Skip to content
Part 28 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Tunda Munaya ta koma gida, ta duƙufa da karatu, da kuma ibada. Shi kansa Zayyad kwana biyu ya rasa gane kanta. Yau har cikin ɗakin ya shigo. Tana kwance kanta a sama tana nazarin rayuwa. Bata san mutum ya shigo ɗakin ba, sai ganin inuwarsa ta yi. Da sauri ta waiwayo yana tsaye ya rungume hannunsa a ƙirji. Da sauri ta rarumi hijabinta ta saka.

Ya ƙaraso daidai ƙafafunta ya sunkuya yana kallonta.

“Na yi tunanin rashin ganina ne kaɗai zai iya sakaki a cikin wani hali? Me yake faruwa? Ko dai na yi maki laifi ne? Kwana biyu kin sakani a cikin damuwa. Ko gidan Hajiya kin daina zuwa. Kowa ya damu, yana tambayar me akayi maki? Kin kama kin kashe wayarki.”

Munaya ta sunkuyar da kai, sai kawai ta fashe da kuka. A hankali ta gaya masa komai da ya faru a tsakaninta da Hauwa. Ta ɗago cikin kuka ta ce,.

“Sun kashe Islam. Bata ji ba bata gani ba. Laifinta ɗaya, dan mahaifiyarta ta kasance a cikin su.”

Zayyad ya ji abun har cikin zuciyarsa. Dan haka ya ce,

“Ki tashi ki shirya, ki sameni a ƙofar gidan abokina.”

Yana miƙewa ya ji muryar Zuwaira. Da sauri ya shige banɗakin ya ɓoye. Ta dubi Munaya ta ce,

“Ke da wa kike magana na ji kamar muryar namiji? Kai muryar Zayyad na ji a ɗakin nan.”

Munaya ta zaro idanu ta ce,

“Ke ma ya fara yi maki irin gizon da yake yi min ko?”

Ta zabga mata harara ta ce,

“Ke awa zai yi maki gizo. Ki shirya ki rakani zan je wani ƙauye neman maganin fuskar nan tawa.”

Munaya ta jinjina kai kawai. Tana wucewa Zayyad bai fito ba, ta yi mamakin yadda ya ƙi fitowa. Sai ya leƙo ya yi mata alamun Zuwaira bata tafi ba. Ta sha mamaki, dan ita dai tasan ta tafi. Dan haka ta miƙe ta yi hanyar waje. Abin mamaki tana nan laɓe, kasancewar da kunnenta ta ji muryar namiji. Kuma bata yarda da Munaya ba a kwanaki biyun nan. Suka ci karo. Ta ɗan yi yaƙye. Munaya ta kauda kanta ta wuce, dole itama ta bi bayanta.

Zayyad ya fice kawai tare da ɗagawa Maigadi hannu.

Munaya ta koma ta canza kaya ta fice ba tare da Zuwaira ta sani ba.

“Idan kika kuskura kika bita wani wuri, ki tabbata kin shiga tarkonta.”

Ta jinjina kai, sannan ta ce

“Ka kaini gidan Hajiyata.”

Suna tafe a hanya ba tare da ya ci gaba da yi mata magana ba.

Suna shigowa gidan yara suka dinga yi mata oyoyo suna murna. Hajiya da Daddy sun kasa haƙuri da kansu suka fito suka tareta. Kunya duk ya rufeta da sauri ta durƙusa ƙasa da nufin gaida su. Hajiya ta ɗagota ta rungumeta.

Zayyad yana tsaye ya rungume hannayensa yana jingine da motarsa yana kallon su. Irin wannan farin cikin yake so yana gani a fuskar iyayensa.

Gaba ɗaya sun mance da shi. Sai da suka kusa shigewa sannan ta juyo ta kalle shi, suka yi wa juna murmushi.

Ayyuka sun yi masa yawa, amma kullum sai ƙannensa sun dame shi akan Anti Munaya. Yana sonta, ya shirya fuskantar kowacce iriyar rayuwa ce akanta. Yana jin farin cikin da bai taɓa zaton akwai ranar da zata zo ya ji irinsa ba.

Cikin hukuncin Allah an ɗauki azumi, wanda daga Zuwaira har Hauwa basa yi, kullum burinsu yadda za su iya ganin bayan juna.

Lokaci yana tafiya, su Munaya sun mayar da hankali akan karatun su babu ji babu gani. Alhamdulillah, Munaya tana samun rinjaye a yayin karatunta. Ta sami goyan baya ta kowanne fanni. Tana cikin farin ciki. Shi kuma Daddy ya tattara ya tafi Umra.

Bayan Sallah da Sati ɗaya aka ɗaura auren Zayyad da Munaya. Ɗaurin auren da akayi ya bayar da mamaki. A can Kano suka je akayi bikin. Ita kanta Anti Zuwaira ta je, amma bata san waye mijin ba. Duk wani abu na bidi’a dukka ɓangarorin sun hana ayi. Shi Zayyad bayan an ɗaura aure ya tattara da shi da abokansa suka dawo Kaduna. Munaya kuwa a ranar kwana ta yi tana kuka. Ita kanta ta rasa kukan me take yi. Su kansu su Hajara tunda aka ce an ɗaura auren Zayyad da Munaya suke kuka. Ƙarfe biyun dare suka tashi dukkansu suka yi nafilfili na nuna godiyarsu ga Allah. Ita dai Hajiyar Zuwaira bata san waye mijin ba, amma kuma ta yi murna. Hatta Zuwairar sai da ta tambayi Hajiyar ko tasan waye mijin Munaya, ta ce batasan waye ba, amma kuma ta yi mata addu’a.

Zuwaira ta fara jin haushin yadda duk yadda take kulawa da Munaya a ce yau ana ɓoye mata miji. Daga baya ta danganta hakan da matsalar auren Mubaraak.

Kowa idan ya tambayeta ina Mubaraak, ta kan ce ya gudu ya kwashe mata kayayyaki yaso kuma ya kasheta. Ita dai mahaifiyarta sai dai kallonta kawai take yi da idanu.

An shirya Munaya zata koma Makaranta kafin ayi maganar tarewarta. Munaya dai har yanzu kuka take yi.

Hajjo ta ce,

“Kukan me ne ne haka? Godiya za ki yi ta yi wa Allah. Amma kukan bai da amfani.”

Zuwaira dai sai kallonsu take yi. Can Hajjo ta saka waya a kunne ta ce,

“Hello Uncle. Har yanzu kukan take yi.”

Ta ɗan yi shiru, sannan ta tura mata wayar a kunne. Bata yi magana ba sai kuka. Yana daga kwance yana jin sautin kukanta yana ratsa shi.

“Matar Uncle Zayyad. Ko matar matacce ne?”

Gani suka yi ta ɗago fuskarta tana murmushi tana share hawaye.

“Goge hawayenki in baki labari.”

Duk abin da ya ce ta yi sai ta yi.

Ya ci gaba da cewa,

“Mu godewa Allah. Babu wanda ya zaci wannan mafarkin zai tabbata. Kin ga ikon Allah ko? Kin ga yadda matacce yake iya tashi ya auri rayayya ko?”

Wannan karon sai da sautin murmushinta ya isa har zuwa kunnuwansa.

“Ka da ki yarda ki shigo garin nan kina kuka. Idan ba haka ba zan gayawa duniya kin auri matacce.”

Abin mamaki Munaya har da dariya. Duk suka dubi juna. Zuwaira ta ce,

“A, bani angon mu gaisa mana.”

Ɗif! Zayyad ya kashe wayar. Ta ji haushin yadda Zuwaira ta katse masu hirarsu. Shi kuwa da ya ji muryar Zuwaira Hussain ke faɗo masa a rai.

Haka aka Munaya ta dawo gidan Zuwaira. Hajara ta ɗauketa a mota, suka fice. Kai tsaye wani ƙasaitaccen wuri ta wuce da ita, wanda aka haɗa masu ‘yar ƙwarya-ƙwaryar Walima. Wannan shirin Hajara ce da Amina, da kuma su Suhaima. Wani ƙaramin ɗaki aka shiga da ita, akayi mata ado da wani baƙin leshi mai walwali. Wurin an saka cool music. A lokacin Zayyad ya ƙaraso shi da abokansa su Mus’ab.

Duk da ya tsani irin abubuwan nan, amma wannan ya ɗauki hankalinsa. Musamman ma da babu hayaniya. A tsaye ya hango Munaya kanta a ƙasa. Tunda ta hango shi gabanta ke wani irin faɗuwa.

Sannu a hankali ya tako ya ƙaraso gabanta, ya jawota jikinsa ya rungume tsam! Dukkansu suka saki ajiyar zuciya. Ya lalubo kunnenta ya raɗa mata,

“Kin fi ko yaushe kyau. Madalla da shigowarki cikin iyalan Mohammed Hashim.”

Bata iya magana ba, sai wasu siraran hawaye da suka sakko bisa kumatunta. Ya ɗago fuskarta ya manna mata Kiss a goshi, sannan ya kamo hannunta suka nufi in da aka tanadar masu. Tafi kawai yake ji ko ta ko ina. Hotuna kuwa hatta lokacin da yake rungume da ita duk an ci nasarar ɗauka.

Bayan sun zauna yana riƙe da hannayenta kamar za a ƙwace masa ita. Amina ta fara buɗe taron da addu’a, daga nan sai Hajara ta karɓa. Tarihin amarya ta fara da bayarwa, da gwagwarmayar da tasha. Hajara ta ji hawaye yana zubo mata. Ta ɗan yi shiru. Daga bisani ta ɗago kai ta dube su, yadda suka yi kyau. Ta yi magana cikin kuka cikin dariya ta ce,

“Finally Munaya ta zama matar Uncle Zayyad.”

Ta yi saurin ajiye abin magana tana ci gaba da goge hawayenta. Afra ma ta tashi ta yi jawabinta. Daga nan aka ci aka sha. Ita dai Munaya tuni mijinta ya jawota gefe, saboda kukan da take yi, ya rungumeta yana raɗa mata wasu maganganu a kunne. Hakan ya ɗauke kukan da take yi, ta yi shiru tana saurarensa tana kuma sauke ajiyar zuciya.

Ba su suka bar wurin ba, sai kusan sha ɗayan dare. Hajara da Munaya da Amina duk a gidan anti Zuwaira za su kwana. Zayyad ya sumbaci hannunta ya yi mata sai da safe.

Yanayin da suka kasance da Zayyad ya zama wani yanayi ne mai girman da ba zata taɓa iya goge shi a cikin rayuwarta ba. Tunda suka dawo sun fahimci Anti Zuwaira bata nan, dan haka su Amina suna ta hirar dinner ɗin da suka haɗa, ita dai ta rungumi filo tana tuna abubuwa masu yawa a tare da mijinta.

Can ta dube su ta ce,

“Wai yau ni ce matar Uncle? Wallahi ji nake yi kamar mafarki kawai nake yi.”

Hajara ta mintsineta ta fasa ƙara. Duk suka yi dariya suka ce,

“Kin dai tabbatar idanunki biyu ko?”

*****

Kwanaki huɗu bayan bikin Munaya. Ta jiyo Zuwaira tana magana akan ranar da za ayi naɗin sarautar Hauwa, dan haka ta kirawo mijinta ta sanar masa. Ta kira Hajara. Dan haka sun so su yi mahaɗa a gidansu Zayyad amma ta ce ba zata iya zuwa ba, kunyar Hajiya take ji. Dan haka suka haɗu a gidan su Hajara. Bayan sun tattauna suka nufi gidansu Amina, akayi magana da mahaifinta.

Ranar naɗin Sarautar a tare suka isa gidan. Kowannensu yana ɗauke da ruwan Zam-zam da akayi addu’o’i a ciki. Suna kallon lokacin da Zuwaira ta shiga. Dan haka su suka kasance na ƙarshe a shigowa.

Suna tsaka da musayar magana da Zuwaira, Zayyad ya fara shigowa. Lamarin da ya gigita kowa da ke wurin. Duk ya bi su da kallo. Sun shimfiɗa duk abubuwan tsafinsu. Ga hular da za a sakawa Hauwa. Zuwaira ta fi kowa kaɗuwa. Ta nuna shi da yatsa ta ce,

“Kai ne ko fatalwarka?”

Ya dubeta cike da ƙyama ya ce,

“A addininmu babu fatalwa. Kun zaci na mutu ko?”

Munaya ce ta biyu, sauran duk suna biye da ita a baya,

“Kin daɗe kina son sanin waye mijina. Yau dai na zaɓi wannan ranar in sanar da ke Uncle Zayyad shi ne mijina da aka ɗaura mana aure. Dama na gaya maki, ina sonsa, dama na gaya maki shi ne mijina.”

Zuwaira ta dawo da kallonta ga Munaya cike da mamaki.

Alhaji Mohammed Hashim da Hajiya Nafisa suka bayyana, kowa fuska a ɗaure.

“Kun cuci kanku. Kun zaci Allah zai barku ne? Ke Zuwaira Allah ya isa tsakaninmu da ke, mun riƙeki tsakaninmu da Allah. A she ke ba haka bane. Munaya ta taimaka mana, wurin an karar da mu akanki. Da ba haka ba, da yanzu kun halastawa wasu ƙattan banza jininmu.”

Dukkansu Munaya suke kallo cike da mamaki da al’ajabi. Yanzu Munaya ce ta lalata masu dukkan shirinsu kenan? Zayyad ya dube su sosai ya ce,

“Ni na yi maku kama da wanda zaku iya tsafacewa?”

Hauwa ta dube su sosai ta ce,

“Yau kun kawo kanku in da ba zaku fito ba.”

Zamani ya fara wani irin surutai. Zayyad ya ce kowa ya koma baya wannan yaƙin nasa ne. Munaya ta dawo kusa da shi ta ce,

“Wannan yaƙin namu ne ni da kai.”

An fafata, sun haɗa wani irin tsafi mai tsananin zafi. Sai dai duk abin su, basu isa su ja da Ayar Allah ba. Tun su Zuwaira suna iya mayar da martani har suka ci nasarar kai su ƙasa. Duk yadda suke ihu hakan bai sa sun sarara ba. Amina da sauran duk suka shigo suna Karatun Alqur’ani. Wuri ya gigice baka jin komai sai ihunsu. Suna kallon yadda fuskokinsu duk ta ƙone.

Raɗaɗin da suke ji ya wuce misali. Gasu nan dai suna raye, amma kuma babu wani abu da zai iya yin amfani da jikinsu. Hatta ɗiyarta Nasreen kwance take tana ihu. Sun koma babu kyawun gani. Abubuwan tsafin suka zama toka. Sannan Munaya ta dube su ta ce,

“Dama na gaya maku sai na zame maku masifa a cikin rayuwarku. Insha Allahu ba zaku mutu yanzu ba, sai kun ɗanɗani irin azabar duniya da kuka ɗanɗanawa mutane da yawa, kafin ku je can ku haɗu da azabar lahira.”

Sai a lokacin Mubaraak ya shigo saboda tsantsar tsoro. Ya kalleta ya yi saurin kauda kai,

“La’ananniya na sakeki saki uku. Insha Allahu angulu su za su ci naman jikinku.”

Babu lokacin neman yadda akayi Mubaraak ya fito, babban damuwarsu a yanzu su daina jin raɗaɗin da suke ji.

*****

Hatta gidan Zuwaira ya ƙone. Allah ya taimaki Munaya ta kwashe komai nata ta kai gidansu Hajara. Dan haka bayan kwanaki biyu ta koma gidansu. Anan ta sami Hajiyar Zuwaira an, gaya mata duk abubuwan da suka faru. Ta yi kuka, ta kuma godewa Allah da yasa ta yi riƙo da addininta. Ta daɗe tana zargin akwai abubuwan da Zuwaira take aikatawa, amma rashin samun shaida yasa ta zuba idanu. Abba da kansa ya yi ta mata nasiha. Dan haka ta aika har wurin dangin mahaifinta ta sanar da masu da komai. Haka kowa ya yi baƙin ciki ya haƙura.


Komai ya zo ya wuce kamar ba ayi ba. Aka shirya Munaya aka kaita gidan mijinta a Kaduna unguwar Dosa. Haƙiƙa Munaya taga abin da ake kira gata. Shi kansa gidanta abin kallo ne. Bayan an kaita ne, aka sake ɗaukarta aka kaita gidan iyayen mijin. Ta ga tarba, dama kuma ta zaci hakan. Hajiya ta yi kukan farin ciki babu iyaka.

Ƙarfe tara su Hajara suka watse cike da kewar juna.

Zayyad ya, shigo cikin kaya na alfarma. Ya yi kyau fiye da yadda tasan shi. Bayan sun yi Sallah ya ce ta je ta sauya kaya ta same shi a ɗaki. Ta yi shiru. Gani ya yi bata da ninyar tafiya. Ya wuce kawai.

Sai da ya gama kintsawa ya dawo ya sameta yadda ya barta. Jikinta har kyarma yake yi. Ya zagaye ta bayanta ya cire mata ɗankunne yana sunsunan wuyarta. Ita dai ta kasa motsi. Ɗaukarta ya yi cak! Ya dawo falo. Duk yadda yaso ta ci kaji ta kasa, dole ya haƙura ya ƙyaleta. Tana ganin ya kaita gado ta fara ƙoƙarin guduwa. Ya dinga yi mata raɗa a kunne, har ya ci nasarar kashe mata dukkan ilahirin jikinta. Tana ji tana gani ya rabata da dukkan kayan jikinta. Bakinta yana rawa tana so ta yi magana ya haɗe bakinsu wuri guda.

Ta shiga yanayin da tunda take a duniya bata taɓa shiga irinsa ba. Babu shakka aure akwai daraja da tarin girma. A wannan dare Zayyad ya raba Munaya da budurcinta.

Ta yi kuka har ta ji babu daɗi, amma ya ƙi ya ɗaga mata ƙafa. Bata zubar da jini ba, amma duk ta tsattsage sannan taga jini kaɗan, amma bai sauka zanin gadon ba. Zai kaita banɗaki ta ƙi yarda. Ta jawo zanin gado ta nannaɗe jikinta. Ta jima a cikin banɗakin tana tunani kala-kala. Addu’a take yi, kada Allah yasa mijinta ya juya mata baya watarana.
Tana ganinsa ya shigo ta ƙudundune tana rufe ƙirjinta. Ya ƙaraso ya rungumeta tsam a cikin ruwan.

Rayuwarsu rayuwa ce mai sauƙi, domin kuwa da shi da ita sun zauna sun fahimci juna. Ya gaya mata irin abubuwan da yake so, da kuma waɗanda baya so. Duk ta amince.

Ranar farko da suka fara fita zuwa gidansu. Da isar su ta rufe fuskarta saboda tsananin kunya.

Hajiya ta rungumeta tana saka mata albarka. Bayan sun zauna ne Zayyad ya dubi Hajiya ya ce,

“Hajiya ki ƙara saka mata albarka. Duk yadda nake tunanin kirki da mutuncinta abin ya wuce haka.”

Munaya ta ji daɗin yabon da mijinta ya yi mata. Dama kuma ta, gaya masa, idan ta yi kuskure kada ya sanar da kowa ya fara gaya mata ne, insha Allahu za ta kiyaye.

Har yamma bai dawo ba. Munaya da Suhaima da Ruma suka faɗa kitchen. Hirar tafiyarsu Hajj kawai suke yi.

Sai dare ya dawo, ya sameta ita kaɗai a kitchen. Ta baya ya rungumeta yana sunsunanta. Ta ɗan langwaɓe ta ce,

“Sannu da zuwa mijina.”

Ya yi magana cikin raɗa,

“Yauwa matata. Kin yi fushi ko?”

Ta girgiza kai,

“Na dai yi missing ɗinka.”

Ya juyo da ita suna fuskantar juna,

“Nima haka. Na ƙosa in dawo in yi arba da kyakkyawar fuskar nan taki mai kyau.”

Suhaima ta ɗan yi gyaran murya. Munaya ta ruɗe tana ƙoƙarin ƙwace kanta. Ya yi murmushi kawai. Yana zuwa fita ya dungurewa Suhaima kai, ta turo baki tana ‘yar dariya.

*****

Cikin hukuncin Allah sun sami daman zuwa aikin Hajj. Abin farin cikin harda Amina da Hajara.. Suna dawowa suma aka saka masu rana. Wannan lamari ya ƙara saka masu ƙaunar juna. Sun sake kusanci da Ubangijinsu. Munaya ta kan sami matsala da Zayyad na zamantakewa, amma bata taɓa barin abun ya yi nisa ba. Da kanta take kwantar da kai ta gyara rayuwar aurenta. Bata taɓa ɗaga muryarta tafi ta mijinta ba.

Tasan hanyoyin ankarar da shi kura kuransa. Idan ya dawo yana cikin damuwa tasan hanyoyin da za ta saka shi cikin farin ciki.

Yau sun fito wajen siyan Ice cream kamar yadda cikin da ke jikinta yake saka mata kwaɗayi. Wani saurayi ya biyota da gudu. Duk suka tsaya suna kallonsa,

“Sunana Salim. Ni ne wanda kika taɓa taimako daga tarkon su Zuwaira. Ga wannan na gani a cikin Alqur’anin da kika bani. Duk irin neman da na yi maki ban ganki ba, ni kuma duk in da zan fita da su nake fita ina fatar Allah yasa in ganki.”

Munaya ta gane shi, ta karɓa ta zare takardar ta miƙa masa kuɗin,

“Wannan shi ne mai mahimmancin. Kada ka damu, kaje kawai.”

Yaron nan ya durƙusa a har ƙasa yana gode mata. Ta yi murmushi kawai ta jawo mijinta suka wuce tana bashi labari.

A lokacin kiran Mubaraak ya shigo wayarsa ya ɗauka suka gaisa. Anan yake cewa ya ga su Zuwaira a wani bola an yasar da su babu mai kallonsu. Mamaki ya kama su. Dama Zuwaira basu mutu ba? Ya basu labarin yadda suka zama abin kallo, da ƙyamata musamman yadda har duniya tasan munanan halayen da suka sami kansu da shi a baya. Ya kwatanta masu wurin suka ce za su je. Da yake Mubaraak ya nemi afuwan kowa, musamman ma Munaya. Ta nuna masa komai ya wuce.

Abin mamaki suna zuwa suka sami sun mutu anan kan bolar. Innalillahi Wa inna ilaihirraji un. Rayuwar kenan fa shikenan sun yi mutuwar wulakanci kuma za su koma su tarar da abubuwan da suka aikata. Duniyar da suke nemanta idanu a rufe yau gata nan ta juya masu baya. Zayyad ya nemi wasu matasa ya basu kuɗi suka haƙa rami anan bolar aka haɗesu wuri guda aka rufe, gudun kada su dami jama’a da wari. Mutane da yawa sun taru, kowa da irin abin da yake cewa. Babu wata magana mai daɗi daga bakin mutane. Kowa tsine masu yake yi, da fatar azaba mai raɗaɗi.

Munaya ta kira gidansu ta gaya masu. Hajiyar Zuwaira ta yi kuka har ta ji babu daɗi. Ita kuwa Munaya duk yadda ta nuna damuwarta Zayyad ya bi dukkan hanyoyin da zai iya ya toshe faruwar hakan.

Bayan ta koma gida ta warware wasiƙar mahaifinta. Nasiha ce kawai yake yi mata akan ta riƙe addininta. Hawaye suka wanke mata fuska. Shikenan rayuwar. Duk wanda ya ɗauketa da zafi ta ƙona sa. Zayyad da shigowarsa kenan ya sameta a tsakiyar gado tana kuka. Ya jawota jikinsa ya dawo da ita bisa ƙirjinsa yana shafa gashin kanta.

“Babyna bana son kuka kin sani ko.”

Ta sake marairaicewa ta kwantar da kanta sosai tana shafa cikinsa,

“Dole in yi kuka.”

Bai bari ta ƙarasa ba, ya saka harshensa yana ɗauke hawayen, sannan ya tallabo fuskata sosai yana dubanta.

“Zayyad ɗinki yana kusa da ke. Ba zai bari wani ya wahalar da ke ba. Ba zan bari ki zauna cikin damuwa ba. Mu godewa Allah, da ya yo mu a musulmai masu imani da yarda da ƙaddara. Ki gode Allah ki godewa iyayenki. Tabbas da ace bamu kasance masu ibada ba, da neman kusanci da Ubangiji da tuni su Hauwa sun ci galaba akanmu. Yi mini wani abu in tabbatar da kin saurari nasihata.”

Ta ɗan ware idanu ta jawo shi sosai tana yi masa abin da ya fi so. Daga nan ni ‘yar mutan Borno na tattare littafaina na yi saurin barin ɗakin, domin in bar ma’auratan su gabatar da soyayyarsu ba tare da na ga sirrinsu ba.

Cikin Munaya ya yi girma, dan haka bata iya yin komai. Zayyad ya nemi hutu a wurin mahaifinsa ya dawo mai renon ciki. Ko wash! Ta ce sai Zayyad ya kalleta. Da kansa yake kama hannunta su fito suna tafiya a ƙasa domin zagayawa. A lokacin take tambayarsa me ya ba Baba maigadin Zuwaira? Ya gaya mata yadda ya sauya rayuwarsa daga mai kwana a cikin talauci zuwa mai kwana a cikin rufin asiri. Ta gyaɗa kai,

“Nasan halinka mijina. Kana da adalci, kana da zuciya mai kyau. Na fi kowacce mace sa’a a duniyata.
Ya yi murmushi kawai ba tare da ya furta komai ba.

*****

Cikin hukuncin Allah Munaya ta sauka lafiya. Ta santalo ƙaton ɗanta namiji. Ya dubeta ya ce,

“Abba muka samu ko?”

Ta maƙale kafaɗa ta ce,

“A’a Daddy ne.”

Ya ce,

“Masha Allah. Allah ya raya mana Mohammed.”

Haka rayuwar ta miƙa wasu suna cewa sun bata shekara ɗaya in dai namiji ne. Ga shi a yau sun yi shekaru biyar da aure, amma namijin nan bai canza mata ba.

Har gobe ita ce tauraruwarta, domin ita bata da girman kai, duk in da tasan za ta sami ilimin kula da miji da danginsa tana ƙoƙarin kai kanta. Alhamdulillah, haihuwarta biyu, Muhammad Muhseen da kuma ‘yar babynta mai sunan Hajjo, suna kiranta Afaf.

A yau kuma sun ci ribar karatu tunda suke ɗauke da kwalin degree.

Alhamdulillah.. Anan muka kawo ƙarshen wannan labari . Ina kira ga ‘yan uwana musulmai da su yi amfani da abubuwan ciki masu kyau, su watsar da marasa kyau.
Dan Allah mu dage da karatun Alkur’ani, da kuma sadaka ga mabuƙata na kusa da mu. A dage da istigfari, da Salatin Manzo S.A.W
Na Sadaukar da wannan labari a gareku masoyana, a duk in da kuke a faɗin duniya.
Taku har kullum Fatima Ibrahim Garba Ɗanborno
MRS J.T.Z
Oum Ashmaan.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 27

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×