Cikin runtse idanu ta fara addu'a. Jin shiru yasa ta ɗan buɗe idanunta domin ganin me ke faruwa. Dukkansu ita suke kallo cike da mamaki. Wacce aka kira da Hauwa ta zazzaro mata idanu,
"Ke! Ni ba mayya ba ce, bare ki fara tofa mini addu'o'i. Ƙawata mai kwashe-kwashe, yau kuma ina kika samo mana wannan?"
Duk suka yi dariya. Anti Zuwaira ta dubeta ta ja mata tsaki sannan suka yi gaba, ba tare da sun sake dubanta ba. Bata da wani zaɓi da ya wuce bin bayansu.
Abin mamaki da al'ajabi. Falon. . .
Why can’t I read please
Thank you very much this novel is very nice very special gift from you to us thanks