"Aure ya karɓi Asma'u", in ji Umman Deena da Asma'u ta tsare ma rai, Aunty Amnah ta ce "Ta yi sa'ar miji ne, Bashir ba daga baya ai", Umman Deena ta ce "Lallai kam", shiru suka ɗan yi, kowa da abin da yake saƙawa a ransa.
Aunty Amnah ce ta kasa haƙuri ta ce "Ni kam na ce bah!", sai kuma ta yi shiru, ko da jin haka Umman Deena ta san akwai magana a bakinta, cewa ta yi "Ina jin ki", cike da fargaba Aunty Amnah ta ce "Maganar Deena ne, me zai. . .