Skip to content
Part 13 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

Sallamar Abid ta katsemin tunanin da nake yi sai da na amsa masa ya shigo daga cik gefena ya zauna ya miqomin wayar dake hannunsa

“Yaya Sumayyah ki amsa waya Yaya ya bani qawarki na kiranki.”

Ban tsammanin kiran kowa ba bayan Halima Kuma itace dai qawar tawa da Yaya Samir ke da number ‘dinta hakanan kuma naji gabana yana fa’duwa haka dai na daure na anshi wayar,wayar Yaya Samir babu password hakan yasa na kar’ba na danno number ‘din Halima na bi kiranta.

Sallama nayi mata bayan ta ‘daga jin bata amsamin ba yasa na cire wayar a kunnena na duba wayar ba wai an katse ba ne haka nayi tunanin ko ba service haka dai na sake maida wayar kunnena na sakeyin wata sallamar kukan Halima naji da shashshekarta tuni na ru’de gabana ya cigaba da fa’duwa na daure na fara tanbayar Haliman.

“Halima lafiya maike damunki,ba zakimin magana ba sai kuka mai yafaru dan Allah ki sanarmin kar nima ki sani kuka.”

Da wannan lallashin da nake yiwa Halima yasa ta yin shiru tana ajiyar zuciya zuwa can ta soma magana.

“Sumayyah qaddara ta riga fata duk qoqarinmu ba xamu guje mata ba,kuma kowanne bawa da irin yadda qaddararsa ke zuwar masa,haka dole kowa yayi haquri da irinta sa,saboda cikar imaninka.”

Shiru nayi Ina sauraren Haliman Kuma bugun zuciyata na tsananta qaruwa na dai daure na ce.

“Halima dogon jawabin nan ya isheni duk nasan da hakan,ki sanar dani abinda ke faruwa dan Allah,hankalina ya kasa kwanciya.”

Halima ta ‘danyi shiru kafin ta ce
“Exam din mu ta qualyfying ta fito sai dai Sumayyah ajinmu mutum goma suka samu ciki…”

Gaba na ya qara fa’duwa na dakarta da Halima idona yana zubar da hawaye masu zafi.

“Babu ni a cikin wa’danda suka ci ko?”
Nayi mata tanbayar saboda Ina da yaqinin haka ne jikina kawai ya bani

Shiru tayi na sake jefa mata tanbaya

“Ban ci ba ko?”

Cikin qinqina ta ce

“Eh..ey”

Bata kuma sake cewa komai ba
Nice ma na sake qoqarin yin magana amma naji tayi shiru alamun ta katse wayar hakan yasa na cire wayar a kunne na na miqawa Abid da hawaye suka cikamin idanuwa na

Abid ya soma magana
“Yaya Sumayyah mai yafaru ne kike kuka”
Hawaye na na goge na ce

“Bakomai Abid”

Kallona yayi ya ce

“A’a da komai fa Yaya Sumayyah ki fa’damin Dan Allah”

Na sake ce masa

“Bakomai Abid,kaje ka kaima Yaya wayarsa”
Ya ce

“To shikenan zan kai masa amma dai zan fa’damasa kuka kike bayan kin gama wayar”
Haka Abid ya tashi ina kallansa sau tari idan na gansa muna wata firar Ina tunawa da Ahmad da yake kusan kamarsa,haka a halayyarsa nakan tuna Ahmad saboda yadda shima Abid ke da kyawun hali sam ba ruwansa da sabgar ‘yan gidansu,shi da Yaya Samir halayyarsu ta banbanta da ‘yan uwansu su akwaisu da tausayi da son zumunci sa’banin sauran kowa halin iyayensa ya biyo,batun qualyfying ‘dinmu ta fa’domin a raina na rasa mai zanyi kuka zanyi ko me da zan ji sauqi a zuciyata kaina na kife a qasan carpet ‘din da nake kai zaune ina wani irin kuka Mai ciwo shikenan karatun da na saka rai zanqarasa bazai samu ba,karo na farko na fa’di jarabawa,shin ta ina iyayena zasu nemo ku’din da za’a biyamin na kammala karatuna na sani babu mu ‘din da neman na yau da kullum muke ta yaya zamu nemo ku’din biyan jarrabawa,dukda Ina da yaqinin a cikin dangin mahaifina akwai wa’danda mutum dubu zasu biyawa jarabawa ba tare da arziqinsu ya girgiza ba amma inada yaqinin banda ni hakan yasa ma ban saka rai ba,yasa kuma na shiga damuwa mai tsananin gaske.

Sallamar da Abid ya sakeyi ta dawo dani daga tunanina ta Kuma tsayarmin da kukan  da nake amsa masa sallamar nayi ya Kuma shigo ya maida kallensa gare ni.

“Yaya Sumayyah kuka kike ko,ina jiyowa tun daga kofar ‘daki ki barwa Allah komai.”

Na _daga masa kai.

Da ga nan ya ce.

“Yaya yana waje yace kije yana compound”daga nan ya fice nima ba nida za’bi illah na saka hijabi nabi bayansa

A tsaye na hangosa fuskarsa babu wata walwala sallama na masa ya amsamin na gaishesa ba yabo ba fallasa ya amsa gaisuwar tawa,wanda bansan dalilin hakan ba yana nunamin kujerun robar da ke kusa dani yana qoqarin jan ‘daya daga ciki ya ce
“Ki zauna ma na”hakan yasa na ja nima na zauna da Bismillah baki na

Kallon da Yaya Samir yake min da na kasa jurewa nayi qasa da kaina

Shirun da ya ratsa tsakaninmu can Yaya Samir naji gyaran muryarsa ya fara magana
“Sumayyah dan Allah kiyi haquri da duk yadda rayuwar zata zo miki na sani hakan babu da’di, naji kamar ina ma nine ke rayuwarki tana bani tausayi dukda na sani jarabtace daga Allah,nasan komai Sumayyah,ni Haliman ta fara yiwa maganar bansan ta Ina zan tunkareki da zancen ba hakan yasa na ce ta sanarda ke da kanta,ko damuwar zatazo da sauqi a gareni, Sumayyah ba ni da sauran nutsuwa duk da nasan kin cancanta na miki komai sai dai yadda zan riqa kyautata miki ba tare da na ‘batawa su Abba rai ba,bansan ta ina zan misalta bo’dadden halayyar Abba da Ummi ba dan Allah kiya haquri Sumayyah ki ‘dauki komai na rayuwarki bisa kaddara kuma komai zai wuce.”

Kai kawai na ‘dagawa Yaya Samir don bansan irin amsar da zan basa ba don zan iya fashewa da kuka ina fara magana,magana shima ya cigaba dayi

“Yanzu ki kwantar da hankalinki,zanyi magana da Abba zan biya miki ku’di ki zana a private idan lokaci ya tashi.”

Ban wani gasgata lamarin ba dan nasan abin Kamar da Kamar wuya shiga islamiyya ma sun hanani bare Kuma biyan ku’din zana exam,hawaye suka cikamin idanuwa na don ina da tabbacin kawai lallashi ne kawai,na dai daure na ce

“Yaya Samir ko ban zana na ba na kar’bi kaddarata,amma Yaya Samir Halima da Batul nake so naji sun samu,hankalina yafi tashi idan na tuna su bansan tasu makomarba”

Yaya Samir ya kalleni

“Ki share hawayenki Dan Allah,sai na fa’damiki komai.”

Ba nida zabi illah na goge hawayen na fara saurarenshi.

“Batul da Halima duk sun samu,Sumayyah kece kawai Allah ya qaddaramiki hakan ba wai dan baki da qoqari ba illah kawai jarrabata ce daga Allah hakan Allah yaso,idan Allah yaso zai jarrabci bawa saiya jarabceshi da abubuwa kala kala bawai dan bai sanshi ba,sai dan yana nufin mutum da wani alkhairi.”

Bana sauraran zancen Yaya Samir sosai na kife kaina jikin gwiwa ta ina kuka da bana jin akwai mutumin da nake buqata a yanzu bare jin muryar wani,a kusa da ni,qaddara ce na sani amma bansan kalar ta wa ba a lokaci qanqani komai ya sauya min,ni ka ‘dai nasan ciwan da na ke ji da ra’da’din da nake ji da babu mai fahimtata.

Bayan wasu kwanaki da na ‘dauki komai a bisa qaddarata na Kuma amshi hakan,walwalata ta soma dawowa saboda yadda kullum nayi waya da Umma a wayar Yaya Samir takan kwantarmin da hankalina

Yau da shirin zuwa aiken Ummi na ta shi,dutsen safe zamu ni da Abid gidan qanwar Ummi Aunty Ramla kasancewar weekend be qarfe goma muka fito bakin titi ni da Abid da nake sanye da doguwar rigar material sai mayafina kalar brown kwalliyar fulawar jikin material ‘din muna tafe muna fira cikin wasa da dariya munyi matuqar sabo da Abid matuqa kamar mun shekara da shekaru tare haka muka tsaida napep muka shige muna fa’damasa unguwar da zai kaimu dutsen safe low-cost,babu laifi munyi ‘yar tafiya,kafin mu isa unguwar har qofar gida aka qarasa damu,muka miqamasa ku’di muka fito ni da ma ban ta’ba zuwa gidan ba Abid ne yake jagorantar tafiyar sai da muka qwanqwasa gate ‘din gidan da mintina kafin zuwa can muka ji alamun tafiya,hakan yasa muka tsaida buga gidan Aunty Ramla din ce ta bu’de kofar da fuskarta ba yabo ba fallasa tayi mana izinin mu shigo ciki bayanta muka bi har zuwa ciki a babban falo muka zauna saman kujera muna gaishe da Aunty Ramla din haka dai ta amsa tana ‘dan shan qamshi har mamakin hakan nayi ganin da Abid na taho ya kamata ace ta ‘dan saki fuska ko danshi dukda bansan halin Aunty Ramla din ba qila hakan take bamu jima sosai gidan ba muka fito Dan yaran Aunty Ramla biyu duk basa nan,suna gidan kakanninsu,bamu samu napep ba anan qofar gidan ganin zamu da’de yasa muka fara tafiya a qasa dukda saqon da muka amso masu nauyi ne amma ba muda za’bi banda muyi kama kama muka riqe hannun ledar nida Abid muka fara tafiya zuwa bakin titin hankalinmu kwance muna fira da Abid yana bani labarin Aunty Ramla Wanda a labarin na fahimci halayyarta ce shariyar data mana,amma dukda hakan har dama wulaqanci na fa’da a raina labaran Aunty Ramlan ya dinga bani na tun kafin tayi aure har zuwa yanzu wani abun har dariya take bani a raina Kuma “ina lallai su Abid tona asiri ne.”

“Sumayyah!, Sumayyah!!, Sumayyah!!!”
Kin kiran ba ‘daya ba ba biyu ba yasa ni waigowa tare kuma da san tuno Mai muryar tsammanin da nayi ko hakan ne
Malam Hamid ne idan ba idona ne suke min gizo ba,domin a sanina lokaci baiyi tsawon da zan manta da shi ba,kallon mamaki nake masa,nima shi yake min a hakan har ya qaraso inda muka tsaya,gaishesa nayi ya amsa da murmushi fuskarsa haka Abid ma ya gaishesa Malam Hamid ya miqawa Abid hannu suka gaisa yana tanbayarsa sunansa Abid yayi murmushi ya fa’da masa da alamu Malam Hamid ya birgesa guri na ya juyo ya maida dubensa gareni.

“Wato da ba zaki juyo ba ko?,harna fara tunanin qila bake bace,dan muryarki kawai na ji harna cigaba da tafiya nayi tunanin ke ce.”

Nayi murmushi nace,

“Eh nice nima da farko banyi tsammanin kai bane,saboda banyi tunanin sake ganin ka ba”
Murmushi yayi.

“To saboda me,bayan kinsan nan garinmu ne.”

Shiru nayi dan bani da tacewa danni ganin mai ku’di nakewa Malam Hamid Ina zansa wa raina tunanin ganinsa,karo na biyu
Maganar Malam Hamid ta katsemin tunanina.

“Kinyi shiru kullum na kira Halima saina tanbayeta ya kike takan cemin lafiya lau,Kuma har lambarki na buqata tace baki da waya yanzu haka da ta yayanki na nan kuke gaisawa,ni kuma banwai amsa ba saboda bansan mai zance masa ba idan na kira.”

Na jinjina kai alamun na gamsu da maganarsa.

Ya cigaba da cewa”na samu labari jarrabawar ku batayi kyau ba Allah yasa hakan yayi sanadiyyar samun nasararku a nan gaba,abun sam baimin da’di ba Sumayyah saina ji kamar ni abun ya faru dani.”

Dukda banason a tuno min abunda ya faru amma hakanan na daure
“Nace Amin nagode.”

Bai qyale maganar haka ba,ya ce,

“Yanzu kinga rana ta farayi kimin kwatancen gidanku na nan sai na samu lokaci nazo,mu qarasa maganar da bamu qarasa ba a baya”
Shiru nayi Ina tunanin maganar da nasan ta soyayya ce take nufi ba dan ina da buqatar sa a rayuwata ba na masa kwatancen gidan tare da jagorancin Abid a kwatancen kawai dai saboda kirkinsa nayi masa kwatancen amma gaba ‘daya a Raina kulllum bani yake Malam Hamid ba sa’ana bane a soyayya bare kuma aure dukda bansan koshi waye ba
Haka muka yi sallama yana Mai min alqawarin zaiso a satinnan insha Allah,daganan muka cigaba da tafiyarmu Abid yana tanbayata waye shi wannan,na masa bayaninsa,a matsayinsa na malaminmu ya dubeni

“Gaskiya Yaya Sumayyah yana da kirki sosai”
Nayi dariya na ce,

“Kai Abid daga ganin mutum haka ai ba’a shaidar mutum Karan farko.”

Ya jinjina kai ya ce,

“Hakane”,daganan muka sauya firar da wata.”

har muka qaraso bakin titi

Abun abun mamaki nan ‘dinma babu motoci ga zafin rana haka naji Kamar nasa hannu ka na fashe da kuka dan tsabar takaici da bakin ciki ga fangon kaya a hannu tsugunnawa mukayi muna roqon Allah ya kawo mana mafita,babu jimawa mota mai kyau sosai ta tsaya kusa da mu da ni ba ma’abociyar sanin mota ba bare nasan sunanta ko ku’dinta horn aka yi mana ganin bamu san mai ita ba mukayi shiru jin qarar bu’de motar yasa muka ‘dago kanmu,Abid naga ya qarasa gurin mutumin da yafito daga motar da alamu Abid yasan mutumin nima kallansu nayi.

“Kawu”naji Abid ya fa’da

Saurayin da Saida ya kirasa kawun na kallesa tabbas yana yanayi da Umminsu Abid

Tambayar Abid yayi

“Yana ganku anan Abid”

Abid ya sosa kai

“Mota muka rasa”

“Ku shigo na kaiku gida yi ma waccen da kuke tare magana” kawun ya fa’da da ba musu ya qaraso guna Abid ‘din niko tun kafin ya qaraso na miqe dan gajiye nake dama,kayan muka kinkima mu ka qarasa wajen motar,Abid ya bu’de min gidan baya na shiga a lokacin har kawun ya shiga mota abid ‘din ya shiga gidan gaba kusa da Kawun nasa sai a lokacin na gaida Kawunsu Abid ‘din ya juyo ya amsa kafin ya juya ina jinsa yana cewa

“Abid wannan wace ban gane ta ba”

Abid naji ya ce

“Yaya Sumayyah ce,’yar qanin Abbanmu ce Abba Abdullahi”

Naji yana ce wa

“Au ita ce rannan naje gidan na ku,Ummin ku ke bani labarin zuwan nata”

Waigowa Kawun yayi ya sake kallo na naji ya ce

“Yasu Asma’u ai sai yanzu naga Kamar ki da Asma’un”

Na ce masa

“Suna gida lafiya lau”

Da haka yaja motar cikin mintina qalilan muka qarasa gida parking yayi muka fito harda Kawun su Abid ‘din shine ya ‘dauki ledar saqon yana janmu da hira har muka qarasa cikin falon da ba kowa a falon sai Yaya Samir ‘din,yn danna wayar shi d Tv kunne Amma babu volume,sallamarmu ya amsa yana murmushi fuskarsa kusa da shi kawun ya zauna ya bashi hannu

“A’a Malam Samir ana gida kenan”

Yace

“Eh wllh Kawu Mahmud,yanzu da naji shiru basu dawo ba nake tunanin Kiran lambar Aunty Ramlah”

“Ayya wllh a hanya na ha’du dasu suna jiran abin hawa”

Ba muqarasa jin zancen ba muka wuce ciki, kitchen Ni na nufa,na kawo musu lemo zan tashi Yaya Samir yace

“Zauna mana firarki mu keyi da kawu Mahmud,yace waya ya kamata na siya maki yace kin isa riqewa”

Kallona na mayar ga Kawu Mahmud ganin mun haɗa ido yasa ni cikin jin kunya na maida kaina ƙasa,Muryar Kawu Mahmud naji ya na cewa

“Eh mana ki ɗago kanki mana Sumayya aikin isa riqewa nasan ƙawayenki duk wasu na da ita kuma insha Allah nasan ba bazaki wani abu mara kyau da ita ba”Har ya gama maganar ban ɗago ba sai ma cigaba da kallon carpet da nakeyi

Kawu Mahmoud naji ya ɗaura da cewa
“Tun kafin na gane ta na daiga yanayi da Asma’u tunanina ma da ko ƙanwar Asma’u ce saina tuna Asma’u bata da ƙanwa ashe ƴar tace,sosai tana da natsuwa Samir”

Muryar Yaya Samir naji ya bashi amsa da cewa

“Eh nayi tsammani zaka ganeta tana yarinya a Gwarzo tana maqalewa gurina Ummi tana cewa Sumayyahn Samir”

Naji kawu cikin ƙosawa yace

“Zaka fara surutun naka da sai anfi awa ba a qare ba kenan ko?dan Allah tashi muje yanzu a siyo mata wayar nan tun ina da kuɗi a jikina idan mun dawo sai ayi firar,in Kuma an kirani wani gurin shikenan”

Dariya ce take neman zuwarmin jin tattaunawar da suke yi,saika ɗauka abokaine ko nace ƴan biyu ko cousin brothers sun burgeni sosai dukda inada yaqini Kawu Mahmud ma ya girmi Yaya Samir tunda har tayi soyayyah da Aunty Asma’u dukda cewa bansan a yana shekara nawa sukayi soyayyar ba,ƙila soyayyahr ƙuruciya ce kawai,hakan sosai ya ƙara burgeni

“Taso muje ki za’ba da kanki”

Maganar Kawu Mahmud ta katsemin tunanin da nakeyi miƙewa nayi,hanyar komawa ciki nayi na kira Abid mu tafi tare ya tayani zaɓar danni ba wani zaɓen da zan iya ba na sani

“Ina zaki kuma?”

Muryar Yaya Samir ta sani juyowar na kuma tsaya da tafiyar da na fara idonsa na tsaye akaina yana kallona daurewa nayi cire idona daga nashi sannan na ce

“Abid zan kira yaya”

Yaya Samir ne ya harareni kafin yace
“A’a Malama dawo wuce mu tafi”ya ƙara sa maganar yana nunamin hanyar fita falon

“Toh Yaya”na iya fa’da na dawo da baya inda suke da Kawu Mahmud har ya buɗe ƙofar falon yana ƙoƙarin ficewa nima nabi bayansu

A motar Kawu Mahmud muka fita,Ba muyi tafiya mai nisa ba muka ƙara sa inda zamu siya wayar Green House parking Yaya Samir yayi muka fito duk a tare muka shiga ciki

Nida bansan wayoyi ba bare na iya zaɓar waya Yaya Samir ya zaɓarmin Iphone,da qarama maxfone da Kawu Mahmud yace a ɗaukar min acewarsa saboda iPhone bata riqe caji sosai shine kuma ya biya kuɗin wayoyin,har layuka aka siyamin akamin register Yaya Samir yayi min register saboda shine mai National ID Card sai ko Kawu Mahmud da yace ya bar nashi a gida,Murna sosai nakeyi da yin wayar tawa dan ban taɓa kawowa raina ba na kuma dinga musu godiya kamar kujerar Makkah suka biyamin,dan kam wayar babbace sosai wanda ya siyama wannan wayar ya samu dama da rabon ka Makkah ɗin ma zai biyama dan ina gani Kawu Mahmud ya ciro Atm ɗin shi aka cire dubunnan kuɗin wayar da sai lokacin na gasgata kuɗin wayar dan dan ko da aka faɗa da farko ban gasgataba

Nakasa Kuma fahimtar dalilin hidimar Kawu Mahmud mai yawa haka wajena Nidai nasan bamu da wata alaƙa banda kasancewarsa ƙanin Ummi Saidai tunda ya ambaci Aunty Asma’u na fara tunanin qilashima yana cikin samarin Aunty Asma’u tana budurwa tayi samari babu laifi “Hakanne ma banda hakan ai bazai miki hakan ba”zuciyata ce ta faɗa min hakan ta gasgastarmin,Dukda a halayyar Aunty Asma’u banyi tsammanin akwai wanda zai mata matukar so hakan ba saidai ance so gamon jini ne

*****
Ban jira na caza qaramar ba,Na kira layin, Halima,duk abinda zanyi bana manta Halima itace take fara fa’domin a raina,inasan Halima,fiye da tunani,inajin wayarnan dama tana nan tare za’a siyamana,Batul kam ba tada wata matsala,ita dai biye mana take yi,aurenta ma,tana gama makaranta za’ayi nafi tunanin  kirana dukda ban tabbatar ba

Har wayar ta gama ringing ta katse Halima bata ɗaga ba hakan yasani tunanin ko tana wani guri ko takai wayar caji da wannan tunanin na miƙe na maida ba wayar caji,na cigaba da saƙa da kwancewa wata damuwa ta fara ƙoƙarin ziyartata  

Wayar na maida caji ina cigaba da tunanin Halimah Allah yasa dai ba wata damuwa idan kaji shirun mai ƙaunarka yakamata ka shiga damuwa dan masoyi ɗaya yafi ma maƙiyinka sau million

Tunanin nawane ya katse jin ƙarar wayata daga cajin na ciro ta ina duba mai kiran nawa da bana raba ɗaya biyu Halima ce dan itace zan iya cewa kaɗai na kira a wannan lokacin

Da sallama bakina mai haɗe da zumuɗi na ɗaga wayar Halima ɗin

Ba tare da ta amsamin ba sai ƙarar murnar ta da ta cika kunnena ta ɗaura da cewa
“Sumayyah,ba dai kinyi waya ba,”
Nayi murmushi mara sauti Halima kenan nayi maganar a zuciyata daganan na furta
“Oh Halima haka kike yi kuma yanzu,kin cikamin dodon kunne da ƙara”
Tsaki Halima ta yimin ta ce
“Kiji ‘yar rainin wayau dan ina murna shine kike min wulaqanci,bari na kashe wayata dama ba katin gareni ba”…

<< Na Cancanta 12Na Cancanta 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×