Skip to content
Part 7 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

Da farin cikin da yakasa ‘buya a gareni har ya bayyana ga fuskata dashi na isa gida ina kwa’da sallama Mama da naci Karo da ita tsakar gida tana zuba ruwa tukunya ta amsamin tana mai maida kallonta gareni.

“Lafiya kuwa, Sumayyah irin wannan fara’a haka?”

Na ‘dan turo baki nace,

“Kai Mama kin manta yau muka gama exam ta qualifying.”

Ta ce,

“Yo ai harna manta yi haquri Sumayyah.”

Murmushi nayi a raina ina ayyana mama kenan ita ba ruwanta ko yaron goye idan bata masa dai-dai ba tana iya basa haquri tunanin da nake na katse na ce,

“Mama ina Khalil,ko har yau ba’a taso su makarantar ba.”

Mama da take qoqarin ‘daukar tukunya ta ce,

“Na aikesa ya siyomin fulawa,jeki ki ‘dauki Humaira na barota ita ka’dai ‘daki.”

“Yawwa Mama yau wainar fulawa za’ayi ko?”nayi maganar ina fara tafiya.

“A’a sai dai wainar qwai qarewar ta fulawa,yadda rayuwa tayi tsada zaki ce wata waina tama fulawa za’ayi to yarinya ‘dan wake za’ayi.”

Na zun’buri baki jin abinda Maman ke fa’da na ce,

“Kai Mama daga tambaya.”

Tsaki tayi tare da cewa”Au tanbaya ce kenan,ki jini da yarinya ‘yar rainin wayau,ni wuce ki ‘daukarmin ‘yata karta tashi taji ba motsi,ki je da’kinku da ita,ki shirya ki ki kawan ita kizo kiyi kwa’bin ‘dan waken.”

Ba tare da nace komai ba ina qunkunai na shiga ‘dakin Maman tamu da inaji Maman na cewa.

“Oho dai yau yin ‘dan wake babu fashi.”

Saina iya cewa a rayuwata bani qaunar ‘dan wake shiyasa ko kusa bana ci idan ko naci sai dai idan inajin yunwa.

Aisha na kinkima kawai na baro ‘dakin kayan na cire na koma kitchen da na tarar dawowar Khalil kenan daga siyo fulawar kwa’bin mama ce tayi daganan ta anshi Humaira tabar kitchen din badan naso ba na jira tukunyar ta tafasa na fara sakin ‘dan waken cikin minti talatin na kammala na taqo plat da abuna na shiga ‘dakin Mama  ina ci.

Mama ta dubi ‘dan waken da nake baza uwar loma.

“Ke Sumayyah keda ba kya son ‘dan wake ya zakiyi da wannan da kika zubo,khalil yasa hannu kuci tare.”

Na ce,

“Mama yunwa na keji shiyasa,da khalil ‘din zanci abinci yayi ta’be ta’be da hannun nasa.”

Mama ta ce,

“Kya yi dai gulmarki kya gama,kuma Khalil ‘din bawan Allah mai ya ta’ba.”

Nace,

“Kai Mama muma ai bayin Allahn ne,kawai dan yaron yaci sunan Abbanku shikenan aita gatantasa,mu Kuma kakanmu ne fa, both side.”

Dariya Mama tayi ta ce.

“To ya ranki.”

Nima nayi dariya ba tare dana bata amsa ba.

Na kalli Khalil da yake ta kallona nace masa.

“Jeka ka wanko hannunka da ragowar klin ‘din da nayi wanke wanke da safe,saura kuma ka karar da klin ‘din.”

Kamar jira yake nayi maganar ya fice da gudu na bisa da da kallo Allah sarki Khalil idan ban mantaba yau cikinmu ba wanda ya karya muka tafi makaranta yau dole ne ma muji yunwa,nasan yanzunma da alama bashin fulawar aka ciyo sai abunda Abba ya samu yau idan ya dawo za’a bada kudin.

Shiru ne ya ratsa tsakanina da Mama da lokacin har Khalil ya wanko hannunsa ya fara cin abincin.

Mama ce tayi qoqarin katse shirun namu ta hanyar cewa.

“Sumayyah kina addu’a kuwa akan qualifying ‘dinnan taku kinsan komai kokarinka su irin wa’dannan jarabawowin sai da addu’a,tunda kuka fara jarabawarnan bana iya rintsawa saina kaiwa Allah buqatata akan jarabawarnan da kukeyi,yau ko da kanada yaqinin za’a samu ku’din biyama jarabawarnan kowa yanada burin yaga yaci,bare kuma ke da babu yaqinin hakan idan baki ci ba sai dai ki haqura da karatunnan dan kinsan ko gona Abbanku baida ita tasa takansa.”

Kai na ‘daga da hawaye suka wankemin fuska tunda mama ta fara maganar nan dan nima zullumina kenan murmushi nayi ina share hawayena na ce.

“Mama ina addu’a duk abinda zaifi zama alkhairi a rayuwata ya ha’dani da samunsa”
Mama ta jinjina kai tare da cewa.

“Haka ne Sumayyah kinyi tunani mai kyau,Allah ya baku sa’a ke da su Halima da sauran qawayenki dama duka musulmai.”

Nayi murmushi nace,

“Amin Mama.”

Mama kenan rayuwarta tana burgeni tasan yakamata ita dai inada yaqinin da Allah zai azurta mamanmu ba makawa zata kyautatawa ‘yan uwanta fiye da tunanin mai tunani sai dai ita haka tata jarabtar take,da inada yaqinin suma masu ku’din jarabtarsu ce Allah ya basu ku’din da a dalilinsu idan basuyi wasa ba sai su halakar dashi.

“Anjima idan an taso su Rumaisa makaranta saiku shirya kuje gidan Mama Atika ku yinar mata,kun da’de baku je ba”maganar da mama tayi ta katsemin tunani na na kalli Maman sororo jin kalmar da take fa’da.

“Kike kallona ko ba kiji mai nace bane”fa’din Mama.

Na ‘dan rausayar dakai na ce,

“Naji Mama amma gaskiya banason zuwa gidan Mama Atika,dukda bata da matsala amma ‘ya’yanta ko gaishesu mukayi basu amsawa kuma na fa’damiki irin abunda suke mana a banzace suke kallonmu gaskiya mama kiya haquri nidai ba zani ba.”

Mama cikin fushi ta fara magana

“Sumayyah na gaji da kalmomin ‘batanci da kike jifan dangina,danni dangina ba irin dangin ubanku bane,da dai danginku kikace suyi haka ina iya yarda,amma kowa yasan Mama Atika irin alkhairin da take mana dukda ba cikinmu ‘daya ba amma qannen Abbanku da suke ciki ‘daya ba wanda zai iya bugar qirji ya kawo muku koda kwancen ‘ya’yansu kusa,ina laifin Mama Atika wannan atamfar holland ta jikinki ba kwance Malika ‘diyarta bane,da wulakanci suke maku idan kunje ina zasu baku kaya,dan haka saikinje bazan zura ido aqi zumunci ba idan dangin Abbanku basu sanku ni nawa suna sanku”
Baki na zun’bura na ce.

“Mama ba zaki gane bane,amma ‘ya’yan mama Atika idan mukaje wulaqanci suke ma…”
Mama data kawo hannu zata bugemin baki nayi saurin rufe bakina da qunshe sauran maganata.

“Idan kika qara yimin magana saina mareki sakarai kawai”fa’din Mama da nasan a dalilin ita Bata zuwa gidan Mama Atikar sai dai ta turamu ta fa’di haka amma irin kallon banzar da ake mana da yada mana magana da akeyi idan mukaje abin ba ‘karamin ‘konamin rai yake ba shiyasa rabon da muje mun da’de tun sanda mukaje da kwancen kayan Aunty Abida ‘diyar Mama Atikar a jikina muna shiga gidan Aunty Abida da tana ganina cikin ‘kawayenta ta fara cewa

“Mai zan gani haka Sumayyah a baki kaya ko wata basu yi ba duk sun kwarko’de omo kike samu su ko,saida na cewa Mama dama karta baki su.”

Tana gama fa’dar haka ‘kawayennata suka kalleni suka sheqe da dariya
Haka cikin kunyar tozarcin da suka yimin na wuce cikin na ratsasu ta falon zuwa ‘bangaren Mama Atika da suka bini da dariya wata tana cewa da Aunty Abida
“Amma ince yarinyar daga qauye take ko?”

Ban dai tsaya saurara amsar da Aunty Abida zata bayarba na qarasa shigewa ciki
Tun bayan faruwar hakan naji bana sha’awar qara zuwa gidan saidai banaso na fa’dawa Mama saboda nasan ranta zai ‘baci gashi har hakan ya shafi zumuncin Mamar da Mama Atika gashi laifin bawai na Mama Atikar bane ‘ya’yanta sukamin hakan,kuma tun bayan faruwar haka Mama bata qara cewa muje gidanba sai yau
Maganar Mama ta katsemin tunanina tana cewa.

“Da zaki ce ba zakije gidan Mama Atika ba,ai kya tafi dangin ubanki nanda kwana biyar kije kiyi zaman bauta,da kafin ku girma daidai da gwanjo babu wanda ya ta’ba kawo muku,Mama Atika ba abinda bata yi muku harta da sabbin kaya dinko muku take,ai ina tunanin komai ‘ya’yanta suka yi muku,ba zaki ce ba zakije gurin Mama Atika ba,saboda cancantar mahaifiyarsu gareku,da Kuma yadda nake da Mama Atika a matsayinta qanwar mahaifina”

Kalaman Mama sunyi tasiri gareni,Dan gaskiya Mama Atika batada laifi tanasan ‘yan uwanta sosai laifin dama ‘ya’yanta ne suma basu fiye yi gabanta ba, nisawa nayi na ce
“Hakane Mama kiya haquri zamuje,Halima tace zatazo idan tazo saimu tafi tare”

Murmushi Mama tayi ta ‘dora da cewa

“Yawwa Sumayyah ki qara haquri da yanayin da rayuwarmu tazo mana da shi,ko bakomai nasan Allah yana sanmu dan rayuwar talauci jarabta ce,Kuma a yanzu ne zamu gane masoyanmu,dan da wani abu garemu zaki ga yadda dangi zasu riqa tururuwar zuwa wajenmu,amma yanzu wa kike gani,sai ‘dai’daiku musamman dangin Abbanku”

Wani abu naji ya tsayamin maqoshina jin Mama ta anbaci dangin Abbanmu dan tunowa da halayyarsu da nayi,Haqiqa zan iya cewa akwai banbanci mai girman gaske da muke gani a kowanne ‘bangare daga dangin mahaifinmu,hatta Baban katsina duk sallah sai ya ‘dinke duka ‘ya’yan qannensa amma bandamu a ciki,wannan banbancin ka’dai idan na tuno yakan qara sawa naji bana sha’awar zuwa Katsinan nan,domin ina zullumin rayuwar da zan tsinci kaina a can”

“Sumayyah  mai kike tunani ne,inata magana”

Muryar Mama da naji kamar daga sama ya sani dawowa daga duniyar tunanin dana fa’da,na kumayi saurin cewa.

“Babu komai Mama.”

Mama ta girrgiza Kai

“A’a Sumayyah ban yarda ba,sau biyu fa ina miki magana,hankalinki baya tare dani gaba ‘daya”

Bansan qaryar da zan yiwa Mama ba dan tabbas banji maganar da tayi min ba,sai yanzu

Mama ta dubeni ta ‘dora da cewa,

“Sumayyah ,ba zaki yi haquri da rayuwar talaucin da Allah ya ‘doramana ba ko,to wallahi wannan rayuwar ta talauci itace hanyar da ake fahimtar haqurinka,amma kina nufin ke baza kiyi ba ko,idan tunaninki zai qare a haka kina so ki ‘dorawa kanki wani ciwo ko,Ni da nake mahaifiyarki nayi haquri amma ke baki so kiyi,duk fa halin da zamu shiga ubangijinmu yana sane damu kuma yana tare damu.”

Murmushi nayi jin Mama tayi shiru alamu sun nuna ta kawo qarshen zancenta, Mama macace mai sanin yakamata,babban abunda nake qara jin da’di idan na tuno na samu shine uwa ta gari, tunanina na tsaida na maida kallona ga Mama nace,

“Mama sam ba tunanin talauci nake ba,saboda nasan idan nace shi zanyi ban yiwa kaina adalci ba,saboda mahalliccinmu da yafi kowa sanmu ya qaddari zuwanmu duniya haka,domin ya jarrabcemu.”

Mama ta ‘daga Kai tare da cewa,

“Naji to,fa’damin tunanin mai kikeyi?”

Na durqusar da kaina qasa da kwalla ta ciko idona nace,

“Mama banason zuwa Katsinan nan gaba ‘daya,nasan ba rayuwar ‘yanci zanyi ba,bansan wanna gurbi Baban Katsinan zai aje ni ba,idan naje can.”

Mama ta ‘dago kaina dake qasa tare da cewa,

“Kuka kike Sumayyah,Kar kiyi kuka kamar yadda nake yi duk lokacin dana tuno zaki tafi bigeren da ba’a damu da ku ba,saboda yadda Allah ya qaddara rayuwarmu zata kasance, bigeren da ake kallona a matsayin mai qashin tsiya dana hana babanku arziqi.”

Murmushi nayi na ce,

“Mama ba kuka na ke ba,yanzune ma maganarki zata iya sani Kuma”

Ta ce,

“Amma ga idonki da hawaye,shikenan Sumayyah Allah yana sane damu karki zubda hawayenki,da ba zasuyi anfani ba gurin zubarsu,saboda komai daga Allah ne.”

Na ce

“Shikenan Mama bari naje na huta ‘daki.”

Mama ta kalleni a lokacin harna miqe.

“Wannan ‘dan waken fulawar fa nufinki Khalil ne zai iya cinyewa?”Khalil ‘din na kalla da yake ta zuba lomar ‘dan wakensa,da ni ko tunda muka fara magana da Mama naji abinci ya fita raina shiko yana taci hankalinsa kwance,tausayi Khalil ya bani tunowa da nayi shima nan gaba zai girma matsalolin rayuwa su tarar masa kamar mu wanda godiyar Allah ka’dai take wadatarmu a kullum,dukda bana yiwa Khalil fatan ina fatan kafin ya girma komai ya wuce,cikin dauriya dai na cewa Mama
“Na qoshi”
Daganan na soma takawa ina barin ‘dakin da guntun hawayena,ina shiga ‘dakinmu na kwanta saman yagulallar katifarmu qirar ta ‘yan boarding saidai ta ‘yan boarding tafi tamu fasali dan tamu kamar tsumman tabarma take,kuka na rushe dashi ina tunanin rayuwar zumunci irin na yau danginmu basu rasa dukiyar da zasu tallafi rayuwarmu ba,amma sun barmu muna rayuwa irin wannan,hannu na kai sama cikin kuka ina cewa

“Ya Allah nasan baka manta mu ba,ya Allah mun bar komai a hannunka,ba muda kowa sai kai,Allah ka tsare mana zukatanmu ka qara mana haquri bisa jarabtarmu da kayi,domin ka fi kowa sanmu,Allah ka qara mana haquri,domin nasan wasu irin rayuwarmu suke so amma baka ba su ba.”

Wannan addu’ar na kanji Mama ta nayi sau tari a duk sanda abubuwa suka ta’azzara gare mu,wanda indai zan shiga ‘dakinta na Kan jiyo ta nayi da sai nagama saurarenta nakan shiga kona fasa shiga tun ina yarinya qarama na saba jin haka ga Mama,har na haddace su.

<< Na Cancanta 6Na Cancanta 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×