Skip to content
Part 6 of 31 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Aiki Deena take, amma gabaɗaya hankalinta na wurin Deeni, don ta fahimci duk lokacin da ya samu kansa shi kaɗai, toh sai ya afka a kogon tunani.

Duban sabuwar mai aikin da Yaya Asiya ta kawo mata ta yi, wanda tun bayan gaisuwa basu sake magana ba saboda rashin sabawa, kasantuwar wannan ne karo na biyu da Deena ta taɓa ganin dattijuwar matar.

Duban ta Deena ta yi “Aunty Yaha, bari in ɗan dawo dan Allah”, Tamkar ƴa haka Aunty Yaha take jin Deena, saboda ladabi da kuma shiga ran da Deena take da shi “Ba damuwa Deena, sai kin fito”, Aunty Yaha ta faɗa bayan ta aje cup ɗin dake hannunta a cikin ruwan wanke-wanke.

Kai tsaye bedroom Deena ta nufa, kwance ta samu Deeni a kan sofa ya lulluɓe fuskarsa da wani handkerchief, rashin amsa sallamar da ta yi ne ya tabbatar mata da bai ji shigowar ta ba.

Cike da damuwa ta zauna zauna ƙasa, ɗan dafo shi ta yi, muryarta a raunace ta ce “Yaya, bacci kake?”, shirun da yayi ne ya bata damar yaye handkerchief ɗin, aikuwa firgit ya dawo daga hayyancinsa, gyara kwanciyarsa ya yi akan kafaɗa yana fuskantar inda ta ke, cikin disashewar murya ya ce “Har kin gama aikin?” Kai ta girgiza duk da ta san baya ganin ta “A’a, bacci ka yi ne.?”

Tabbas idan ya nuna mata zurfin tunani ya faɗa, toh akwai damuwa, cikin basaja ya ce “Yeah, fitarki kenan bacci ya fizge ni” ya ƙarashe maganar hannunsa cikin nata.

Bata san me ya sa ta kasa gasgata cewar bacci yake ba, saboda ta fi kowa sanin motsi kaɗan ke tada shi daga bacci, ɗan shiru suka yi, daga bisani ta ƙara sassauta murya “Yaya”, 

A yadda ta ambaci sunan ne ya gane magana take son yi, attention ɗinsa ya bata ta hanyar faɗin sunan da ta fi so “Ina jin ki my Golden Deena,” aikuwa ta ƙara marairaicewa “Dan Allah kada ka bari tunani ya zaunar maka a rai.”

Ya san ta san abin da bai yiwuwa ne ace kada mai irin wannan lalurar ya yi tunani, don haka bai ɓoye mata ba ya ce “Deena, dole ne in yi tunani, saboda alamu sun nuna komai nawa ya tsaya, ki yi imagining lafiyata ƙalau, da yanzu ina wurin aiki ko?”

Kai ta rausaya “Uhmm”, ya ce “Toh yanzu one week ina zaune gida, kuma ban san yaushe zan warke ba har in koma aiki ba, sai a ce kada in yi tunani Deena?”

Tunda ya fara magana take kallon sa, ba muryarsa kaɗai ba, hatta idanunsa sun nuna emotionally yake maganar.

A hankali Deena ta lumshe idanu tare da haɗe wani yawu marar daɗi da ya tsatstsafo mata a baki.

Amsar maganar shi ta ba shi “A’a, tunani dole ne fa”, ya ce “Yauwa my Dee-Dee, zaman gidan ko da lafiya gajiya ake”, ta ce “Haka ne, Allah ya baka lafiya Yaya”, ya ce “Amiiin ya Allah.”

Zaunen da ya tashi ne ya sa ta komawa kan kujerar ta zauna a gefensa, ɗan kwantar da kanta ta yi a kan kafaɗarsa suka cigaba da magana, inda ya tambaye ta “Ina kika baro ƴar aikin?”

Murya can ciki ta ce “Tana kitchen”, sake tambayar ta ya yi “Halan ta maki ko?”, ranta ba daɗi ta ce “Eh ta yi sosai, amma ni fa bana son ƴar aiki”, haƙuri ya bata, tare da nuna mata ƴar aikin na da matuƙar amfani, don zata rage mata aiki da kuma tunani, tunda shi ba cikakkiyar lafiya ne da shi ba.

Wayarshi dake saman kan kujera ce shiga ruri, miƙo mashi ta yi tare da faɗa mashi Medical Director ɗinsu ne. Cike da ladabi Deeni ya amsa sallamar da MD ɗin ya yi gami da gaishe shi, daga can cikin kulawa MD ya amsa, lokaci ɗaya kuma ya ce “Ya kuma wannan jarabawa da ta same ka, ko kuma ma ta same mu bakiɗaya?”

Yadda MD ɗin ya yi magana kamar Uba ne ya karyar ma Deeni da zuciya, cikin sanyin jiki ya ce “Jarabawa sai godiya yallaɓai, amma ana cikinta” daga can MD ya ce “Allah Sarki, Allah ya baka lafiya, anjima Insha Allah ni da sauran staff zamu shigo ganinka” cike da jin daɗi Deeni ya ce “Nagode sosai Yallaɓai, Allah ya kawo ku lafiya”, MD ya ce “Amiiiiin Dr”, daga nan suka yi sallama.

Kallon Deena ya yi da zuciya, “Kin ji anjima zasu zo gani na”, kai Deena ta jinjina “Allah ya kawo su lafiya, bari in je mu ƙarasa aikin da Aunty Yaha.”

Tashi ta yi kamar yadda ta faɗa ta koma kitchen, Deeni kuma ɗan zamewa ya yi tare da kwantar da kansa ga bayan kujera, daga inda ya tsaya a tunani ya dasa, a hankali zuciya ta hakaito mashi zamansa a office, da irin aika-aikacen da ya saba yi, “Allah Sarki, yanzu wannan ya zama tarihi kenan.?”

Wasu ƙwalla masu kauri da kuma zafi ne suka ɓuɓɓugo mashi a idanu, wanda shi kanshi ya san wahala ce tsayar da su, don haka ne ya bar su suka cigaba da malala a kumcinsa, saboda rashin fitarsa aikin nan shi ne babban abin da ya fi taɓa mashi zuciya, kasantuwar da shi ne yake riƙe da duk wanda ke da haƙƙi a kansa, kuma abu ne mai sauƙin gaske ya rasa shi madamar bai samu lafiya ba. Addu’a ya shiga yi a fili da kuma ɓoye, domin ya gama tabbatar da cewar ya yi mutuwar tsaye.

A irin wannan lokacin ne kuma Mahaifiyar shi ta kai maƙura wurin kai kokenta a wurin Allah, a cikin sallarta ta Walha, domin kuwa a wurin Allah ne kaɗai zata kai maƙurar kukunta ba tare da wani ya tambaye ta don me ba, shi ya sa duk lokacin da take ganawa da Ubangiji Allah, ko kuma ta kasance ita kaɗai, toh sai ta zubar ma ɗanta da hawayen tausayi, tare da nema masa lafiya a wurin Allah mai duka.

“Allah gareka muke bauta, kuma gareka muke neman taimako, ina roƙon ka da sunayenka kyawawa, da kuma siffofinka tsarkaka, da ka ba Deeni lafiya, don rahamar ka da jin ƙanka ya Allah”, goshinta na ƙasa ta cigaba da wannan addu’a, da ma sauran wasu addu’oin, lokaci ɗaya kuma idanunta na cigaba da buɓɓugar da ruwan hawaye.

Asma’u na shigowa ta ji sautin kukan mahaifiyarsu da ke fitowa a cikin sujudar da take, sosai ruɗu ya mantar da ita abin da ya kawo ta ɗakin, sai dai ta fice ɗakin tana kuka itama, ɗayan ɗakinsu ta shiga tare da zama a gefen gado, a cikin ranta ta ce “Allah ka san kalar jarabawar da ta same mu, Allah ka bamu ikon samun nasara a kanta Amiiin.”

Kuka sosai ta riƙa yi, har sai da muryar Hajiyarsu ta dakatar da ita ta hanyar kiran ta, da hanzari ta share hawayen sannan ta je, “Gani Hajja”, ta faɗa tare da zama a gabanta.

Kallon tausayin junansu suka yi, daga bisani ta ce “Farouk zaki kira mani”, cike da ladabi ta ce “Toh, amma me za a yi maki?”, Murya a raunace ta ce “Gidan Deeni zai kai ni, so nake na ga wane hali yake ciki.”

Kamar Asma’u zata yi wani kukan ta ce “Eh gaskiya Hajja, gwara ki je, nima hankalina ya ƙi kwanciya”, wayar Lalu aka kira, suka yi sa’a kuwa yana kusa, don haka ya ɗauko mai napep ya zo suka tafi.

Deena ta fito daga kitchen kenan ta ji ana knocking, buɗewa ta yi, da Mamaki sai ta ga su Hajiyarsu, da kuma ƙanwar Hajiyarsu Deeni mai suna Hajiya Yalwa, Deena ta ji daɗin ganinsu sosai, musamman da ya kasance tare da Asma’u, sannu da zuwa ta yi musu,, bayan sun amsa ne suka shigo tare da zama a falo.

Ciki ta shiga ta faɗa ma Deeni ga su Hajiyarsu nan sun zo, wani irin farinciki ya samu kansa a ciki wanda ya sassauta mashi riƙewar da zuciyar shi ta yi, jagora ta yi mashi suka fita.

Gabaɗaya babu wanda bai zubar ma Deeni da hawaye ba, sai dai Hajiyarsu da a koda yaushe tana ƙoƙarin danne damuwarta a gaban mutane, sai dai idan ta keɓe ita kaɗai ne ko cikin sallah sai ta ci kukanta son rai.

Har inda suke zaune kan two seater Deena ta kai shi, guiwa har ƙasa ya durƙusa “Hajiya Sannunku da zuwa”, daƙyar Hajiyarsu ta iya cewa “Yauwa Deeni”, Hajiya Yalwa kuwa kuka ta fashe da shi, dafa kafaɗar shi ta yi “Sannu Deeni, Allah ya baka lafiya”, cikin muryaryar kuka ya ce “Amiin Hajiya, nagode sosai.”

Gaisuwa irin ta ɗa da iyayensa suka yi, sannan Lalu ya taimaka mashi ya zauna a kan kujera one seater. Deena ma har ƙasa ta gaishe su, cike da ƙaunar ta suka amsa, tare da sanya mata albarka, don suna da yaƙinin a tsaye take wurin kula da Deeni, duk da nauyin juna biyu, ga ƙarancin shekaru, don almost shekarunta ba zasu wuce ashirin ba a duniya.

Asma’u da Lalu ma gaida Deeni suka yi, cike da ƙaunar ƴan’uwanshi ya amsa, sai kuma ya yi shiru, Hajiyar ce ta katse shi da faɗin “Cewa muka yi bari mu zo mu ganka”, yadda ta ƙarashe maganar ne ya sa mashi karayar zuciya.

Idanunsa a lumshe ya ce “Na gode sosai’, a ranshi kuma yana ƙara gode ma Allah da ya sa mahaifiyarsu na raye, ƙila da bai san ya zai yi ba.

Mai aikin Deena ce ta zo suka gaisa, a nan ta jajanta ma musu halin da Deeni yake ciki. Bayan ta koma kitchen ne Hajiyarsu ta dubi Deena da ke zaune a hannun kujerar da Asma’u ke zaune akai ta ce “Yauwa, gwara da aka samo mai aikin, kin ga zata rage maki aikin gida”, kai Deena ta ɗan jinjina tana ƴar dariya.

Da kaɗan-kaɗan suka yi ta hira, nan yake faɗa mata cewar sun yi waya da a ƴan asibitinsu, sun ce Yau zasu zo, addu’a ta yi Allah ya sa su duba lamarinshi, Saboda babu mai son ya rasa aikinsa.

Zam-zam ɗin da suka zo dashi ne Hajiya Yalwa ta fiddo tare da miƙa ma Hajiyarsu Deeni “Gashi ki sa mashi da kanki”, ta yi hakane saboda ta bar uwa ta ji ƙan ɗanta.

Bata yi musu ba ta karɓa, miƙewa ta yi ta dogara sandarta ta je a gaban Deeni, tamkar ƙaramin yaro ta dafa kanshi, a yadda ta ga ƙwayar idanun Deeni ta sauya kamannu sai da kanta ya juya, da juriya ta ɗiga mashi Zam-zam ɗin mai ɗauke da Ayatu shiffa’a, miƙa ma Deena ragowar ta yi, sannan ta yi kashi addu’r samun lafiya. Ba tare da sake zama ba ta ce “Mu je gida ko.?”

Shirin tafiya suka yi, in banda Asma’u da ta ce ita ba yanzu ba. Deeni ya so su tsaya a gama girki, amma suka ce ce a’a.

Har ƙofa Deeni ya raka su, sun fito kenan sai ga tawagar colleagues ɗinsu Deeni a mota biyu, cike da girmamawa suka gaishe da su Hajiyar tare da yi musu jajen wannan abu da ya faru.

Sosai ta yi musu godiya, sannan suka shiga motar Deeni suka tafi.

Ciki duk tawagar suka shiga, MD da kansa ya taimaka ma Deeni suka zauna a kan kujera ɗaya, cike da tausayin Deeni ya dafa kafaɗar shi “Sannu Dr, Allah ya baka lafiya”, Deeni ya ce “Amiiin ya Allah, thank you Sir”

Gaisawa suka yi, inda sauran Colleagues ɗin duk suka jajanta mashi tare da nuna zallar tausayinsu a fili, in banda Dr. Bello da ke jin kamar an yi mashi bushara.

Deena da Asma’u ne suka kawo masu gaisuwa, bayan sun gaisa ne MD ya dubi Deena “Sorry kin ji daughter, Allah ya bashi lafiya”, kanta na ƙasa ta ce “Amiiin Sir, mun gode sosai.”

Sosai Deena ta yi mamakin yau Dr. Bello bai ƙure ta da kallo ba, may be dan yana cikin mutane ne. Asma’u kuwa ji take kamar a kan ƙaya take, don haka ta riga Deena yin gaba ma.

Bayan Deena ta wuce ne MD ya nemi ba’asin inda neman maganin Deeni ya tsaya, Deeni ya ce “Mun je eye center, ranar Monday zamu koma Insha Allahu”, MD ya ce “Okay, toh batun sauƙi fa?”, Wasu daga cikin mutanen da suke zaune sun yi na’am da tambayar MD, don ba zuwan asibitin ba, shin ana samun sauƙi.?

Cikin yanke tsammani Deeni ya ce “Toh har yanzu dai ba wani chanji Sir”, girgiza kai MD ya yi “Okay, toh zuwa Monday ɗin ka koma, muma a ranar ne zamu yi meeting mu ga me ya kamata mu yi, don two-days ɗinnan da baka nan, abubuwan duk sai a hankali.”

Kallon juna Dr. Bello da Jabiru suka yi “Tunda mu mahaukata ne ba ma’aikata ba ko”, Dr. Bello ya faɗa a ranshi.

Sosai MD ya yi ma Deeni kyawawan albishir a kan zasu taimaka masa ya samu lafiya da Iznin Allah. Godiya sosai Deeni ya yi musu a lokacin da zasu tafi.

Bayan fitarsu ne MD ya dubi Bello “Ka haɗa mani kan staff on Monday, zamu yi zama sosai a kan Deeni.”

Ta ɓangaren mahaifiyar Deena kuwa ta shiga ruɗani, akai-akai tana kiran Deena da Deeni ita da jama’arta, babban burinta kuma shi ne ta dawo ta ga wane hali Deena take ciki, saboda a yadda ta san Deena da saka damuwa a rai, tana da yaƙinin tana can duk ta rame. Washegarin ranar da suka dawo ne Driver ya ɗauko su ita da ƙawarta suka nufo gidan Deena

Tuni Deena ta san da zuwan su, kuma ita dama ba a bin ta bashin kula da gida, don haka ko ina tsaf-tsaf, Deeni ma falo ya dawo da zama, ba a fi minto ci ba sai ga motarsu ta yi paking a ƙofar gidan.

Deena na jin knocking dama tana a bakin ƙofar sai taje ta buɗe musu, cike da ƙaunar mahaifiyarta ta rungume ta, sannan ta rungume Aunty Hafsat sannan suka ƙaraso ciki.

Da sautin muryarsu Derbo ya gane a kan kujera two seater suke zaune, don haka sai da ya durƙusa yana fuskantar su tare da gaishe su. 

Cike da kulawa suka amsa, sannan Umman Deena ta ce “Ya jikin?”, Ya amsa “Da sauƙi”, Aunty Hafsat ta ce “Allah ya baka lafiya Deeni”, ya ce “Amiin, nagode sosai Aunty Hafsat.”

Bayan ya koma ya zauna ne Umman Deena ta ce “Haka kawu Sanusi fa ya yi, shima lafiya ƙalau ya je kasuwa, amma sai gashi an maido shi gida baya gani”, cike da mamaki Aunty Hafsah ta ce “Ko mi ke kawo wannan sudden blindeness ɗin?”, da yake Umman Deena tana da ilimi sosai, nan ta shiga zayyana musu irin cutukan da suke kawo sudden blindeness.

Sun dai sha hira sosai, daga nan Deeni ya ce ma Deena ciki zai koma, Jagorar da ta yi mashi ne ya ƙara basu mamaki da tausayinsa, Aunty Hafsat ta ce “Allah Sarki, abin tausayi”, Umman Deena ta ce “Ke dai bari, mutum ba komai bane wallahi, kuma dai bawa bai wuce ƙaddararsa.”

Suna ta jajanta maganar ne Deena ta dawo, Tambayar ta suka shiga yi ya batun aikin Deeni? Nan ta faɗa musu ai bai sake fita ba, Umman Deena ta ce “Toh ai ba batun fita kam sai lafiya ta samu.”

Ta sha tambayoyi sosai dai, har suke zaton ko bata lafiya don duk ta rame.

Aunty Yaha ma da ta gaida su, sai da suka bi daddiƙin inda aka samo ta, Deena ta faɗa musu Yaya Asiya ƙanwar Deeni ce ta samo mata ita, Aunty Hafsat ta ce “Tun yaushe?”, Deena ta ce “Bayan abin ya faru”, baki su duka suka taɓe, Umman Deena ta ce “Hmm.”

Burinsu kawai su samu mafakar da zasu fake wurin raba auren Deena, ita kuma da ta ga alama sai ta riƙa ɓoye wasu abubuwan, wanda dama ita a wurinta ba matsala bane.

Sun ɗan daɗe a gidan har suka ci lafiyayyen abincin da aka shirya musu. Bayan sun yi shirin tafiya ne Deeni ne ya zo suka yi bankwana.

Har a waje Deena ta raka su tana musu Allah ya kiyaye. Bayan sun shiga mota ne Aunty Hafsat ta dubi Umman Deena “Toh wai haka zata ƙare a ƴar jagora?”

<< Mutuwar Tsaye 5Mutuwar Tsaye 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×