Tunda Munaya ta koma gida, ta duƙufa da karatu, da kuma ibada. Shi kansa Zayyad kwana biyu ya rasa gane kanta. Yau har cikin ɗakin ya shigo. Tana kwance kanta a sama tana nazarin rayuwa. Bata san mutum ya shigo ɗakin ba, sai ganin inuwarsa ta yi. Da sauri ta waiwayo yana tsaye ya rungume hannunsa a ƙirji. Da sauri ta rarumi hijabinta ta saka.
Ya ƙaraso daidai ƙafafunta ya sunkuya yana kallonta.
"Na yi tunanin rashin ganina ne kaɗai zai iya sakaki a cikin wani hali? Me yake faruwa? Ko dai na yi maki laifi ne? Kwana. . .