Zaune Deena take bedroom a ƙasan carpet ta miƙe ƙafafunta da suka ɗan kumbura, tana cikin saƙawa da kwancewa ne ta ga Deeni ya shigo ɗakin, duk da daɗin zaman da take ji bai hana ta yunƙurawa ba zata mike, lokaci ɗaya kuma bakinta na faɗin “Yaya bari in zo dan Allah.”
A yadda Deeni ke kallon ɗakin a zuciyarshi ko ita mai idanu sai haka, zuciyarsa na kallon ta zaune a ƙasa ya dakata “Yi zamanki Madam, zan iya kawo kaina har ƙasan da kike zaune”, mamakin yadda ya san tana zaune a ƙasa ne ya hana ta yi mashi gardama, cewa ta yi “Toh shikenan, amma zan yi guiding ɗinka saboda kada ka yi karo da sofa”, ya san da ita, amma ya ce “Okay, muje toh.”
Yanzu kam ba zai iya tantance farko ko tsakiyar ɗakin yake ba, tambayar ta ya yi “A ina nake yanzu?”, amsa ta ba shi “Ka wuce ƙofar kaɗan, amma ba ka zo tsakiya ba”, kai ya jinjina “Okay”, don ya gane inda yake, cigaba da takowa ya yi, lokaci ɗaya kuma yana laluben hanya, ba don yana gudun kai ma wani abu karo ba, sai dai kawai don ya saba.
Deena kuma wannan abun ɗaga mata hankali yake, don shi ke tabbatar da Deeni baya gani, kamar zata yi kuka ta ce “Ka sauke hannun mana”, da hanzari ya yi yadda ta ce, tafiya kaɗan ya ƙara sai gashi ya zo inda take tare da zama a kan sofa.
Matsawa ta yi kusa da shi tare da jingina bayan ta da sofar, ɗan shiru suka yi, daga bisani Deena ta tambaye shi “MD ɗin ya tafi kenan?”, amsa ya bata “Yes ya tafi, nima ban yi zaton zai tafi da wuri haka ba.”
Kai ta ɗan rausaya alamar “Okay”, lokaci ɗaya kuma ta buɗe baki zata yi magana wayar Deeni da ke gaban aljihunsa ta dakatar da ita. Da hanzari Deeni ya fiddo wayar “Duba ki ga waye ke kira.”
Sunan “Barrister” ta gani na yawo a screen ɗin, Deeni kuma ya gane mijin matar nan ne da suka haɗu a super market.
Da sallama ya amsa kiran, bayan sun gaisa ne daga can Barrister ya ɗaura da faɗin “Dr godiya muka kira mu yi maka, don kuwa cikin ƙasa da mako ɗaya Madam ta samu lafiya sakamakon magunguna masu kyau da ka rubuta mana.”
Ba wannan ne na farko da aka yi ma Deeni godiya ba sakamakon sauƙin da marasa lafiya suke samu a dalilinsa ba da ikon Allah, amma ya ji wannan special, saboda wannan ya tabbatar mashi da bai samu gazawa ga aikinsa ba, idan ma har ya samu, toh ba zata hana shi wasu ayyukan ba.
Cike da jin daɗi Deeni ya ce “Masha Allah, Allah ya ƙara mata lafiya”, daga can Barrister ya ce “Amiiin ya Allah.”
Ɗan shirun da Deeni ya yi ne ya ba shi damar ɗorawa da faɗin “Dr. Na ce me zai hana ka dawo aikinka, sai nake ganin kamar zaka iya cigaba da komai, tunda dama ƙwararre ne”, yana sauka da magana Deeni ya ɗaura da nashi “Toh Barrister, Nagode sosai da shawara, amma aiki a makance ba abu bane mai sauƙi, amma zan yi nazarin idan zan iya, amma sai an yi mani theater tukunna.”
Barrister ya fahimci sanyin jikin Deeni, mafarin ya shiga ƙarfafa ma Deeni guiwa da maganganu masu ƙarfi, inda ya nuna mashi gazawa ba nashi bane, ko don ya ƙuntata ma maƙiyansa da suke son su ga durƙushewarsa.
Ba ƙaramin tasiri maganganun Barrister suka yi ma Deeni ba, musamman batun maƙiyan nan, don ya sani cewar su Dr. Bello na cikin masu son ganin ƙarshensa, kuma da ikon Allah zasu ji kunya, godiya sosai Deeni ya yi mashi, daga bisani suka yi sallama.
Gefensa ya aje wayar tare da yin shiru, cikin ɗan ƙanƙanen lokaci ya shiga tunanin yadda zai iya komawa aiki a haka, sanin abu ne mai wahalar gaske ne ya sauke ajiyar zuciya, don kuwa komai na bukatar tsari.
“Kamar mijin matar nan da muka haɗu a super market ko?” Deena ta katse mashi tunanin da yake shirin lulawa.
Ajiyar zuciya ya sauke “Shi ne, ya ce matar ta ji sauƙi ai”, cike da murna ta ce “Masha Allah, ai mijina perfect ne, ya san kan aikinsa”, ya ji daɗin yabon da ta yi mashi, domin jan maganar ta yi tsawo ne ya ce “Ko?”, Ta ce “Eh, gashi cikin ƴan kwanaki daga ka bata magani da taimakon Allah har ta warke, saɓanin waɗancan da basu iya komai ba sai zalunci.”
Kai ya jinjina, da ƴar dariya a bakinsa ya ce “Allah dai ya kyauta”, ta ce “Amiiin.”
Duk da ya san ta ji maganar da suka yi da Barrister, amma ya ce “Ai kin ji saboda murnar matarsa ta warke wai in koma aiki”, ba tare da ta yi dogon nazari ba ta ce “Allah kuwa, nima na daɗe da wannan tunanin a raina, gani nake tsaf zaka iya”, kai ya gizgiza “A’a Deena, komawata aiki ba abu bane mai sauƙi, duk da MD ma maganar ce ta kawo shi yanzu.”
Karon farko kenan da ta ga yana gudun aikinsa a sanadin makantar, duk da cewar ta san ba da son ransa ba, kamar zata yi kuka ta ce “Haba Yaya! Meye rashin sauƙinsa? Dan Allah ka da ka sare guiwa, ni na san zaka iya.”
Leɓensa ya cije tare da girgiza kai ya ce “Deena, maganar ba ta rashin iyawa bace, challenges ɗin da zan fuskanta ne abin gudun, kin ga farko waye zai yi mani jagora a kullum? Na san ƙila tunaninki zai baki Lalu ko? Toh shi bai da aikin kansa ne?, Kin ga ba dalilin da zan shiga haƙƙinsa.”
“Sannan yanzu digital muke ba analog ba, da system ake aiki, shin zan koma aiki da files ne, ace ni daga office ɗina sai dai a kai files niƙi-niƙi, kin ga ko a wannan kaɗai aka tsaya manyan ƙalubale ne da ya kamata kowa ya yi nazari a kansu kafin a ce in koma aiki.”
Sosai Deena ta fahimce shi, cewa ta yi “Hakane, amma duk da haka kada ka yi saurin sarewa, tunda MD da kansa ya nemi ka koma, na san zai yi maka tsarin da komai zai zo maka cikin sauƙi”, cewa ya yi “Haka ne, na ce mashi ya bari ayi mani aikin tukunna, result ɗin da aka samu ne zai ba ni damar making decision.”
Sun tattauna sosai a kan batun, tun yana kan sofa har ya dawo ƙasa, saboda Deena ta yi nauyin da ba zata iya faɗi da tashi ba.
A cigaba da maganar aikin da za a yi masa ne ta ce “Ai ƙila har ayi maka aikin ban haihu ba”, tambayar ta ya yi “Yaushe ne EDD ɗinki?”, a yadda lissafin ya kama sai ta haihu da mako ɗaya ne za a yi mashi aikin, kai ya ɗan jinjina “Okay, Allah ya sauke ki lafiya” ta ce “Amiiin ya Allah.”
A ɓangaren Dr. Bello kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye, musamman da ya ji MD ya zo wurin Deeni a kan batun dawowarsa aiki. Duk wata hanya da ya ga ta kamata ya bi wurin toshewar kada Deeni ya dawo ya bi, amma sam bai samu nasara ba, don haka sai ya yanke shawarar bin ɗayar hanyar.
Tunda safe matarsa ta ga yana shiri, cike da kulawa ta tambaye shi “Sai ina?”, Amsa ya bata da “Ƙauye zan je”, bata yi mamaki ba tunda ɗan ƙauyen ne, amma duk da haka sai da ta sake tambayar shi “Me ake a ƙauye?”, tambaya ya maido mata “Mutum da ƙauyensu har sai an tambaye shi me zai yi?”, Kai ta girgiza tana dariya “Sannu masu ƙauye, mu da bamu da shi kada a yi mana gori”, cewa ya yi “Eh ƴan birni”, ta ce “Ku kuma ƴan ƙauye”, wani irin kallo ya wurga mata “Au hada zagi?”
Hannunta rufe da baki ta ce “Ayya, sorry”, ƴar zolayar juna suka ƙara yi saboda shi mai sauƙin kai ne ga iyalansa, babbar matsalarsa ita ce hassada da muguntar ga mutann waje, wanda kuma wannan babbar illa ce a gareshi. Sallamar ta ya yi, sannan ya fita
Motarsa ya fidda, inda suka yi mahaɗa da wani abokinsa da suka iya shige-shigen malamai a tare, hanyar ƙauyensu suka nufa, a hanya suka yi ta tattauna batun Deeni da irin mugun shirin da suka tanadar mashi.
“Ai ka san, ko nawa ne zan iya kashewa madamar Deeni zai dauwama a gida”, inji Dr. Bello da ke driving ɗinsu, mutumin ya ce “Ban ga laifinka ba Dr., Ni fa a rayuwata ban yarda wani ya shige mani gaba ba, shi ya sa ka ga na riƙi Malam Sa-su a koma, don cikin ɗan lokaci matsalar zata kau”, Dr. Bello ya ce “Ai Nima Nagode da haɗani da shi da ka yi, don na ga biyan buƙatu da yawa”, haka suka yi ta tattauna batun har suka isa ƙauyen.
Gidan Malamin a farkon gari yake, nan suka faka motarsu a waje suka shiga, sun yi sa’a kuwa ba mutane da yawa. Layi suka bi har aka zo kansu, tare suka shiga wurin mutumin da ke iƙrarin shi Malami ne. Ɗaki ne madaidaici da aka manna fatar mugayen dabbobi a kowane bango, kusurwowin ɗakin kuwa duk layu ne da ƙahunna a manne, ga wanda yake matsoraci ba zai iya zama koda da wani a ciki ba, bare shi kaɗai, don kana ganin ɗakin ka san aljannu na safa da marwa a cikinsa.
A gaban buzun da mutumin yake zaune suka zauna, inda su da shi suka sanya ƙasa a tsakiya.
Gaisawa suka yi, daga nan ya ɗora da faɗin “Har yanzu makaho na damunka ko?”, Kai Dr Bello ya ɗaga “Sosai Malam, yanzu ma..”, bai ƙarasa ba mutumin ya katse shi “Suna so ya dawo a bakin aikinsa, toh hakan ba zai yiwu ba, dan ba zai warke ba ma bare har ya iya taɓuka komai, idan kuma ya ce zai yi, toh zamu ɗaukar maka matakin da za a manta da shi a doron ƙasa.”
Tamkar bushara Dr. Bello ke jin wannan magana, don abin da yake fatan ji kenan, godiya ya yi ma Malamin, shi kuma cike da izza ya ce “Ai ba godiya a tsakanimu.”,
Juyawa ya yi wurin ɗayan da shi kuma a kan matarsa da ya saka ne, “Matarka aure zata yi, kuma zata haihu, sannan mutuwa ce zata raba ta da mijinta, don haka ka je ka saurari Allah kawai.”
Ko kusa bai ji daɗin hakan ba, cewa ya yi “Ba wata mafita?”, Malamin ya ce “Akwai, ita da makaho duk mataki ɗaya za a ɗaukar musu, ba za a bari su zauna lafiya ba..”
Wasu laƙunƙuna da layu ya basu, su kuma suka jibga mashi kuɗaɗe, sannan suka tafi.
Uwa mai daɗi! A lokacin da Dr. Bello ke ƙulla ma Deeni makirci, a lokacin ne ta zage dantse wurin yi ma ɗanta addu’a da kuma halsataccen magani, ta san akwai makircin mutane sosai a cikin halin da Deeni ya samu kansa, don ko ba asiri, toh akwai kambun baka, saboda kusan sunan Deeni ya zagaye ko’ina acikin garinsu, har ma da wasu garuruwan.
Lokuta da dama an sha yi mata tayin Malamai ƴan tsubbu wurin nema ma Deeni magani, amma bata taɓa yadda da batun ba, saboda gudun rasa imani da kuma dukiya, sai dai duk inda ta ji Malaman Islamic tana aikawa, wani lokaci har gida suke iske Deeni saboda karamci, kuma suna ƙoƙarinsu wurin bashi addu’oi masu kyau, shi ya sa ƙullinsu Dr Bello bai hana tauraruwa Deeni haskawa ba, don har gida yanzu iske shi ake akan aikinsa.
★★★
Kwanci tashi kuma a sarar mai rai, har an sanya ranar aikin, amma Deeni ya ce a ɗaga har sai Deena ta haihu saboda EDD ɗinta ya wuce, ita kuma bata so haka ba saboda tana son ta ba mijinta kulawa, wadda idan ta haihu da wahala ta iya ba shi.
Complain ta yi mashi, cike da lallashi ya ce “Kwantar da hankalinki, duk ɗaya ne tunda muna tare”, lallashinta ya yi sosai da maganganu masu sa nutsuwa, aikuwa ta yi lamo a jikinsa tana sauraro.
Tamkar an tsunkuleta ta ji a mararta, zabura ta yi “Wash Allah”, tambayar ta ya yi “Me nene?”, Kamo hannunsa ta yi ta sa a mararta “Tamkar ana tsunkulk na a nan.?”
Cike da damuwa ya ce “Ko Labour ne?”, Haihuwar fari ce, don haka ba zata iya tantancwa ba.
Sannu ya shiga yi mata, kan ka ce me ciwo ya rikice, Mahaifiyarsa ya kira, inda ta turo su Hajiya Umma da Lalu aka nufi asibiti, Mahaifiyarta ma tuni an sanar da ita, kuma bata ɓata lokaci ba ta iske su can.
Sanin kowa ne ba a ga maciji tsakanin Umman Deena da dangin Deeni, don haka kowa ya kama shiyyarsa. Dangin Deeni na murna matar ɗan’uwansu zata haihu, ita kuma tana murna lokacin da zata raba Deeni da Deena ya yi.
Ba’a daɗe ba Deena ta santalo santalelen yaro, murna wurin Deeni kuwa ba a magana, musamman lokacin da aka kawo mashi yaron ya yi masa huɗuba. Tamkar zai maida shi a ciki ya rungume shi, cike da ƙaunar yaron ya yi masa addu’oin neman albarka da kuma kariyar Ubangiji, sannan aka karɓe shi.
Sai da kowa ya gama shige da fice wurin Deena, sannan Deeni ya samu damar keɓancewa da matarsa, gefen gado ya zauna bakinsa na faɗin “Barkanki Madam”, daga kwancen da Deena take ta ɗaura hannunta a kan cinyarsa “Yauwa, Nagode”, yadda ta yi maganar ba ƙarfi ne ya ƙara tabbatar mashi da ta sha wahala, gam ya riƙe hannun “Haihuwa da wahala ko?”, a shagwaɓe ta ce “Na sha wahala sosai, na ɗauka ba zan rayu ba.”
Cikin tausasa murya da lallashi ya ce “Sorry Dee-dee, ai yanzu ya wuce, Allah ya ƙara maki lafiya ke da baby”, ta ce “Amiiin.”
Tambayar ta ya yi “Da wa baby ke kama?”, Sai da Deena ta kalli kyakkyawan yaronta sannan ta ce “Da babansa ya ke kama”, ya ce “Ko?”, ta ɗaga kai “Eh”, ya ce “Kin yi murna da hakan?”, Ta ce “Eh, Nagode ma Allah da ya yi mani kyautar ɗaa da babansa iri ɗaya, ina addu’ar Allah ya tsare mani su daga dukkan sharri”, cikin wata sabuwar ƙaunarta da ta mamaye shi ya ce “Amiiin My Golden Deena.”
So yake ya raɓi jikinta, sai dai yana gudun ƴan shige da fice su banko ƙofar, itama hakan take a wurinta, don haka ne ta taƙarƙara zata tashi, dakatar da ita ya yi, sannan ya raɓa gefenta ya kwanta suna fuskantar juna, cikin raɗa ya ce “Ina son ki Deena, Allah ya yi maki albarka, ya barmu tare.”
Cewa ta yi “Amiiin ya Allah”, shiru suka yi lokacin da wata nutsuwa ke ratsa su, take Deena ta manta duk wata azaba da ta sha, cikin ɗan lokaci bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita, Deeni na jin saukar numfashinta ya zare jikinsa, da lulube ya juya ta suna fuskantar juna ita da baby.
Gefen gadon ya dawo da zama, a ransa yana tunanin kewarta da zai yi, tunda gida zata koma wanka. Haƙiƙa yana son Deena, son da bai ƙi ba ace kullum suna maƙale da juna, “Allah ka bar mani matata a kusa da ni”, ya faɗa a fili, tunda daga Allah sai shi, sai kuma Deena da baby a ɗakin.
Da yamma liƙis aka sallami Deena, kuma tun a ranar dangi na kusa da na nesa suka fara zuwa. Washegari da Aunty Hafsat ta zo ne take tambayar Deena “Yaushe ne za a yi ma Deeni aikin?”, Deena ta ce “Sai next week”, buɗan bakin Aunty Hafsat sai cewa ta yi “Ashe baki nan za a yi”, da mamaki Deena ta ce “Ina zan je Aunty Hafsat?”, Aunty Hafsat ta ce “Gida mana, ko ba zaki je wanka ba…?”