Skip to content
Part 7 of 36 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Irin amsar da Aunty Hafsah ke son ji ta samu a bakin Umman Deena, cewar “Kema kin san abin da ba zai yiwu bane, kawai dai mu zuba musu ido har mu ga ƙarshen gudun ruwansu.”

Kai Aunty Hafsah ta rausaya, ranta cike da zuga ta ce “Ah toh! Idan kin bar ta dai wahala ce zata kashe maki ita da ƙuruciya, don haka ya rage naki, ko kuma in ce ya rage namu, tunda ƴar ba taki ce ke kaɗai ba”, sosai maganar ta taɓa ma Umman Deena zuciya, shiru ta ɗan yi tana nazarin ta wace hanya zata raba ƴar gudaliyar ƴarta daga wahalar da suke ganin tana ciki, bata kai ga samun mafita ba Aunty Hafsat ta katse ta da faɗin “Kuma ki duba a can baya fa ita kaɗai take aikin gida kamar baiwa, sai yanzu zasu wani nemo mata tsohuwa su haɗa ta da ita da sunan ƴar aiki.”

Duk halin Umman Deena na ɗaukar zuga a wasu times ɗin ta san abin da ya kamata, cewa ta yi “Aikin gida ba wani abu bane, tunda ita mace ce, kawai ni Family ɗin da take ciki ne sam bana so, ina son ta fita inda duniya zata san ta, ba inda za a ƙumshe mani ita a gida ba, babu inda take zuwa sai gidan dangi.”

‘Yar dariya Aunty Hafsat ta yi tare da ɗauke idanunta akan titin da take kallo ta glass ɗin mota, duban Umman Deena ta yi “Wallahi kuwa, ƴar bokon nan ma sun ƙi su bari ta cigaba, suna nufin daga NCE ta gama”, cikin fusata Umman Deena ta ce “Kuma su ga ƴarsu can ta dasa D.E”, da mamaki Aunty Hafsat ta ce “Wai Asma’un?” Umman Deena ta ce “Ita fa, ai na rantse da Allah da sakel.”

Irin wannan fusatar ce Aunty Hafsat ke son ganin Umman Deena ta yi, ranta fal da farin ciki ta ce “Ah toh, dubara ta rage ga mai shiga rijiya.”

Duk surutan da suke akan kunnen drivernsu, ransa cike da haushin Aunty Hafsat ya ƙarasa karin maganar da cewa “….Ko ya shiga ta ka, ko ta ƙafafu ma duk ɗaya”, a ranshi ya yi wannan maganar, don ya daɗe da fahimtar idan Umman Deena bata yi sannu ba, toh sai makircin Aunty Hafsat ya kai ta ya baro, don kuwa bai taɓa jin ta ba Umman Deena shawarar arziki ba, tunda shi ne ke kai su duk wata unguwa ta kusa da ta nesa.

Don ya katse hirar ne suna zuwa dab da round ɗin da zai iya kai su maban-bantan unguwanni ya ce “Hajiya gida muka nufa ko ina.?”, Amsa Umman Deena ta ba shi “Kai mu gidansu Deeni mu yi ma mahaifiyarsu jaje.”

Aunty Hafsah ta ce “Gaskiya ya kamata, dama ina son yi maki maganar cewa yau she zamu je”, Umman Deena ta ce “Ai gwara mu je yau mu ture, daga gobe Monday Commitments ɗina sun ƙaru, bani da time ɗin da zan yi ta zirga-zirga gidan kowa.”

Traffic lights ɗin da suka tsaya ne ya katse musu hirar, inda Umman Deena ta maida hankalinta a kan phone yayin da ta shiga Instagram, Aunty Hafsat da driver kuma a waje suka maida idanunsu suna kallon motoci da mashinan da suke jiran damar tafiya.

Vedion da Umman Deena ta yi playing ne ya dawo ma Aunty Hafsat da hankalnta ga phone ɗin Umman Deena, cike da mamaki suke kallon yadda ƙawa ke yi ma ƙawarta terere a media kawai dan sun samu saɓani, har motarsu ta tafi ba tare da sun sani ba.

Sai da vedion ya kai ƙarshe ne Umman Deena ta nisa tare da faɗin “Zama celeb ko bala’i”, Aunty Hafsat ta ce “Ke dai bari, kuma fa ƙawaye ne sosai”, Umman Deena ta ce “Aikuwa tir da irin wannan ƙawancen da ba rufin asiri a ciki.”

Baki Malam Garba ya taɓe, a karon farko da ya sa musu baki a magana ya ce “Hmm, Allah dai ya kyauta Hajiya, abotakar yanzu ai ba kowa ke sa Allah a ciki ba”, a ranshi kuma ya ƙarasa faɗin “Wannan kuma ya rage naku”, don yana da yaƙinin ƙarshen alaƙar Umman Deena da Aunty Hafsat ba zata yi kyau ba. 

 Zaƙal Aunty Hafsat ta yi “Kai dai bari Malam Garba, Allah dai ya kyauta”, kusan a tare suka ce “Amiiin ya Allah.”

 Cike da ƙunar rai suka cigaba da tattauna maganar har suka zo ƙofar gidansu Deeni. 

“Oh, yaushe aka sa ma gidan nan gate?”, Aunty Hafsat ta faɗa cikin muryar gulma a lokacin da suka fito mota, idanun Umman Deena na kan milk gate ɗin ta taɓe baki “Au! Dama gidan ba haka yake ba?”, Saboda bata san lokacin da gidan yake da ƙofa ba.

“A’a ƙofa ce a can baya”, Aunty Hafsat ta bata amsa, cikin gidan suka shiga suna ta ƴar gulmarsu ƙasa-ƙasa, sai da suka sa ƙafarsu a tsakar gidan ne suka yi shiru bayan sun yi sallama.

Yaran dake tsakar gidan ne suka amsa musu, Asma’u ma daga kitchen ta jiyo kamar an yi sallama, fitowa ta yi domin tabbatarwa “Laa Mommy! Sannun ku da zuwa”, Cike da fara’a Umman Deena ta amsa “Yauwa Asma’u”, gaishe da su ta yi, kana ta yi musu iso a ɗakin Hajiyarsu.

“Hajja ga su Mommy”, Asma’u ta faɗa lokacin da ta sa kai a ɗakin dake cike da su Yaya Asiya da wasu ƴan’uwan Hajiyar.

Sannu da zuwa suka yi musu, Cikin girmamawa su Umman Deena suka duƙa har ƙasa tare da gaishe da Hajiyarsu Deeni, dan kuwa ba wadda bata haifa a cikinsu ba, ran Hajiyarsu Deeni sal ta amsa musu, sannan suka zauna a kan kujera.

Kaf ƴan’uwan Deeni ba mai son Umman Deena, saboda ƙiyayyar da ta nuna ma ɗan’uwansu lokacin da yake neman auren Deena, haka itama idan akwai ahalin da ta tsana toh su ne, don gani take su suka raba ta da ƴarta, saboda sai da Deena ta haƙura da komai na jin daɗi duk don ta auri Deeni.

 Gaisuwar ba yabo ba fallasa suka yi ma juna, musamman Yaya Asiya da ke jin ba a fi su tsumma ba, don haka ba wanda ya isa ya goga musu kwarkwata.

Umman Deena dama da gadararta ta shigo gidan, don haka da su da babu duk ɗaya, wurin Hajiyarsu ta zo, don haka ta maida dukkan hankalinta gare ta, cikin ladabi ta shiga jajanta mata da faɗin “Ya kuma aka ji da wannan ƙaddara da ta samu Deeni?”, Hajiyarsu ta ce “Sai godiya Hajiya Hadiza”, Umman Deena ta ce “Allah ya ba shi lafiya”, Aunty Hafsat ma jajanta mata ta yi, daga nan suka dasa da tattauna yanayin rayuwa kamar babu komai a ran kowa.

Yaya Asiya kuwa ba’a yi wannan tattaunawa da ita ba, kanta a ɗage ta fito daga ɗakin, kitchen ta nufa tana ta ƴan waƙenta masu ɗauke da habaici.

Duk sun lura da yanayinta, amma sai kowa ya basar, suka cigaba da hira, basu suka tashi ba sai da Driver ya fara kiran Umman Deena.

Yaya Asiya na ganin sun fito ta ƙara haɗe fuska “Har kun fito”, Umman Deena ta ce “Aikuwa dai”, Kusan a tare suka yi musu Allah ya kiyaye, Asma’u kuwa tunda Maman ƙawarta ce har waje ta raka su.

Bayan fitarsu ne matar ƙanen Hajiyarsu ta ce ma Yaya Asiya lokacin da suka koma ɗakin “Kai waccan matar na ji da gadara”, bakin Yaya Asiya a taɓe ta ce “Matsalar ta ce ai, kuma in dai gadara ce gida ta zo.”

Hajiyarsu ta san dole ƴaƴanta su zagi Umman Deena, ita kuma saboda Deenar bata son abin da suke, dakatar da su ta yi da faɗin “Asiya bana son tsurfa, don haka ku iya bakinku”, shiru suka yi, duk da kowa bakinsa cike da magana.

A mota kuwa Aunty Hafsat ce ta kawo gulmar su Yaya Asiya, ai kuwa kamar jira Umman Deena take ta ce “A banza wai talaka ya girmi sarki! Rabu da ƴan iska, na rantse sai na yi maganin su, don kuwa ko da bala’i sai Deena ta rabu da Deeni.”

Sabon shafin zagin dangin Deeni suka buɗe har suka isa gida. A ƙayataccen falon Umman Deena suka yada zango. Ɗaya bayan ɗaya ƴan aikin gidan suka zo yi mata sannu da zuwa, har mai yi mata girki ta juya zuwa kitchen ta dakatar da ita “Karime”, cikin ladabi ta zo tare da ɗan russunawa “Hajiya ga ni”, tambayarta ta yi “Me ake dafawa gidan ne Karime?”, Cikin ladabi Karime ta ce “Shinkafa ce da miya Hajiya”, Umman Deena ta ce “Da kuma me?”, Ta ce “Ita kenan Hajiya, sai kuma pepper soup”, kai ta jinjina “Okay, Gobe Alhaji zai dawo shi ma, so nake tun yau a fara shirin tarbar sa da girki mai kyau.”

Cike da jin daɗi Karime ta ce “An gama Hajiya, ai mun ɗauka tare zaku dawo”, kai Umman Deena ta girgiza “Bai gama uzurinsa bane shi ya sa, ni kuma gobe Monday nake komawa aiki.”, ƴar magana suka yi, sannan Karime ta nufi kitchen.

Sai da Aunty Hafsat ta tabbatar da Karime ta shige kitchen sannan ta buɗe bakin gulma, cike da mamaki ta ce ma Umman Deena “Ina ruwan ƴar aiki da dawowar Alhaji? Wallahi kina sake ma maids ɗinki da yawa”, dariya Umman Deena ta yi “Ke ba wani abu fa, kin fa san mu da ƴan aikinmu akwai fahimta mai kyau, don Alhaji ma nan yake haɗe mu da su a sha hira”, bakin Aunty Hafsat a buɗe ta ce “Taɓ, bakwa gudun raini ko ɗan hali?”, Kai Umman Deena ta girgiza “Inaa! Ai ba wannan maganar, kowa ya san matsayinsa ai.”

Dawowar Karime da abinci ne ya tsaida hirar, ta nufi dining area kenan Umman Deena ta tsaida ta “Karime mun ci abinci fa, ko da yake..”, juyawa ta yi wurin Aunty Hafsat “Madam ko zaki ci a kawo maki nan?”, Kai Aunty Hafsat ta girgiza “A’a dai, pepper soup ɗin dai zan bani in tafi da shi.”

Komawa Karime ta yi da warmers ɗin kitchen, wuri na musamman ta samu ta zubo ma Aunty Hafsat pepper soup ɗin mai yawa ta kawo mata, godiya ta yi mata bayan ta karɓa.

Ƴar hirar su ta ƙawaye suka ɗan taɓa, daga bisani Aunty Hafsah ta yi shirin tafiya, har compound Umman Deena ta rako ta, aikuwa tana ganin Driver ta ce “Malam Garba ko zaka kai ni gida ne?”, cike da jin haushin ta ya ce “Toh Hajiya, amma ina kika baro motarki?”, amsa ta ba shi da “Tana gida ban fito da ita ba.”

Zai fara kawo mata uzurin ƙin zuwa ne Umman Deena ta sa baki, ba don ransa ya so ba ya gyara mota, bayan shigar ta ne Umman Deena ta ce “Sai yaushe?”, Ta ce “Sai an kwana biyu kuma”, bankwana suka ƙara yi, sannan Driver ya ja mota, Mai gadi ya buɗe musu gate suka fita.

Kai tsaye upstairs Umman Deena ta nufa gami da shigewa bedroom, jakarta da mayafi gami da phone ta zube akan gado, sannan ta shiga ban ɗaki ta yi alwalar sallar la’asar, bata wani ɓata lokaci ba tana fitowa ta gabatar da sallar, tana gamawa daga inda take zaune kan carpet ta jawo wayarta da ke kan gado.

Danna wayar ta ke, amma gabaɗaya hankalinta na wurin Deena, a fili ta ce “Oh ni Hadizatu! Wace irin ƙaddara ce wannan ke bin Deena, farko ta auri mijin da bana so, yanzu kuma ga shi ya makance, anya zaman kuwa zai yiyu?”, Kafin ta samu amsar tambayar da ta yi ma kanta ne vedio call ya shigo wayar. “Yallaɓai” ne ya kira, ko kuma in ce mijinta ne, wanda ta aura tun bayan rasuwar Baban Deena.

Ɗan gyara hijabin jikinta ta yi kafin ta ɗaga kiran, da sallama suka yi ma juna kallon mai cike da tsantsar so da ƙauna, bayan ya amsa ne suka gaisa, daga nan ta tambaye shi shirin dawowa, cewa ya yi “Sai jibi ranki ya daɗe, ko kin fara missing ne?” Cikin kissa ta ce “Ai tun ranar da na dawo nake missing mijina”, daga can ya ce “Koh?”, Cikin salo ta ɗan rausaya kai “Yeah, don Allah kada ka wuce jibin, gidan sam ba daɗi”, ya ce “Insha Allah.”

Batun Deeni ya yi mata, saboda ya lura da jikinta ya yi sanyi sosai.

Sai da ta sauke ajiyar zuciya kana ta ce “Ƴallaɓai abin ba daɗi fa, ba Deeni da ciwon ke a jikinsa ba, hatta ita kanta Deena duk ta fita hayyancinta.”

Cike da damuwa ya ce “Subhanallah, Allah ya ba shi lafaiya, Insha Allahu idan na dawo sai mu je a ga irin taimakon da za a iya musu”, Umman Deena ta san magana ce ta ya ba Deeni kuɗi, ita kuma ba wannan ne a gabanta ba, ɗiyarta kawai take so, ranta ba daɗi ta ce “Ni dai kawai ya sako mani ƴata Alhaji, baka ga yadda Deena ta fige ta lalace ba”, yadda ta ƙarashe maganar cikin fushi ne ya sa shi sassauta murya.

“Toh shikenan Madam, ki bar maganar sai na dawo”, bata yi gardama ba ta ce “Allah ya dawo da ku lafiya”, ya ce “Amiiin Tamaigari.”, hirar su suka sha ta miji da mata, daga bisani suka yi sallama..

Asalin Umman Deena bafulatanar Yola ce gaba da bayanta.Ta haɗu da Baban Deena ne a lokacin da aikin soja ya kawo shi Yolar har suka yi aure, sun kuma dawo Kaduna ne duk a dalilin aikin sojan da ke ta relocating ɗinsa. Deena kaɗai ce ƴar da suka haifa, sai kuma Allah ya yi masa rasuwa sakamakon ƴan boko haram da suka harbe shi a wani zuwa da suka yi Maiduguri. Karatun da Umman Deena take yi ne ya hana ta komawa Yola, daga nan ne kuma ta auri shahararren ɗan kasuwa mai suna Alhaji Lawan, shi ɗin babban mutum ne, yana da manyan ƴaƴa sosai, sai dai tsananin kishin matansa da suke da shi ne ya sa Umman Deena ta hana Deena shiga cikin ƴaƴansa, asali ma tamkar a wurinta babu su, tunda kowace da gidanta.

Sosai Alhaji Lawan ya ɗauki Deena tamkar ƴar cikinsa, duk abin da take so shi yake yi mata, mafarin da ta ce Deeni ta zaɓa ya yi mata tsayuwar daka har ta aure shi, shi ya sa Deena ke ƙaunar shi, kuma bata ɓoye mashi damuwarta ko kaɗan, asalima ya riga Ummanta sanin halin da Deeni yake ciki, kawai pretending yake mata. 

Yana son Umman Deena sosai, duk da bai taɓa haihuwa da ita ba, amma kissa da iya kula da miji ya sa yake ganin ƙimarta fiye da sauran matansa, mafarin suka tsane ta kenan…

★★★★

Dr. Deeni kuwa ya koma asibitin, don kuwa babu wani chanjin da ya samu. A kan wani maganin aka sake ɗaura shi tare da tabbacin idan shi ma bai karɓu ba za a yi mashi aiki a idanun. Shi a nashi ɓangaren ko aikin ma baya so, kawai ya ɗaukar ma ransa ɗaukar wannan ƙaddarar har zuwa lokacin da Allah ya nufa.

Zaune suke a bedroom shi da Deena a kan sofa, sakamakon gajiyar da suka yi saboda daga asibitin Lalu wucewa ya yi da su can gidansu, kasantuwar itama Deena ta je awon ciki.

“Deena, ni fa na yanke ƙauna da warkewa daga ciwon nan, kawai na ɗaukar ma raina ɗaukar wannan ƙaddarar”, ransa ba daɗin gaske ya faɗi wannan maganar.

Na daga cikin wayon Deena idan ta ga ya karaya, ita kuma sai ta danne rauninta ta shiga ƙarfafa mashi guiwa, cewa ta yi “Kada ka cire tsammani daga rahamar Ubangiji, kawai ka bari a yi aikin, tunda ka ga hospital ɗinku sun goyi bayan hakan, idan ka samu sauƙi haka muke fata, idan kuma ba a samu ba bama baƙinciki, sai mu yi fatan Allah ya sa muci jarabawa Amiiin”, ya ji daɗin ƙwarin guiwar da ta ba shi, godiya ya yi mata, sannan suka yi shirin bacci.

Har sun kwanta wayar Deena ta fara ruri, tana dubawa ta ga “Daddy”, da hanzari ta ɗaga kiran da sallama haɗe da gaisuwa, bayan ya amsa ne ya ce “Ƴar gidan Daddy ina mijin naki?”, Cike da kunya ta ce “Gashi nan”, daga can ya ce “Toh ba shi”, miƙa ma Deeni ta yi, bayan sun gaisa ne ya ce ma Deeni gobe zasu shigo, Deeni ya ji daɗin haka, godiya ya yi mashi, sannan suka yi sallama.

Deeni yana jin daɗin yadda manyan mutane ke ta sintirin ganin sa, kuma kowanne da irin taimako da ƙwarin guiwar yake bashi na samun lafiya. Haƙiƙa ya san wannan daga Allah ne, godiya ya yi gare shi, tare da fatan dacewa a wurin Ubangiji.

Washegari da yamma Alhaji Lawan da Umman Deena suka zo, shi ɗin mutumin kirki ne sosai, ba ƙaramin tausayin su ya ji ba, cike da albishir da kuma son kwantar ma Deena da hankali ya ce ma Deeni “Insha Allahu ta ɓangaremu ma zamu yi duk abin da zamu iya don ganin ka samu lafiya”, cike da ladabi Deeni ya yi masa godiya.

Umman Deena kuwa hankalinta na wurin ramewar Deena, kasa ɓoye damuwarta ta yi ta ce “Wai baki da lafiya ne, kullum kamar ana miya da ke.?”

Deeni bai ji daɗin maganar ba, tarbar numfashinta ya yi “Wallahi bata son cin abinci Mommy, kusan kullum sai mun yi faɗa da ita akan hakan?”, Kamar Deena zata yi kuka ta dubi Ummanta da ta ke mata wani kallo “Na rantse Mommy ina cin abinci”, hararar ta watsa mata “Zai miki ƙarya ne? Ki zauna nan yunwa da wahala su kashe ki a banza.”

Shiru duk suka yi, saboda maganar kamar da biyu take yin ta. Alhaji Lawan ne ya shiga maganar ta hanyar yi ma Deena nasiha a kan ta cire damuwa a ranta, ita kuwa abu ne mai wahalar gaske ta iya cire wannan damuwa, saboda ta ga ƴan take-taken Ummanta so take ta ɓullo da hanyar da zata raba ta da mijinta.

Dubu Hamsin Alhaji Lawan ya ba ma Deeni, Deena kuma ya bata tsarabar ta Dubai da ya je last two weeks. Jallabiya ce da turaruka masu ƙamshin gaske.

Shirin tafiya suka yi, Deena na rako su Daddy ya dafa kafaɗarta “Daughter bana son damuwar nan kin ji, komai ya yi zafi maganinsa Allah”, kai kawai Deena ta jinjina, don idan ta buɗe baki kuka ne zai fito.

Ummanta kuwa cewa ta yi “Ai ta ce ta ji ta gani, gashi nan ta ɓige da zama ƴar jagora.”

Mahaifiyarta ce, don haka har a ranta bata da martanin da zata maido mata, bare kuma a fili, duk da maganar ta sokar mata zuciya.

Hannu ta ɗaga musu lokacin da Ummanta ta ja motar, kasantuwar ita ke driving ɗin duk saboda ƙauna. Sai da suka tafi sannan ta koma ciki, inda ta taras da Deeni ya tashi har ya kusa shigewa bedroom, tsaida shi ta yi “Yaya, bari na ƙaraso”, tsayawa ya yi kamar yadda ta buƙata, ƙarasowarta ne ta ce “Dan Allah ka riƙa bari na zo”, hannunsa ta kama suka tafi, cewa ya yi “Deena bana son kina wahala, kin ga aiki ya maki yawa”, sakar mashi hannu ta yi tare da rungume shi lokacin da suka ƙarasa tsakiyar bedroom ɗin, cikin kukan da ya maƙale mata a rai ta ce “Har akwai wahala cikin yi ma miji hidima? Yaya indai kana gidan nan ni ce ƴar jagorarka, zan maka hidima da da dukkan karfina”, wani irin tausayin junansu ne ya kama su, sosai Deeni ya riƙe ta ƙyam, cikin kukan da ya ƙwace mashi ne ya ce “Ina sonki Deena, Allah kuma yana so na ne, shi ya sa ya haɗani da ke don ki share mani hawayena.”

Tamkar zasu haɗe juna suka kasance, lokaci ɗaya kuma suna kukan da ba’a san wa zai lallashi wani ba…

<< Mutuwar Tsaye 6Mutuwar Tsaye 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×