Skip to content
Part 47 of 48 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Deeni ya ce “Gaskiya ne, Insha Allahu ba zamu yi abin da mutuncinmu zai zube ba, kuma wani hanzari Farouk, idan muna biye ma halin wasu mutanen ba zamu yi abin da ya kamata na zumunci ba, dole sai muna ɗauke kai”, Lalu ya ce “Haka ne, Insha Allahu zamu je, amma mu bari Hajjah ta zo, tunda gobe gobe ne zuwansu Insha Allah”, Deeni bai ƙi ba su tafi yanzu ma, amma dole ya bi shawarar ƙanensa, duk don a zauna lafiya.

Shi ma Lalu yana sane ya ce a bari sai Hajjah ta zo, saboda bai tarbi mahaifiyarsa a ƙasa mai tsarki ba, babu dalilin da zai sa ya tarbi mahaifiyar wani ko wata, musamman ma da ya kasance Maman Deena da bata ganin kowa da gashin arziki.

A can Nigeria kuwa Hajjah na can sun haɗa jaka ita da Yaya Asiya, don tuni sun karɓi ticket ɗinsu, ranar tafiya kawai suke jira ta zo. Hajiya Ummah da Salma kuwa tunda aka sa ranar kullum sai sun zo, dukkansu ji suke kamar su ma a tafi da su, don su biyu kaɗai za a bari, Salma ce ta kasa haƙuri, suna zaune a falon suna hira ta ce “Allah kuwa Hajjah sai nake jin ba daɗi”, Hajjah ta ce “Ba daɗin me kike ji Salma?”, kamar zata yi kuka ta ce “Ji nake kamar duk mu tafi tare, kewar ku duk ta hana ni sukuni”, Murmushi haɗe da ƴar ƙwafa Hajiya Ummah ta yi kafin ta ce “Kina iya faɗa ne a ji, nima ina jin kewar nan Salma, mu biyu kaɗai a gari? Mahaifiyarmu da sauran dangi duk a Saudiyya.”

Duk yadda suke ji, tuni Hajjah ta ji fiye da abin da suka ji, bata ƙi ba a ce duka ƴaƴanta su haɗu a wuri ɗaya, toh amma yadda Allah ya tsara shi ne daidai, tunda basu da ikon da zasu yi wannan, cike da tausar musu da zuciya ta ce “Ku ma Allah ya baku iko, kuma Saudiyya lokaci ne, da Allah ya nufa Insha Allahu zaku je”, Hajiya Ummah ta ce “Allah ya sa muna da rabo”, suka ce “Amiiiiin.”

Batun yadda gidan zai kasance idan Hajjah ta tafi suka ƙarasa tsarawa, inda Aunty Salma zata dawo nan ita da yaranta, tunda tana da abokiyar zama a gidanta, sannan mijinta ba mazauni bane. Aunty Salma ta ji daɗi sosai, kasantuwar rayuwar gidanta a ƴan kwanakin nan sai addu’a kawai, abubuwan duk sun ja baya sakamakon tsananin rayuwa da aka shiga, don ma Allah ya sa tana da yan’uwa masu rufin Asiri. Ɗan zaman da zata yi anan gidansu kuwa zata ji daɗi, tunda babu kalar abincin da babu, ko Khamis abincin da ya aiko musu da shi da kuɗi zai kai na dubu ɗari biyar. Sannan ga Gwaggo Salame da zata taya su zaman.

Ana cikin maganar ne Hajiya Ummah ta ce “Ga Salma, da kuma Salame duk a gida ɗaya”, me zasu yi kuwa idan ba dariya ba, Hajjah ta ce “Salmai ta yi tuwo, Salamatu kuma ta kaɗa miya”, Hajiya Ummah ta ce “Allah ya sa dai tuwon ya ciwu”, Bayan Gwaggo Salame ta gama dariya ta ce “Insha Allahu komai zai yi kyau, ai hannu da yawa maganin ƙazamar miya”, Hajjah ta ce “Allah ya sa.”

Washegari ranar tafiya mota biyu ta ƴan rakiya aka yi, Khamis ya ɗauki su Hajjah, Driven Yaya Asiya kuma ya kwashi sauran. Tun a gida suke matse ƴan ƙwallansu har aka zo Airport, Yaya Asiya ta ce ma Hajjah “Dan Allah ya isa haka Hajjah, duk inda muka je ai zamu dawo”, kai Hajjah ta girgiza “Ki bar ni kawai Asiya, ina tausayin Ummah da Salma ne”, itama tana tausayin ƴan’uwanta, don su ne marassa ƙarfin cikinsu, cewa ta yi “Toh ya za a yi Hajjah, kuma fa su ba yara ne ba, bare ayi zaton ko zasu sha wahala, kawai ki yi musu addu’a su ma”, Hajjah ta ce “Toh Allah ya hore musu suma”, Yaya Asiya ta ce “Amiiiiin ya Allah.” Lokacin da zasu rabu kuwa itama Yaya Asiyar sai da ta yi kukan tausayin ƴan’uwanta. Haka jirginsu ya tashi, duk ba wata walwala a tare da su.

A kan Hanya ne Khamis ya tsokani Salma, “Jirgi ya tashi ya bar Salame a tasha”, tana dariyar yaƙe ta ce “Hada tsokana ko Yaya Khamis”, dariya ya yi kafin ya ce “So nake in tunzura ki ai”, ta ce “Na nawa kuma, ai a tunzure nake, muma dai Allah ya hore mana”, Khamis ya ce “Amiiiiin”, magana ya basu sosai ita da Hajiya Ummah, inda ya nuna musu ko mutum na da iko sai idan Allah ya nufa, tunda shi ma ya so tafiya shi da iyalansa, amma ba a samu visa ba, don haka su daina damuwa. Kewa ce ma ba za a hana su ba, tunda duk rai an halicce ta da son kasancewa da wanda take so.

Su Deeni kuwa tuni sun shirya tabar mahifiyarsu a Jiddah, rayukansu cike da farincikin da baya misaltuwa, musamman Asma’u, Bashir ya lura da yadda ta kasa ɓoye farincikinta, ya sani, amma sai ya tambaye ta “Asmy, wannan murnar ta musamman fa?”, a ɗan shagwaɓe ta ce “Ka sani fa”, idanu ya ɗan ware “Me na sani”, ta ce “Ka san murnar zuwan su Hajjah nake, shi ne ka tambaye ni”, dariya ya yi “Na sani kam, so nake in ji daga bakinki ne.”

Lalu da Deeni suna gani, baki Lalu ya taɓe “Uhm”, Deeni na lura ya yi mashi dariya, ɗan raɗa mashi ya yi “Farouk, Allah ya aurar da kai ka huta da yi ma Asma’u jealous”, dariya Lalu ya yi, don tabbas ya san yana yi ma Asma’u kishi, duk lokacin da ya ga sun buga wata soyayyar sai ya ji shi ma yana son ya yi aure.

Deeni ma fama masa ciwon da ke ransa suke yi, don ma zuwansa Saudiyya ya samu sauƙin damuwar sosai, ba komai ne ake yi yanzu ya dame shi ba.

Da misalin ƙarfe huɗun yamma jirgin su Hajja ya sauka, murna kuwa a wurinsu kamar sun taka dutsen Arfa, Asma’u kuwa tunda ta maƙale Hajjah sai ƙwallah, ba wannan ne damuwarsu ba, ƙin sakin Hajja da ta yi ne, Farouk da bai gani ya ƙyale ya ce “Ke dallah ki sakar mana ita, tunda ba ke kaɗai ke da ita ba”, tafka Yaya Asiya ta kai mashi a kafaɗa tana dariya “Farouk baka son a zauna lafiya ko?”, yana dariya ya ce “Haba toh, muma duk mun yi kewar uwarmu ai”, hannun Hajjah cikin na Asma’u ta ce “Farouk bana son iya shege fa”, dariya duk suka yi, Asma’u kuwa tana haɗa idanu da Bashir ya yi mata signal ɗin kada ta ce komai.

Masaukinsu da tuni an tanadar ma su Hajja suka sauka, kimtsawa suka yi, sannan suka suka ɗunguma sai masallaci domin gabatar da sallar magrib, Hajjah da Yaya Asiya da Asma’u wuri ɗaya suka zauna, inda suka sanya Hajjah tsakiya, daɗi cikin ransu ba a magana, duk da a ƙasan rayukansu akwai kewar Hajiya Ummah da Aunty Salma, Asma’u ce ta kasa yin haƙuri ta ce “Allah Sarki, Ummi da Aunty Salma suna can”, Hajjah ta ce “Ke dai bari Auta, nima su ne a raina”, Yaya Asiya ta ce “Lokaci ne, su ma Insha Allahu watarana da su za a yi”, Hajjah ta ce “Allah ya sa.”

Sai da aka yi tarawihi sannan suka koma masaukinsu Hajjah. Tamkar ƙaramin yaro haka Deeni ya zauna a gefen Hajjah daga ƙasa, inda take zaune a gefen gado, maganar ciwon idanunsa aka yi, Hajjah ta ce “Masha Allah, na ga idanu sun yi kyau”, Yaya Asiya ta ce “Aikuwa ba, gaskiya hospital ɗin sun san kan aikinsu”, Hajjah ta ce “Lallai kuwa, Allah ya ƙara lafiya Amiiiin.”

Uwa mai daɗi, zagaye Hajjah suka yi hada Bashir, suna ta hirar yaushe gamo, ita kuwa daɗi cike da ranta, addu’a ta yi musu gabaɗayansu, hada su Hajiya Ummah dake gida.

Can wurin sha-biyu ne Bashir ya ce zai koma ɗakinsu, jirin-jirin Asma’u ta yi da idanu, don idan ta san kunya ba zata bar shi ya tafi shi kaɗai ba, shi ma a ƙasan ransa yana son ya ganta, toh amma kunya yake ji.

 Yaya Asiya mutum ce mai kula, duban Asma’u da ke zaune a bayan Hajjah ta yi “Zaman me kike, mijinki zai tafi”, baki ta ɗan turo “Ba komai”, Bashir kuwa har ya kai ƙofa zai fita, “Ka jira ta mana”, Inji Deeni, da ya lura da kunge kan da ya ke yi.

“A’a, yau wurin Hajjah zaki kwana ko?”, Bashir ya faɗa yana duban Asma’u, ɗaga kai ta yi “Eh”, tana dariya, harara Lalu ya watsa mata, “Ke tashi ki bi mijinki kin ji ko?”, aikuwa dama a ƙule take da shi “Wai kai miye haɗinka da ni ne”, ta faɗa kamar zata yi kuka, kowa kuwa sai da ya ji haushin Lalu, Hajjah ta ce “Farouk ka daina matsa ma ƴata mana”, shi a ransa ba da wata manufa ya yi ba, amma fahimtar an ji haushinsa sai ya ɗan sha mur, “Uhm”, kaɗai ya ce, ya zuba musu idanu.

Baki a zumɓure Asma’u ta sauko daga kan gadon, mayafin rigarta ta roller, sannan ta zura takalma, Bashir na kallon ta ya yi dariya “Saki fuskar mana, dawowa zaki yi yanzu”, aikuwa a take ta saki fuska “Da gaske?”, ya ce “Yeah”, duban Hajjah ta yi “Hajjah bari in je”, ta ce “A dawo lafiya.”

Wayarta ta ɗauka ta yi gaba, tana zuwa ta riƙo hannun mijinta suka fice, inda suka bi ta da idanu. Dariya su duka suka yi, Deeni ya ce “Auntar nan ta ki akwai rigima Hajjah”, ya ƙarashe maganar yana duban Hajjah da farinciki ganin Asma’u da soyayyar miji ta mamaye.

Yaya Asiya ce ta ba shi Amsa da “Ai ta samu daidai ita, don alamu sun nuna tana jin daɗin zama da shi”, Hajjah ta ce “Alamu kam sun nuna.”, Lalu da Deeni ne suka yi ta labarta musu irin kulawar da Bashir ke nuna ma Asma’u, wanda in dai aka ɗore a haka, toh Asma’u ta dace gidan aure.

Asma’u da Bashir basu ce ma juna komai ba sai da suka shiga ɗaki, zama Bashir ya yi a gefen gado tare da riƙo hannunta itama ta zauna gefensa, ƙuri ya yi ma idanunta da suka shashshaɓe alamar zata yi kuka. A yanzu kam wannan kallon bai ƙayatar da Asma’u ba, don ba shi ke gabanta ba, burinta shi ne ta ganta cikin family ɗinta, ba wai da shi ba, tambayar sa ta yi “Lafiya?”, ɗan guntun murmushi ya yi, sannan ya sa hannu ya goge guntun hawayen da suka leƙo a gefen idanunta “Ke zan tambaya lafiya.?”

Hannunta a kan nasa da har yanzu bai janye a fuskarta ba ta dafa “Lalu ne mana”, ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka, baki ya ɗan taɓe “Toh sai miye idan Lalu ne, ke baki san wasa ba?”, ta ce “Ya matsa mani fa”, ya ce “Ba wani matsawa, ni bana son shagwaɓa”, aikuwa ta janye mashi hannu “Ni ce nake shagwaɓar?”, rufe bakinta ya yi daidai da zubar hawaye a ƙumcinta, abin da yake son gani kenan, jawo ta ya yi a jikinsa haɗe ɗan bubbuga bayanta kamar ƙaramar yarinya, “Toh ina son shagwaɓa, yi mai isar ki my Asmy”, kuka take, amma bata san lokacin da tuntsire da dariya ba, ɗan leƙa fuskarta ya yi yana dariyar shi ma “Ya aka yi ?”, ba tare da ta daina dariyar ba ta ce “Kai ne mana ka sanya ni dariya”, haka dama yake so, tsokarnarta ya cigaba da yi har sai da ta dayaye. Sanin zuciyarta na wurin mahaifiyarta ne ya ce “Mu je in raka ki wurin Hajjah ko?”, kai ta ɗaga alamar “Eh”, sai kuma ta ɗora da faɗin “Toh amma kai da wa zaka kwana?”, tambaya ya maido mata “Dama ana barci a wannan kwanakin goma na Ramadan?”, kai ta girgiza “A’a”, ya ce “Toh kin gani ko da kina nan masallaci zamu kwana”, Asma’u na dariya ta ce “Haka ne.”

Daidaita jikinta ta yi, sannan ya raka ta har wurin mahaifiyarta, dawowa ya yi daƙinsu ya cigaba da aikinsa a system ɗinsa.

Deena kuwa tuni ta matsa ma Aunty Amnah ta faɗa ma Ummanta su Deeni na nan ƙasa mai tsarki, aikuwa ana faɗa mata ta yi ma Deena kallon tuhuma “Ta ina kuka san suna nan su ma?”, a dake Deena ta ce “Shi ya faɗa Mani”, Aunty Amnah ta ji daɗin ƙarfin halin da Deena ta yi, jinjina kai ta yi sannan ta ce “Daga India suka zo nan ko?”, Deena ta ce “Eh”, kai Ummanta ta ɗan jinjina, bata kuma yi mamaki ba dan Deena ta ce shi ya faɗa mata, tunda ta san suna waya, ƙyale ta kawai take don kada zafin ya yi mata yawa. Tamkar babu komai a ranta ta yi ta jefa ma Deena tambaya a kan shi, da taimakon Aunty Amnah kuwa Deena ta yi ta bata amsar da ta dace game da lafiyarsa, daga ƙarshe ta ce “Toh Allah ya kyauta gaba”, suka ce “Amiiiiin.”

Duban Raihan da ke a hannun Aunty Amnah ta yi, “Ashe da rabon tsohon ka ya ganka a duniyar ga”, Aunty Amnah ta ce “Lallai kuwa dai, ai zai je ya ga babansa ko?”, Aunty Amnah ta ƙarashe da tambayar ta “Toh me zai hana, yanzu suna ina ne?”, Aunty Amnah ta ce dubi Deena “Nan Madeena ko? Hada Mahaifiyarsu”, Deena ta ce “Eh”, rausaya kai Ummanta ta yi alamar “Toh”, Duk da bata sake magana ba, amma hakan ya yi ma Deena daɗi sosai a ranta, don kuwa alamu sun nuna Ummanta ta fara saukowa dangane da al’amarin Deeni.

Wurin sha-biyun dare suka shirya tsaf domin tafiya Masallaci yin Tahajjud, gaɓadaya suka ɗunguma suka tafi, inda mazan suka nufi bangarensu, Deena da mahifiyarta da Aunty Amnah ma suka nufi wurin mata, don kishi ya hana su haɗewa da sauran matan Alhaji Lawan da iyalansu, iyakar su da juna gaisuwa idan an haɗu, amma kowa ramin kura ce, daga ita sai ƴaƴanta. Wannan rabuwar kai kuma ba da son Alhaji Lawan ba, kawai dai abin ne ya fi ƙarfinsa, kuma hakan ne kaɗai ke sa su zauna lafiya.

Duk da fita da wurin da suke ganin sun yi, amma sai da suka iske tarin jama’a, don kuwa duk irin sammakon mutum a irin waɗannan wuraren masu daraja, toh zai taras da wasu a nan suka kwana, sai dai mutum yayi iya ƙoƙarinsa kawai, sauran kuma ya bar ma Allah kayansa.

Sahu ɗaya suka su uku suka zauna, sai Raihan da ke hannun Deena tana ba shi Mama, a gefenta kuma akwai worker da ake masa dubara a kwantar da shi, idan Allah ya sa ya yi barci, don mahaifiyarsa ta samu damar yin Sallah, tsit suka yi, suna ta ambaton Allah a cikin zukatansu, lokaci ɗaya kuma suna jiran a fara sallah, “Deena, har yanzu bai yi barci ba.?”

Sunan Deena da Aunty Amnah ta faɗa ne ya ratsa kunnuwan su Hajjah da ke sahun gaban na su Deena, gabaɗaya suka waigo domin ganin idan Deenar da suke tsammani ce, tunda an faɗa musu tana nan Madina itama..

 

 

 

 

 

<< Mutuwar Tsaye 46Mutuwar Tsaye 48 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×