Ɗif wutarsu ta ɗauke, musamman Deeni da kan Hajjah ke akan cinyarsa, "Ta rasu ko?", cike da firgici Yaya Asiya ta tambaye shi, kai ya ɗaga a hankali tare da lumshe idanunsa da suke ta tsatstsafar da hawaye, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Lahaula wala ƙuwatta illah billah", Yaya Asiya da Lalu suka riƙa faɗi, Asma'u kuwa tana fara sallallami ta sarƙe, bata ƙarasa ba ta fasa wata ƙara tare da sulalewa ƙasa iskoki sun bige ta, da hanzari Yaya Asiya ta yi kanta tana kuka, kasa taɓuka komai ta yi duk da fizge. . .