Cike da tsananin farinciki Asma'u ta furta "Laa! Dee-dee", wannan ne ya ja hankalinsu Deena har suka lura da ko su waye a gabansu. Itama Deena cike da murnar ta ga waɗanda take nema ta ce "Ƙawa! Ku ne dama a gaba?."
Umman Deena kuwa faɗuwar gaba ce ta riske ta, musamman da suka yi ido huɗu da Yaya Asiya, domin kuwa ita dodonniyar ta ce, duk tsaurin halin Umman Deena, toh tana shakkar Yaya Asiya, domin ko a fuska bata ɗaukar rainin da Umman Deena ke musu. Ta bangaren Yaya Asiya ma irin firgicin. . .