Su Deeni sun ga kara da karamci a wurin jama'a, don kuwa har wanda basa zato, da waɗanda ma basu sani ba sai da suka zo musu gaisuwa, kasantuwar Hajjah mutuniyar jama'a ce, sannan abin duniya baya rufe mata idanu, ta na yin kyauta ne da abin da ba a san tana da shi ba, aikuwa mutane sun yi kukan rashin ta. Wata mata ƴar gudun hijira da ta zo tana kuka tana faɗin "Yanzu mai bamu abinci ta tafi, bamu san ya zamu yi ba", Hajiya Ummah ce ta bata haƙuri tare da fa. . .