fadila ta tashi zaune, murya a marairaice ta ce “Inna li Llahi, Haba Yaya Rahila, me ya sa zaki yi mani wannan fahimtar?”, Rahila ta ce “Toh ga magana nan a fili, ko kin manta me kika ce?”, kai Fadila ta girgiza “Ban manta ba, amma na rantse ba yadda kika fahimta nake nufi ba”, shirun da Rahila ta yi ne ya bata damar cigaba da faɗin “Amma don Allah ki yi haƙuri, kuma ke kam kin fi ƙarfin a goranta maki a kan soyayya”, baki Rahila ta taɓe “A’a ke dai faɗi gaskiya”, saboda yadda suka ƙare magana da Deena ya tsaya mata a rai, matsowa Fadila ta yi tare da dafa mata hannu “Allah kuwa gaskiya na faɗa, ke ce kika ƙi soyayya, amma ba soyayya ce ta ƙi ki ba, don haka ki gafarce ni Ƴaƴata.”

Tabbas Rahila ita ce taƙi soyayya, amma a can baya, domin babu kalar namijin da bai zo ya ƙaunace ta ba, amma sai ta ƙi amincewa, a ganinta ɓata lokaci ne, saboda ta fi son ta cimma burinta na karatu, kuma ko a yanzu ma akwai soyayyar da ke ta bibiyarta, kamuwa da soyayyar Deeni ce ta makantar da ita har bata ganin komai.

Sosai maganar Fadila ta karya mata zuciya, don kuwa tabbas a yanzu ita soyayya ke gudu, tunda ga shi ba wani salon da bata bi ba na nuna tsantsar soyayyar ta ga Deeni, amma sai pretending yake kamar bai san tana yi ba, hannunta riƙe da na ƙanwarta ta ce “Fadila, a can baya ni nake gudun soyayya, amma a yanzu ni ce nake bin soyayya da gudu, amma na kasa cimma ta”, yadda ta ƙarashe maganar ba alamun wasa ne ya sa Fadila tattaro dukkan nutsurwata, tambayarta ta yi “Me ya sa kika ce haka Yaya?”, Rahila ta ce “Na kamu da tsananin son wani, son da ban taɓa zaton akwai irinsa a rayuwa ba, don da shi nake dukkan numfashina, sai dai matsalar kamar bai san ina yi ba, ko kuma ƙila ya sani, pretending kawai yake mani.”

Sosai yanayin Rahila ya ɗarsa ma Fadila tausayin yayarta, cike da son jin waye wannan ta tambaye ta “Waye wannan da ke shirin yi ma kansa asara, don kuwa da ya san wacece ke a nargarta, ba zai tsaya ɓata lokacinsa ba wurin ƙin karɓar soyayyar ki”, Rahila ta ce “Ya sani, tunda shi ma yana faɗa”, Fadila ta ce “Toh wai waye?”, ba tare da Rahila ta ji wani abu ba ta ce “Deeni ne”, wata irin faɗuwar gaba ce ta riski Fadila, don kuwa yayarta ta ɗaukar ma kanta dala ba ganmo.

Da mamaki ta ce “Deeni dai mai ciwon ido”, kai ta ɗaga mata “Yeah, shi”, jinjina kai Fadila ta yi “Babbar magana, amma ba kya ganin lalurar da ke tare da shi? Ke ce shaida fa”, Rahila ta ce ” Toh shi so ai ba ruwansa da siffa”, Fadila ta ce “Haka ne, kuma ga shi ma an ce ya warke ko?”, Rahila ta ce “Eh.”

Ɗan shiru suka yi kowa da abin da ke ransa, daga bisani ne Fadila ta ce “Ni fa Yaya sai nake ganin wannan duk mai sauƙi ne, kawai matsalar ita ce matarsa da muke ƴar kunya da ita”, Fadila ta ce “Ni ma ita ce damuwata, Allah kuwa da tuni na cire kunya na faɗa masa”, kwaɓarta Fadila ta yi, don ta san illar da ke cikin mace ta fara faɗa ma saurayi tana son sa, duk da ba haram bane, amma matsalar mazan yanzu girman kai ne ke shigar su, a hausance ma an ce “Matar cushe bata daraja”, don haka ta bari dai a isar mata da saƙonta, shi ma za a nuna ba wai daga Rahilar bane.

Amma sharaɗin da Fadila ta kindaya shi ne a ɗan dakata a ga shin za a maida mashi matarshi? Idan ta koma sai su san wace dubara zasu yi, idan bata koma ba, toh kai tsaye zasu san hanya mai sauƙin da za a haɗa su, domin kuwa Rahila tana da kalar nata wayau ta hanyar connection, saboda ta haɗa aure fiye da a ƙirga, auren yayarta kuwa ba zai gagare ta ba da ikon Allah.

Daga ƙarshe kuma ta bata shawarar ta cigaba da addu’a. 

Deena kuwa duk yadda ta so danne ma ranta sai da ta kasa, zaune ta tashi cikin dare ta haɗa tagumi tare da tambayar kanta “Ita Rahila me take nufi ne?”, don ta yi mamakin da ta iya mallar picture ɗin Deeni, da kuma ƙwarin guiwar ɗaura shi a status, wani sashe na zuciyarta ne ya ɗarsa mata zargin Deeni ta hanyar faɗin “Ko dai suna tare ne?, Ɓoye maki yake?”, sanin gaibu sai Allah, sai da ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin ta yi magana a fili “Tunda maza basu da tabbas ba, amma Allah ne masani”, don kuwa mijin ƙawarsu da ya auri causin ɗin matarsa ya goge musu hadda, shi ya sa duk abin da aka ce namiji zai yi, toh zai aika. 

Kasa haƙuri ta yi har sai da ta ajiye ma Deeni saƙon voice a WhatsApp, bayan ta rufe data ne ta sauka a kan gadon, alwala ta yi ta fito, ganin Raihan na son falkawa ne ta ɗauke shi haɗe da ba shi mama, bai wani daɗe ba ya koma barci, kwantar da shi ta yi, sannan ta kimtsa kanta haɗe da kabbara sallah. 

Deeni bai shiga WhatsApp ba sai da suka shiga birnin Madina, don washegari tunda safe suka tafi. Da niyyar faɗa ma Deena sun sauka Birnin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya shiga WhatsApp, amma sai ya ci karo da saƙonta wanda ya sanya shi dariya, ta wani bangaren kuma ya ba shi takaici. Farko dai tuhumarsa ta yi inda Rahila ta samu hotonsa, daga ƙarshe kuma ta nuna mashi idan ma Rahilar son ta yake ya aure ta, tunda ita yanzu bata a kowa. 

A fili ya yi dariya, a WhatsApp ɗin kuma reply ya yi mata da emoji mai riƙe da haɓa, sannan ya rubuta mata “Sannu Madam, wai shin me ma ke damunki ne.? 

Aikuwa dama jiransa take online, a take ta yi masa reply da “Au haka ma zaka ce?”, tambaya ya maida mata da “Toh ya kike so na ce ne Deena? Ke kullum cikin zargina kike, wai idan na ta shi son wata zaki hana ne?”, reply ɗin da ta yi mashi ne ya tabbatar mashi da ji zafin maganar, don kuwa voice ne mai ɗauke da muryarta tana kuka, lokaci ɗaya kuma tana faɗin “Ni kake faɗa ma haka ko Yaya?, Koda yake laifina ne da na manne maka, duk da sakin da ka yi mani, kuma ba damuwa, zan kama kaina, kai kuma ga Rahila nan.” 

Sosai ya ji bai kyauta ba, kamata ya yi tun farko ya wanke kansa, toh amma halinta ne ya sa shi yi mata haka, don bata barinsa ya zauna lafiya. Voice call ya kira ta, da mamaki sai ya ga ta yi reject na call ɗin, bai wani ɓata lokaci ba ya naɗi voice mai ɗauke da “Haba Deedee, ke ce ba kya barina na zauna lafiya, yanzu sai sauri nake in faɗa maki mun isa Madina, amma ke kuma kin rusa farincikin”, sakin voice ɗin ya yi, ya so sake yin wani voice ɗin domin ya wanke kansa daga zargin da take mashi, sai kuma ya fasa, saboda ya fahimci lallaɓatan da yake ne ke bata damar yi masa karan tsaye a duk lokacin da ta ga dama, gwamma ya riƙa barin ta a duhu, Mai yiwuwa ta shiga taitayinta. 

Aljihu ya maida wayarsa, lokaci ɗaya kuma yana faɗin “Yarinyar nan na ba ni mamaki”, Lalu da ke gefe da ya san wadda yake nufi, amma sai ya basar ya ce “Wa kenan?”, Deeni ya ce “Deena mana, wai daga Rahila ta ɗaura ni a status sai masifa take mani, toh wai ita zata hana ni yin aure ne ko da muna tare da ita? Bare kuma yanzu da bama tare”, ɗan rausaya kai Lalu ya yi, a fili ya ce “Ahafi! Duk laifinka ne ai”, Deeni ya ce “Ta ya yake laifina”, ma so zuwa birni ne, kuma aka aiko masa da Sarki na kira, Sosai Lalu ya nuna masa kuskurensa wurin nuna ma Deena makantaciyyar soyayya, tunda suka rabu Deeni ya susuce mata, wai duk don kada ta shiga damuwa, yanzu ga shi nan ita da bata iya cin ƙwan makauniya ba tana sa shi damuwar.

Nuna mashi Lalu ya yi ya kama kansa a matsayinsa na namiji, kada ya bari tausayinta ya sake ja masa raini, asali ma bai kamata a ce alaƙarsu ta yi ƙarfi haka ba tunda babu tabbacin za su sake aure, don haka gwara tun da wuri su koyi haƙuri da nesa da juna. 

Sosai Deeni ya ɗauki shawarar Lalu, musamman da ya ga ta share shi, fita batunta ya yi shi ma, sannan ya cigaba da addu’a. 

Deena kuwa tun tana sa ran zai ɗora wata maganar a kan wadda ya yi mata har ta fidda, aikuwa sosai abin ya dame ta, don zuciya ta gama faɗa mata soyayya yake da Rahilar tunda gashi har zai iya share ta. Sosai abin ya taɓa ta, har ta kai ga da kyar take cin abinci wurin sahur da buɗa baki, Ummanta na lura ta ce “Wai me ke damunki ne da ba kya cin abinci sosai”, kamar zata yi kuka ta ce “Ba komai Mommah”, baki kawai ta taɓe, don ta san tatsuniyar gizo bata wuce ƙoƙi, ko shakka babu tunanin Deeni ne, kuma zata yi ta gama. 

Bayan Deena ta koma ɗaki ne ta yi jugum a kan gado, “Yanzu ni Yaya zai iya sharewa?”, ta tambayi kanta, amsarta a fili take, tunda ga shi har kwanansu huɗu bai tanka mata ba. Zuciya ce ta ingiza ta a kan ta yi mashi magana, har ta yunƙura, sai kuma ta fasa, bari ta yi ko da zata yi maganar, sai idan sun je Saudiyya, tunda suma gobe ne tafiyarsu. 

Deeni kuwa ko a jikinsa, asali ma hakan sai ya bashi ƙwarin guiwar dagewa da addu’a, ba dare ba rana kullum yana masallaci, roƙonsa shi ne idan akwai Alkhairi, Allah ya sa ya maida matarsa, idan kuma babu Alkhairi, Allah ya sa mashi dangana, ya kuma zaɓa kashi mafi Alkhairi, don a yanzu ya rage jin wannan haukan son na Deena, wanda idan babu ita ba zai iya rayuwa ba, ya san dai yana matuƙar ƙaunar ta, amma kuma zai iya rayuwa idan babu ita. Tasirin addu’a kenan, wanda in dai mutum ya dage, toh zai samu kowace irin mafita ce yake nema a wurin Allah. 

Washegari da misalin ƙarfe goma na safe jirginsu Deena ya bar Nigeria. Wurin ƙarfe huɗu kuwa har masaukinsu sun sauka a Hilton Hotel. Tafiyar ta family ɗin Alhaji Lawan ce, don kusan mutum goma ne suka zo a tare, kuma sauran ma suna tafe kafin a shiga goman ƙarshe. 

Daɗi kamar ya kashe Deena, saboda ta zo inda kukanta ya ƙare. Room ɗaya aka ware mata ita da Aunty Ammah, wanda ƙanwa ce a wurin Ummanta, dan itama ta shiga cikin tawagar tafiyar. Aunty Ammah tana da kirki sosai, kuma sam bata goyon bayan abin da Umman Deena ke yi. Bayan sun samu nutsuwa ne Aunty Ammah ke ce ma Deena “Kin ga yanzu dama ta samu da za ki kai kukanki wurin Allah, ki roƙe sa ya sa ki koma ɗakinki”, Ɗan murmushi Deena ta yi kafin ta ce “Gaskiya ne Aunty Ammah, kuma kin san shi ma yana nan Saudiyya fa”, Aunty Ammah ta ce “Da kyau, ya san kin zo?”, Deena ta ce “A’a”, ta ce “Toh ki faɗa masa mana”, maƙe kafaɗa Deena ta yi tare da labarta mata sun kwana biyu basu yi magana ba, da Aunty Ammah ta ji ba’asi ta yi ma Deena faɗa sosai don laifin nata ne. 

Waya Deena ta ɗauka, tare da shiga WhatsApp, contact ɗin Deeni ta shiga ta rubuta mashi “Asslm Alkm Yayana, na yi kewar ka sosai, kuma mun shigo Saudiyya..” 

Deeni na zaune a masallaci ya ji alamar shigowar saƙo a wayarsa, da hanzari ya duba, yana ganin Deena ya saki nannauyar ajiyar zuciya saboda jiran ta shi ma yake, sosai ya yi kewar rigimar ta, wadda a can baya yake kallon ta a matsayin damuwa. Buɗe saƙon ya yi, bayan ya gama karantawa ne ya lu

mshe idanu haɗe da faɗin “Alhamdulillah.” 

<< Mutuwar Tsaye 44

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×