Skip to content
Part 8 of 36 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Ta ɓangaren Alhaji Lawan kuwa sam baya jin daɗin abin da Umman Deena take yi mata, kawai yana dannewa ne saboda lokuta da yawa tana nuna mishi ta fi shi power da ita, amma ba don haka ba, da sai ya nuna mata illar kuskuren da take tafkawa ko da ta ƙarfin tsiya ne duk da ba shi ya haife ta ba, idan kuwa da shi ya haifi Deena, toh ko kusa ba zata fara ba, don babu mai yi masa karantsaye a harkar ƴaƴa, baya tauye haƙƙin duk wani mai haƙƙi a kan ƴaƴansa, sannan baya zuba idanu suma ƴaƴan ana tauye musu haƙƙinsu. 

Duk da wannan ƙalubalen da ya sani, amma ya ɗaukar ma ransa yi ma tufkar hanci, don idan ya yi sanyin jiki har auren Deena ya samu matsala, toh damuwar sai ta shafi har wanda bai ji bai gani ba.

Ko kusa bai nuna mata yana da muhimmiyar magana da ita ba sai da suka yi shirin bacci a ƙayataccen bedroom ɗinsa. Zaune yake a kan sofa, ita kuma tana zaune a gefen gado suna fuskantar juna. 

Da irin salon da ta fi so ya ambaci sunanta “Hadizatu”, cikin kissa ta amsa “Na’am Yallaɓai”, saboda shi da ta fi ƙauna ne ya sanya mata sunan, kuma duk lokacin da ya ambace ta da shi wani shauƙi na musamman ne ke taso mata. 

Ko da ya ga kaf attention ɗinta ya dawo a kansa ne ya ce “Muhimmiyar magana nake son yi dake”, ɗan nazarin ko wani abu ya faru ta yi, kafin daga bisani ta ɗan rausaya kai “Toh Alhaji, ina sauraron ka”, shi ma shiru na wuccin gadi ya yi, a ransa yana fatan Allah ya sa ta fahimce shi. Duban ta yi one on one, sannan ya cigaba da faɗin “A kan batun Deena ne nake son mu yi magana, me ya sa kullum kike son saka ta a damuwa?”

Cikin rashin fahimtar tuhumar da yake yi mata ta jefo mishi tambaya itama “Kamar ya nake saka Deena a damuwa?”, Amsa ya bata da “Ta hanyar datsa mata duk maganar da ta fito a bakinki mana, halan ke ba kya ganin illar hakan?” 

Idan a kan Deena ne, toh sam bata yarda tana laifi ba, idan kuwa har an haska mata, toh gadara ba zata bari ta ɗauki laifin ba, mafarin yanzu ta ɗan jinjina kai tare da sakin gajeren murmushin takaici, “Toh Alhaji! Amma wacece Deena don ubanta da ba za’a faɗa mata magana ba? Tunda har ta zaɓi ra’ayinta fiye da ra’ayin uwar da ta haife ta.”

Ganin ta harzuƙa ne sai ya sassauta murya ya ce “Deena ba kowa bace faace ƴarki, don haka kina da ƴancin da zaki faɗa mata son ranki, kuma ba za a yi komai ba, tunda ita ƴa ce mai biyayya.”

Tarbar numfashinsa ta yi “Toh an san da haka kuma za a tuhemi ni?” Cike da ƙwarin guiwa ya ɗaga kai “Ƙwarai, kawai abin da kike shirin yi ne bai kamata ba, ki bar yarinya ta ji da abin da aka jarabce su da shi mana, ba wai ki riƙa sa mata fargabar da ke ƙara mata damuwa ba.”

Ta fahimci inda ya dosa, don haka ta ce “Alhaji, in dai akan zama da Deeni ne na rantse Deena ba zata zauna lafiya ba har sai ta bar gidanshi, kuma yanzu ai ga alhakina nan ya kama ta, sai da na nuna bana son auren amma ta tubure, yanzu ga ta nan tana fama da makaho a cikin gida.” 

Wani irin mamaki ne ya kama shi, duk da ya san halin matarsa sarai, tambayar da ta zo ransa ne ya yi mata “Au! Dama alhakinki ne kenan ya kama ta?”, kai ta ɗaga “Eh”, cewa ya yi “Ba wannan maganar, mutane nawa ne ƙaddara marar daɗi ke samun su, ba tare da sun taɓa ɗaukar alhakin kowa ba? Allah ne ya ɗaura ma Deena da mijinta, ba wai alhakinki da kike iƙrarin na a kansu ba.”

Ɗan saurarwa ya yi ko zata yi magana, jin bata ce komai ba ne ya cigaba da faɗin “Kuma ko da bai makance ba ai kin daɗe kina son raba su, to meye hujjar ki na son raba yarinya da mijinta?” Ita kanta bata da wata ƙwaƙƙwarar hujja, cikin feleƙe da gadara ta ce “Kawai auren ne bana so”, ya ce “Koh?”, Ta ce “Eh”, ya ce “Kamar fa ni da ke ne ace za a raba mu, ya zaki ji.?”

A yadda take mutuwar son Alhaji Lawan to ƙila mutuwa ce kaɗai zata raba su ta iya ɗauka, basar da maganar ta yi “Alhaji ban san me ya sa kake son ɓata mani zance ba.”

Kamo hannunta ya yi, saboda ya ga karayar da zuciyarta ta yi “Saurare ni ki ji Hadiza”, kamar yadda ya buƙata kuwa ta saurara.

Nasiha mai ratsa zuciya ya shiga yi mata, inda ya nuna mata illar ganagnacin da take shirin yi, don kuwa idan ta kashe ma Deena aure ba tare da hujjar da addini ya ke goyon baya ba toh nadama ce zata biyo baya. Sannan ya nuna mata aure ɗan ra’ayi ne, tunda Deena ta ji ta gani Deeni take so, toh a barta da shi, duk yanayin da ya samu kansa a ciki ba zai yi mata illah ba, tunda ita ta ce ta ji ta gani.

Idan kuwa a ka ce da tsiya sai ta rabu da shi, toh duk ƙuncin da ta samu kanta har ta jefa wani a ciki kada a zarge ta, don ba za ta iya samar ma kanta farinciki ba, bare har ta samar ma wani, don haka a bi komai a sannu, sannan a cigaba da addu’a.

Idan Alhaji Lawan na irin wannan nasihar bata cika yi masa gardama ba, don haka sai da ya gama sannan ta ce “Shikenan Alhaji, Allah ya ba kowa mafita ta Alkhairi Amiin”, ya ji daɗin sanyin jikinta, duk da ba shi ke nuna ta ji maganarsa ba.

Ƙawa ita ce babbar matsalar Umman Deena, domin ita ce masarrafin tunani da kuma ra’ayinta, shi ya sa kullum Aunty Hafsat ke yi mata ingiza mai kantu ruwa ba tare da ta sani ba, shi ya sa idan ta yi wani abin mamakin sai dai a raka ta da idanu.

Ko da bata furta ta ji nasihar mijinta ba, amma alamu sun nuna maganar ta ratsa ta, mafarin suna haɗuwa da Aunty Hafsat a wurin aiki ta bata labarin yadda suka yi da shi, buɗan bakin Aunty Hafsat sai cewa ta yi “Ke rabu da Alhaji Lawan, ƴaƴansa mata na can suna auren hamshaƙan masu kuɗi, shi ne ke zai ce ki bar ƴarki inda wahala zata kashe ta.”

Sosai wannan magana ta yi tasirin gaske a ran Umman Deena, don kuwa ƴaƴan Alhaji Lawan uku da ke ma’auri ba wadda mijinta ba merchant ba, daga wadda take Dubai, sai wadda ke Abuja da kuma wadda ke Lagos, wannan kishin ne ya harzuƙa ta har ta ɗaukar ma ranta sai ta kashe auren Deena, ta yadda itama za ta auri mai kuɗi tunda ba inda ƴarta ke da makusa, asali ma kyawunta na daban ne, don kuwa zaka yi zaton Deena ƴar Ethiopia ce, tunda mamanta bafulatana ce, babanta kuma kyakkyawan bahaushen Katsina ne.  

Deena kuwa jikinta ya daɗe da bata mahaifiyarta na can tana shirin raba ta da mijinta. Sannan ta fahimci raunin da ya mamaye Deeni na tsoron rasa ta, mafarin ta ɗaukar ma ranta sanya mashi nutsuwa a rai, domin ta lura da kauce ma sanya ta wasu ayyuka da yake, yana yin hakan ne don ya dogara da kansa ba sai ya dogara da wani ba. 

 Ita kuwa tamkar ɗan cikinta ta maida shi wurin kula da shi, ankare take da duk wani motsi nasa, duk da itama tana bukatar a kula da ita saboda cikinta ya shiga wata takwas. Sosai Deeni ke jin daɗin jajircewarta, kuma shi ma yana iya ƙoƙarinsa wurin kulawa da ita itama,  

Kamar kullum idan mai aikinsu ta gama aikinta take tafiya, da yamma shi kuma sai ya fito falo shi da Deena, kasantuwar sanyi ya yi sauƙi sosai.

Zaune suke a kan two seater suna hira, Deena da ke zaune a kan cinyarsa ne ta shafi fuskarsa”Wannan fuskar tana bukatar gyara”, hannunsa ya ɗaura akan nata ya shafi fuskar shi ma.

“Gaskiya ne Madam, ya za a yi yanzu?”, ya faɗa yana murmushi, don kuwa fuskar ta yi wani irin gashi, amsa ta ba shi da “Aski zamu je ayi maka”, domin samun farincikinta ya ce “An gama Madam.”

A ranar ne da daddare Lalu ya zo da nufin kai Deeni aski, da mamaki sai ya ga Deena cikin hijabi kamar mai shirin fita, tambayar ta ya yi “Dee-dee ina zaki je?”, Deeni da hannunsa ke cikin na Deena ne ya ce “Tare zamu je ai.”

Lalu ya san halin Deena da kafiya idan tana son abu, mafarin mijinta ma bai hana ta ba, bare shi ƙanen miji, bai yi musu gardama ba ya ce “Okay, toh muje.”

Fita suka yi Lalu ya sa ma gidan Key, a wurin shiga mota ne ya buɗe ma Deeni gaba “Yaya shiga”, faɗarsa ta yi daidai da yunkurin taimaka ma Deeni ya shiga motar, aikuwa Deena ta turo baki “Ni kaɗai zan zauna a baya kenan”, zuciyar Lalu iya wuya ya ce “Ke Dee-dee, kin cika rigima wlh, Yaya koma baya wurinta kawai.”

Shi ma Deeni ya fi son bayan saboda ita, bakinsa ɗauke da dariya ya zauna bayan da taimakon Lalu, tana shiga ta saƙalo hannunta cikin na Deeni tare da lahewa a jikinsa, wanda dama don hakan ta ke so ya zauna baya. 

Wurin askin suka fara zuwa, inda ta zauna a cikin mota har aka gana ma Deeni askin sannan suka dawo. Daga nan Super market suka nufa don yin ƴan saye-sayen kayan masarufi. Sosai ta ɓadda mutane wurin gane mijinta baya gani, domin kuwa da specs a fuskarsa, sannan hannunsu cikin na juna suka shiga, ta yadda duk wanda ya gani zai yi tsammanin soyayya ce kawai. 

Deeni kuwa tamkar ɗakinsa haka yake kallon cikin super market ɗin a zuciyarsa, saboda wurin zuwansu ne duk ƙarshen kowane wata, shi ya sa kai tsaye yake saka ƙafarsa duk inda Deena da Lalu suka saka tasu.

 Bayan sun gama siyayyar sun zo biyan kuɗi ne wata mata da ta san Deeni a asibiti ta ce ma mijinta “Laa! Ji Dr. Deeni.”

Yadda ta yi maganar cikin farinciki ne ya ɗauki hankalin mutanen wurin, Deeni kuwa bai so haka ba, duk da bai ga yadda idanun mutane suka mamaye shi ba. Deena da Lalu kuwa fuskarsu ba yabo ba fallasa suke amsa gaisuwar mutane, don majority na mutanen wurin sun san Deeni by name, amma ba su san shi by face ba.

Matar da mijinta kuwa har bakin mota suka rako su, inda mijinta ke yi ma Deeni complain ta koma asibiti kan lalurar da Deeni ne ya fara duba ta, amma Dr. Bello sai karɓar musu kuɗi yake, kuma ba wani ingantaccen magani.

Deeni ya san fiye da haka na faruwa a asibitin, ransa ba daɗi ya ce “Allah ya kyauta, idan ba damuwa bari na ji ta bakinta, sai na sake rubuta mata wasu magungunan.” 

Lalu ne ya miƙo masa Jotter da pen a cikin motar, sannan shi da Deena suka ɗan zagaya saboda tambayoyin na buƙatar privacy.

Matar na kallon mijinta ta matso kusa da Deeni don jin me ke damunta, cikin ranta kuma tana mamakin yadda zai yi rubutu alhalin baya gani.

 Tambayar ta Deeni ya yi “Me ke damun ki?”, Aikuwa ta shiga zayyana ma Deeni dukkan matsalolinta na mata, shi kuwa tamkar a office ɗinsa yake, a tsare ya rubuta mata magunguna masu kyawun gaske, sannan ya basu shawarwarin da zasu kula da lafiyarsu a kan tsari.

Sun ji daɗi sosai, matar kamar zata yi kukan daɗi ta ce “Mun gode Dr. Allah ya baka lafiya”, Hannun Deeni cikin na mijin ya ce “Amiiin ya Allah, Nagode sosai”, mijin matar ya ce “Ai mu ne da godiya Dr.”

Basu bar wurin ba sai da suka yi exchanging numbers, matar ta karɓi ta Deena, shi kuma mijin ya karɓi ta Deeni.

Da tunanin aika-aikar da su Dr Bello ke yi Deeni ya koma gida, shi ɗin ba ma’abocin gulma ba ne, amma da suka zo bacci sai da ya ce ma Deena “Ban san yaushe Bello zai zama na gari ba, mutane na ta complain a kansa”, baki Deena ta taɓe kafin ta ce “Hmm, Allah dai ya kyauta, tunda baka nan ai dama zasu yi yadda suke so, Allah dai ya baka lafiya”, cike da kewar aikinsa ya ce “Amiiin Madinatu.”

A can asibitinsu Deeni kuwa, MD sai faɗi ta shi yake wurin ganin Deeni ya dawo a bakin aikinsa, wanda hakan ba zai yiwu ba sai ya samu lafiya. Lokaci bayan lokaci ya kan tara staffs don jin ta bakinsu a kan Deeni, masu zuciya mai kyau shawararsu ita ce a taimaka masa ya samu lafiya, don akwai wanda ya ce “Ko ba idanu Deeni zai iya aiki.”

Wannan magana ta tafi da tunanin MD, cike gamsuwa ya ce “Gaskiya ne, rubutu ba zai gagara ba, kuma ko da ta kama a duba patient na san ba zai gagari Deeni ba.”

Katse masa magana Dr.Bello ya yi ta hanyar faɗin “Ƴallaɓai da wane idanun zai duba marasa lafiya, kawai a rabu da shi ya ji da damuwarsa, kuma menene Deeni yake wanda mu bama yi.?”

 Zaman jin ra’ayin juna ne, don haka MD bai yi tunanin hassada ce ta sa Dr. Bello faɗin haka ba, nazari ya yi sosai tare da jin shawarar kowa, wasu sun bada shawarar Deeni ya dawo aikinsa, wasu kuma sun bada shawarar a barshi ya cigaba da neman magani, tunda yanzu idan ya dawo kafin ya iya sabawa da aikin ba idanu za’a ɗauki lokaci.

Da MD ya gama jin ta bakin kowa ne ya ce “Duk na ji ta bakinku, yanzu ra’ayin Deeni muke bukata, idan ya ji zai iya, toh ya dawo a bakin aikinsa, idan kuma ba zai iya ba, ba dole, sai dai batun taya shi neman lafiya yana nan daram! Ko da kuwa ta kama a fitar da shi waje.”

Dr. Bello kamar zai mutu dan mugun abu, a ransa ya ce “In dai ina raye Deeni ya gama aikinsa a wannan hospital ɗin.”

Da ya san me ke ran Deeni, toh da bai ɗaukar ma ransa wannan mugun ƙudirin ba, don kuwa har gida MD ya iske Deeni ya yi masa complain ɗin taɓarɓarewar komai a hospital ɗinsu, sannan ya roƙe sa da ya dawo a bakin aikinsa kawai.

Deeni ya ji daɗin wannan tayin, amma sai ya ce “Yallaɓai a bari ayi aikin tukunna, tunda next month ne, idan Allah ya sa na warke sai in dawo, idan kuma ban warke ba sai a sake sabon tsari.”

Cike da ƙauna gami da tausayinsa MD ya ce “Insha Allahu ma zaka warke”, Deeni ya ce “Toh Yallaɓai, Allah ya sa”, don kuwa shi gani yake kamar ba zai warke ba, MD ya ce “Amiiin Deeni”, ƴan maganganu suka ƙara, daga bisani MD ya tashi da nufin tafiya, har bakin ƙofa Deeni ya raka shi, sannan dawo ciki duk shi kaɗai, wannan ne ya ƙara ma MD tabbacin Deeni zai iya aiki ko ba idanu..

<< Mutuwar Tsaye 7Mutuwar Tsaye 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×