Washe gari ranar dana dawo Aunty Asma'u ta dawo daga Katsina da zallar abunda yafaru dani acan ta dawo qarya da gaskiya,haka suka tattara maza da mata a gidan suna maida yadda akayi Abbah ne da yaji Hajiya ta fara zaginshi akan zancen har tana cewa bai bamu tarbiyya ba mu tattara mu bar mata gida baza ta iya ba kar a 'debo mata abun fa'da a gari ashe shine sakamakon komawa kanon da Abbah yayi saboda mu zamar masa jari yanaso yaji da'din mu zama 'yan iska har yaran 'ya'yan masu ku'di suna. . .