Skip to content
Part 2 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Ita ma Munaya hawayen ya ƙwace mata. Cak! Anti Zuwaira ta dakata da kukan da take yi, kamar wacce ta tuna wani abu, ko kuma wacce take cikin halin mamaki. Idanu ta zubawa Munaya, yadda take kuka da iya gaskiyarta, tamkar an yi mata wahayi da mutuwar Umma. Bata kula cewa ita take kallo ba, dan haka ta ci gaba da kukanta, har da zamewa ƙasa tana shure-shure.

“Wayyo Uncle Zayyad, ka tafi ka barmu.”
Karaf! Ta haɗa idanu da Anti Zuwaira. Hakan yasa ta ɗan shiga taitayinta.

“Dama kin taɓa saninsa ne? A ina kika san shi haka Munaya?”

A lokacin idanunta suka raina fata. Mahaukaciyar zuciyarta ta dinga gargaɗinta akan wuce gona da irin da take ƙoƙarin aikatawa.

“Ban san shi ba Anti. Tausayinki ne ya kamani, domin nima a baya na taɓa shiga makamancin irin wannan halin, a dalilin mutuwar saurayina Khalifa.”

Har cikin zuciyar Anti Zuwaira ta yarda da zancenta, wanda a zahiri ƙarya ta shirya mata, irin ƙaryar da bata taɓa sanin ta gwanance akai ba.

Dukkansu suka yi shiru, kowa da irin abin da yake saƙawa a cikin zuciyarsa. A daddafe ta miƙe tana bin bango. Ji take tamkar zuciyata za ta fito waje. Soyayyar Zayyad kaɗai idan aka barta da ita, zata iya, kasheta har lahira. An sha bata labarin yadda soyayya take, ita kuma take ganin tamkar aikin banza ne, da kuma rashin abin yi. Ashe dafin soyayya ya wuce duk yadda ake iya kwatanta shi.

Zuciyarta ta ci gaba da raya mata, ta koma falo kawai ta yi zamanta, ko babu komai kallon tangamemen hoton nan zai rage mata masifar zogin zuciya.

A firgice ta kalli hoton, ta sake mutsittsike idanunta. Haƙiƙa bata taɓa shiga tsananin firgici da tashin hankali ba, irin na yanzu. Hoton da ta gani ɗazu babu alamun murmushi akan fuskarsa bare akai ga dariya. Amma a yanzu, Dariya ce manne a fuskarsa wanda ya baiwa gefen kumatunsa daman lotsawa. Fararen haƙoransa tar! Tar!! Suka bayyana. A yanzu ya fi kyau fiye da sauran hotunan da ta gani a farko.

A hankali ta sulale ƙasa ta zube. Jikinta babu in da baya kyarma. A lokaci guda kuma, wani bahagon tunani ya kawo ziyarar bazata a cikin ƙwaƙwalwata. Zargi mai ƙarfi ya ci nasarar huda zuciyarta akan Anti Zuwaira.
Anti Zuwaira ta gani a gabanta tana kallonta sosai,

“Wai Munaya lafiyarki ƙalau kuwa? Ko dai da akwai abin da ke damunki ne?”
Ta haɗiye yamun da tasha wahala kafin ta iya tattaro su,

“Lafiyata ƙalau Anti. Hoton nan ne ya firgitani. Da farko sai naga kamar hoton baya dariya, a yanzu kuma, sai naga yana dariya.”
Ta bata amsa cikin rawar murya.

Anti Zuwaira ta ware idanu cike da mamaki,
“Dariya kuma? Ai tunda nake da Zayyad ban taɓa ganinsa yana dariya ba, bare kuma a hoto. Hasalima ya tsani hoto sosai, dan haka ne duk hoton da ya ɗauka za ki ga kaman an tursasa shi ne. Nakan sha wahala wajen yi masa magiya, sannan yake amincewa.”

A gigice Munaya ta sake kai dubanta kan hoton da nufin ta nuna mata. Sai dai ko sama ko ƙasa ta nemi haƙoran da ta gani a buɗe ta rasa. Ta lumshe idanunta tana jin hawaye suna sauka bisa kuncinta. Tabbas soyayyar Zayyad yana shirin haukatata. Ta yarda a yanzu ta bambanta da ‘yan matan da basu taɓa yin soyayya ba. Dama an gaya mata soyayya shaiɗaniya ce idan ta tashi sauya salo. Yau ga soyayya tana, shirin zarar da ita.

“Anti ki kaini ƙabarin Uncle Zayyad mana.”
Ta yi maganar cikin dakewa. Ta shirya binsa har ƙabarinsa domin ta gaya masa irin soyayyar da take yi masa, ko babu komai insha Allahu zuciyarta zata rage raɗaɗin da take yi mata. Za ta gaya masa, ba zata taɓa karɓar soyayyar kowa ba, har sai sun haɗu a cikin Aljannah.

“Na kula, kamar kin fara shaye-shaye. Idan kika je ƙabarinsa me za ki yi masa?”
Anti Zuwaira ta yi maganar cike da jin haushin Munaya.

“Anti Addu’a zan yi masa.”
“To baya buƙatar addu’arki. Kin ganni nan? Bana son ciwon kai. Muddin kika ce za ki saka mini damuwa babu ko shakka zan sakaki a mota ki koma wurin Ummanki. Duk son da nake yiwa abu muddin naga zai saka mini ciwon kai, zan ɗauki mummunan mataki akai. Kada ki kuskura ki ce za ki kai kanki in da Allah bai kaiki ba.”

Munaya ta kafeta da idanu cike da mamaki, bakinta kuma a buɗe.

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 1Na Kamu Da Kaunar Matacce 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×