Skip to content
Part 46 of 46 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Zuciyarsa cike da farinciki ya kira ta voice call, jiran sa dama take, tana ɗagawa ya ce “Oyoyo my Dee, barka da zuwa Makkatul Mukarrama”, daga can yana jin ta cikin farinciki ta ce “Barka dai Yaya”, ƙorafin da ke cike da ranta ta ɗora da shi ta hanyar faɗin “Na yi kewar ka sosai, ka manta da ni, duk na shiga damuwa”, dariyar wannan ƙorafin ya yi mata, sannan shi ma ya ɗora da faɗin “Nima na yi kewar ki sosai, sauran maganar kuma sai mun haɗe ko?”, ta ce “Eh, amma yaushe zamu haɗu?”, ya ce “Sai kun huta”, tambayar ta ya yi “A ina kuka sauka?”, ta ce “Hilton ne”, tuni dama ta faɗa mashi, kawai so yake ya ƙara tabbatarwa, faɗa mata ya yi su ma a Hilton ɗin suke, bayan ya yi mata kwatance suka fahimci kusa suke, kai su ko da nesa suke haɗuwarsu abu ne mai sauƙin gaske.

Bayan sun gama wayar ne ya yi ma Allah godiya da ya kusanto mashi da Deena a kusa da shi, wanda hakan na nuna alamun samun nasarar komawar ta a matsayin matarsa da aka yi masa fin ƙarfi aka raba shi da ita.

Itama daɗi kamar ya kashe ta, zuciyarta fal da farinciki ta dubi Aunty Amnah da ke kusa da ita a gefen gado “Wai su ma a hotel ɗin nan suka sauka”, Cike da Mamaki Aunty Amnah ta ce “Ke don Allah?”, Deena ta ce “Haka ya ce, kawai muna a saman su su ne”, Aunty Amnah ta ce “Kin ji wani ikon Allah ko? Insha Allahu a kwai Alkhairi mai yawa cikin haɗuwar ku, Allah ma ya sa ta zama silar gyaruwar aurenku”, cike da zaƙuwa Deena ta ce “Amiiin ya Allah.”

Shirin masallaci suka yi, sannan suka fita, haɗuwa suka yi da su Umman Deena, sannan suka tafi. Ba wannan ne karon farko da Deena ta fara ganin Ɗakin Allah ba, amma wannan ya zama na musamman a gare ta, domin tafe take da bukatunta, waɗanda take sa ran dukkan damuwoyinta sun zo ƙarshe.

“Ya Allah, ka san tarin damuwoyin da na zo da su, ina roƙon ka alfarmar wannan ɗakin naka mai daraja, ka yi mani maganin su dukkan su”, addu’ar da ta faɗa kenan a ranta lokacin da suka shigo masallacin.

Deeni kuwa ka sa ɓoye farincikinsa ya yi har sai da ya faɗama su Lalu Deena ta shigo Saudiyya, murna suka taya shi, musamman Asma’u da Deena ke ƙawarta, shi kuwa bayan murnar sai kuma zaƙuwa da son ganin su da yake, don ma a ransa yana ta tsara ya zasu haɗu ba tare da wata matsala ta auku ba.

Deena ma tunaninta kenan, tambayar Aunty Amnah ta yi, bayan sun koma ɗakinsu “Aunty, kina ganin idan na haɗu da yaya ba za a samu matsala ba?”, Aunty Amnah ta ce “Matsalar me?”, Deena ta ce “Kawai tsoro nake ji, kin san Mommah ba a iya mata, kaɗan za a kuskure na yi laifi”, ɗan rausaya kai Aunty Amnah ta yi “Haka ne, amma ba zamu yi yadda za a samu matsala ba, zamu faɗa mata Deeni na garin nan, kuma zamu je wurinsa yi masa ya jiki, haɗe da kai masa ɗansa ya gani, ko kina ganin zata hana?”, shiru Deena ta yi, domin ta san wacece mahaifiyarta wurin murɗaɗaɗɗen hali, tsaf kuwa zata hana, kawai dai Allah ya kyauta.

“Kin yi shiru, kina ganin zata hana ko?”, Aunty Amnah ta katse ma Deena shirun, “Eh, zata iya hanawa fa, amma na rantse ko da ta hana sai na je na ga mijina, tsananin ya yi yawa”, mamaki fal da ran Aunty Amnah ta ce “Deena! Mamanki ta ƙeƙasar maki da zuciya ko?”, ran Deena ba daɗi ta ce “Ai ana tauye mani haƙƙi ne Aunty Amnah, har wani lokaci nake jin kamar Mommah bata so na”, Aunty Amnah ta san halin Umman Deena sarai, ko su da suke ƴan’uwanta idan halinta na faɗa ya motsa ba daɗinta suke ji ba, duk da tana da kirki sosai, kawai ita tana son ayi komai a kan tsari ne, cewa Aunty Amnah ta yi “Ki daina tunanin wai mahaifiyarki ba ta son ki, ba haka bane”, tarar numfashinta Deena ta yi “Aunty Amnah kullum faɗa fa?”, jinjina kai Aunty Amnah ta yi “Ai wannan faɗan shi ne son, duk duniya bata ƙi ki fi ɗan kowa ba saboda tsananin ƙaunar da take maki, toh da ta ga kin yi kuskure ne sai ta hau faɗa, a ganinta laifinki ne, don haka sai kin yi haƙuri, kuma kin koyar da kanki yin abubuwan da take so”, idanu Deena ta lumshe tare da haɗe yawun damuwa, lokaci ɗaya kuma ta ce “Na rantse kuwa ina yin duk yadda take so Aunty Amnah, amma a cikin yi mata biyayyar ma sai ki ga tana faɗa, wani lokaci sai in ji kamar zan mutu don takaici.”

Cike da tausayin ta Aunty Ammah ta ce “Ki yi haƙuri kin ji, Allah yana jarabtar bawa da duk ta inda ya ga dama, Annabawan Allah sun ishe mu wa’azi, saboda an jarabci wasun su da makusanta”, Kai Deena ta jinjina “Gaskiya ne”, Aunty Amnah ta cigaba da cewa “Annabi Ibrahim an jarabce shi da Mahaifi, ki duba ki ga ƙaunar da Allah yake yi ma Annabi Ibrahim, amma aka jarbci mahaifinsa da kafirce ma Ubangiji, toh ya zai ji a matsayinsa na Manzon Allah, kuma mahaifinsa baya goyon bayansa?”, Deena ta ce “Da ciwo”, Aunty Amnah ta ce “Toh kin gani, kin san dai tunda mahaifinsa ya ƙi yin imani da shi, toh kowa ma zai ƙiya, sai waɗanda Allah ya so da Rahama ne kaɗai zasu bi shi”, cike da gamsuwa Deena ta ce “Haka ne, kuma fa mahaifa ne aka sani da goyon bayan ɗansu idan ɗaukaka ta zo mashi, tunda babu ɗaukakar da ta kai Annabta da Manzanci.”, Aunty Amnah ta ce “Toh jarabawarsa kenan, ga Annabi Nuhu da aka jarabta da mata da ɗaa! Duk wahalar wa’azin da yake, ashe matarsa da ɗansa basu yi imani da shi ba, yana tufka suna can suna warwara, a gabansa aka halakar da ɗansa cikin kafirai, toh shi kuma ya ce me?”, Deena da ta fara sanin daɗin ɗaa ta ce “Gaskiya ba daɗi, yadda iyaye ke ƙaunar ɗansu a ce gashi can ya halaka? Akwai damuwa.”

Aunty Amnah ta ce “Toh kin gani”, kafin ta cigaba da magana ne Deena ta tarbi numfashinta “Shi ma Annabi Luɗu matarsa an halakar da ita ko?”, Deena ta sani, kawai tana son maganar ne, saboda nutsuwar zuciyar da take samu, Aunty ko kuma Malama Amnah ta ce “Eh, kin ji wata fitinar da tafi ta kowa ma”, bakin Deena a yamutse ta ce “Wallahi kuwa Aunty Amnah, ina tsoron abin da mutanen nan suke aikatawa”, Aunty Amnah ta ce “Ai bala’in ya yi yawa, ace mutum ya rasa wa zai haƙe mawa sai jinsinsa, wanda ko dabbobi basa yin haka.”

Deena ta ce “Allah ya tseratar da mu, su kuma masu yi Allah ya shiryar da su”, Aunty Amnah ta ce “Amiiiiin don Nabiyi Rrahmati, kwanaki ai na ji Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa yana faɗin addu’ar da ya kamata mu riƙa yi, domin samun kariyar Ubangiji mu da ƴaƴanmu daga wannan ɓarnar ta homosexual da lesbianism”, da gaugawa Deena ta matso kusa da ita “Don Allah ya addu’ar take, tsoron wannan zamanin nake wallahi, yanzu wata school mate ɗinmu na nan kamar mutuniyar kirki, ashe wannan abun take yi, kuma da aurenta, hankalina yana tashi Aunty Amnah”, yadda ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka ne ya ƙara ma Aunty Amnah ƙaimin faɗa mata addu’ar, cewa ta yi “Dole hankalinki ya tashi Deena, duniyar ce idan mun san farkonmu, bamu san tsakiya da ƙarshe ba, sai dai fatan Allah ya sa mu yi kyakkyawan ƙarshe”, Deena ta ce “Amiiiiin ya Allah.”

Faɗa mata addu’ar Aunty Amnah ta yi kamar haka “Rabbi Najjini wa ahali mimma ya’amalun”, maimaita addu’ar Deena ta yi sannan ta ɗora da faɗin “Kamar ayar Alkur’ani ce ko?”, Aunty Amnah ta ce “Eh, Annabi Luɗu ne ya yi addu’ar, muma ana son mu yawaita yin ta, tunda mun ritso zamanin da babu kalar alfashar da ba a aikatawa”, Deena ta ce “Gaskiya ne Aunty, Allah ya tseratar da mu daga aikata abin ƙi.”

Nan Aunty Amnah ta yi ta buga ma Deena misalai na Annabawa da Salihan bayi, inda ta buga mata misali da Annabi Yusuf da aka jarabta da ƴan’uwa, sannan ta kawo mata misalin Asiya matar fir’auna, da dai sauransu, daga ƙarshe ta rufe da tambayarta da “Yanzu jarabawarki ta kai girman ta waɗannan bayin Allah?”, girgiza kai Deena ta yi “Ko kusa bata kai ba”, Aunty Amnah ta ce “Toh haƙuri zaki yi, su ma shi suka yi har suka ƙara samun ɗaukaka a wurin Allah”, jinjina kai Deena ta yi “Insha Allahu”, a cikin ranta tana ƙara gode ma Allah, domin ita faɗa ne kawai mahaifiyarta ta ke da shi, bawai mutuniyar banza ba ce, don babu abin da ya kai takaicin ɗaa ya tsinci kansa a hannun iyayen banza.

Aunty Amnah ta lura da sanyin jikin da Deena ta yi, wata nutsuwar ta shiga cusa mata, tambayarta ta sake yi “Kin san tarihin Juraiju?”, Ɗan shiru Deena ta yi tana nazari, daga bisani ta ce “Eh, amma na manta yadda asalin tarihinsa ya ke”, Aunty Amnah ta ce “Bari in baki tarihinsa a taƙaice, na san zaki ɗauki darasi mai yawa a ciki”, Deena na son tarihi sosai, tana dariya ta ce “Yauwa Aunty Amnah, ina son jin tarihinsa.”

Zama Aunty Amnah ta gyara a gefen gadon, sannan ta cigaba da faɗin “Juraiju mutumin kirki ne a cikin banu Isra’ila, saboda tsabar bauta da rashin son shagala ya koma bayan gari inda babu hayaniya ya gina ƴar bukka, tare da dawowa a ciki yana bautar Allah. Wata rana sai mahaifiyarsa ta zo tana kiran sa, lokacin shi kuma yana sallah, a ransa yana son ya je wurin mahaifiyarsa, amma kuma yana tsoron katse sallarsa, tunda ibada ce mai girma, ita kuma jin shiru bata fasa kiran sa ba, don ta san tabbas yana ciki, hankalinsa sai ya rabu gida biyu, sai ya riƙa faɗin ‘Ya Allah, ga mahaifiyata tana kira na, sannan kuma ga sallata’, yana miƙa lamarinsa ga Allah saboda baya son yin laifi.”

Kasaƙe Deena ta yi, tana son jin ƙarashen labarin, Aunty Amnah kuwa ta lura da haka, shi ya sa ta cigaba ba tare da kawo maganar da zata ratsa cikin labarin ba.

“Shirun da mahaifiyarsa ta ji, sai ta fusata, saboda babu daɗi kana kiran mutum, kuma yana ji ya ƙi amsawa”, jinjina kai Deena ta yi alamar “Haka ne”, Aunty Amnah ta cigaba da cewa “Aikuwa sai ta yi mashi baki ta hanyar faɗin Allah ya haɗa shi da sharrin mace”, Deena na jin haka hankalinta ya tashi, kamar zata yi kuka ta ce “Inna li Llahi, ita bata san sallah yake ba?”, Aunty Amnah ta ce “Bata sani ba, bayan wani lokaci, ita da shi har sun mance, sai a cikin gari wata mata ta yi ciki ta haihu ba tare da aure ba, da aka turke ta a kan waye uban yaron, sai ta ce ‘Juraiju ne’ mahaifinsa.”

Hankalin Deena a tashe ta ce “Na shiga uku Aunty Amnah, yanzu shi miye laifinsa, gashi bakin uwa ya kama shi”, Aunty Ammah ta ce “Tasirin bakin Uwa kenan, don haka ki roƙi tsarin Allah daga bakin iyaye muddin ba Alkhairi zasu faɗa a kanki ba”, idanu Deena ta lumshe, gabanta na cigaba da faɗuwa, saboda Ummanta ta sha lafta mata maganganu, yanzu tsoro take kada ace suna nan suna bibiyar ta, “Allah ka yafe mana”, idanunta cike da ƙwalla ta faɗi haka, Aunty Amnah ta ce “Amiiiiin ya Allah”, cigaba ta yi da faɗin “Juraiju na zaune ɗakinsa yana Ibada, sai ya ji hayaniyar mutane, kan ya yi wani motsin kirki wasu sun shigo ciki, wasu kuma suna waje sai izgilanci da zaginsa suke, da ya nemi ba’asi aka ce ai wata ya yi ma ciki har ta haihu, hankalinsa ya tashi sosai, duk yadda ya so ya kare kansa, amma suka ƙi yarda, suka rushe masa ginin ɗakinsa, sai ya nemi alfarmar da a zo da jaririn, sannan a ba shi damar zai yi sallar Nafila, suka ba shi, bayan ya gama sallar ya ɗaga hannu sama ya yi addu’a, sannan ya tashi ya je wurin wanda ke riƙe da jaririn, ɗan taɓa jaririn ya yi tare da tambayar sa “Kai, waye Babanka?”, cikin ikon Allah kuwa jariri ya ce “Mai kiwon awaki ne.”

Cike da farinciki Deena ta ce “Allahu Akbar, Allah ya wanke sa”, Aunty Amnah ta ce “Ƙwarai kuwa, da aka tuhumi mai kiwon awaki cewar jariri ya ce shi ne ubansa bai yi musu ba, jayayya kuwa sai ta ƙare, suka yi ta ba shi haƙuri, suka ce kuma zasu gina masa ɗaki wanda ya fi nasa na farko, ya ce shi dai ya fi son irin nasa. Mahaifiyarsa kuma ta zo suka yafi juna.”

Deena ta ce “Allah Sarki, lallai bakin uwa bala’i ne”, Aunty Amnah ta ce “Bala’i mai zaman kansa ma kuwa, don haka ki yi taka tsantsan, in dai abin da iyayenki ke so bai saɓa ma dokar Allah ba, toh kawai ki yi haƙuri ki bi shi, ba zaki taɓa taɓewa ba. Annabi Isma’il ma da mahaifinsa ya ce Allah ya umurce shi da ya yanka shi, cewa ya yi ‘Ya Babana, ka aikata abin da aka umurce ka da shi, Insha Allahu zaka same ni cikin masu haƙuri’, daga ƙarshe sai Allah ya fanshe shi ta hanyar aiko da ƙaton Rago daga sama, sannan ya yabe shi, kuma ya ɗaukaki darajarsa.”

Sai da Deena ta ɗan lumshe idanu kana ta ce “Lallai Annabawa sun yi haƙuri, muma Allah ya ƙara mana haƙuri, ya kuma bamu ikon yi musu biyayya sau da ƙafa”, Aunty Amnah ta ce “Amiiiiin ya Allah”, sun tattauna muhimman abubuwa da yawa, basu yi shirin barci ba sai da Deena ta ji a ranta duk hukuncin da Ummanta ta yanke ta ɗauke shi, idan ma ta hana ta haɗuwa da Deeni toh zata haƙura, ko da kuwa wannan damuwar zata kashe ta.

Aunty Amnah ma ta ɗaukar mata alƙawarin ita zata tsaya mata, har Allah ya sa Ummanta ta amince.

Deeni ma shi kaɗai sai tsara yadda zai haɗu da Deena ya ke, ya fi so su yi haɗuwa ta mutunci, bawai ta ɓoye-ɓoye ba ko satar hanya. Ɗaukar ma ransa ya yi zai je har inda Deena ta ke, ya gaida mahaifiyarta, sannan ya ga ɗansa. Bayan ya gama yanke wannan shawar ne ya tambayi Lalu “Kana ganin ya dace na je wurinsu Deena.?”

Tambaya ya maido mashi “Wurin su Deena kuma?”, Deeni ya ce “Eh, ka ga ai yana da kyau mu haɗu ko?”, ɗan taɓe baki gami da ɗaga kai Lalu ya yi “Eh, gaskiya kam ya kamata, kawai ni bana son mu cika cusa kai a wurinsu ne saboda mahaifiyarta, ka san matar nan sai a hankali, gwara muna kama kanmu.”

<< Mutuwar Tsaye 45

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×