Skip to content
Part 4 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Cikin runtse idanu ta fara addu’a. Jin shiru yasa ta ɗan buɗe idanunta domin ganin me ke faruwa. Dukkansu ita suke kallo cike da mamaki. Wacce aka kira da Hauwa ta zazzaro mata idanu,

“Ke! Ni ba mayya ba ce, bare ki fara tofa mini addu’o’i. Ƙawata mai kwashe-kwashe, yau kuma ina kika samo mana wannan?”

Duk suka yi dariya. Anti Zuwaira ta dubeta ta ja mata tsaki sannan suka yi gaba, ba tare da sun sake dubanta ba. Bata da wani zaɓi da ya wuce bin bayansu.

Abin mamaki da al’ajabi. Falon nan cike yake da manyan alhazai, waɗanda suka ci suka tada kai. Kowannensu yana cin abin da ya gadama. Naman da suke yanka ta kaiwa kallo. Duk yadda ta kai ga gane dabba, wannan dabbar ta yi mata wahalar ganewa. Namar dai tana yi mata kama da gangar jikin ɗan adam ne, aka cire kai da ƙafafu. Fitsari ta ji yana shirin kubce mata, a sakamakon wani ƙaton mutum da ya zuba mata idanu yana siɗe baki.

“Zu Baby ina kika samo wannan ‘yar shilar?”

Anti Zuwaira dai fuskarta ta nuna bata ji daɗin ganinsu a gidan Hauwa ba. Hasalima a zuciyarta tana danasanin zuwa gidan. Dan haka bata ce komai ba, ta yanki namar nan ta cusa a baki tana lumshe idanu. Daga bisani ta yi wani irin firgita, ta jawo hannun Munaya suka, wuce can baya wurin Hauwa.
Munaya ta ja ta tsaya tana kallon abin al’ajabin da tunda take a duniya bata taɓa gani ba. Anti Hauwa ce ta murƙushe shirgegen Shanu ta yanka. Ashe maganar da ta gayawa Anti Zuwaira da gaske take yi. Babu wani a kusa da ita, ita ɗaya take wannan aiki. Ta ɗago tana murmushi.

“Kin ga har aikin gama ya gama ko?”

Anti Zuwaira ta ce,

“Lallai kin yi ƙoƙari.”

A lokacin ƙarar wayar Anti Hauwa ya cika kunnuwar kowa. A natse ta ɗauka, ba tare da ta goge jinin ba. Gaba ɗaya ta buɗe muryar wayar ta yadda kowa ke iya ji.

“Allah ya yi wa mijinki rasuwa, a dalilin hatsarin mota.”

Duk suka dubi juna suka yi murmushi. A lokaci guda kuma sai suka saka kuka. Anti Hauwar ta kiɗime sosai. Munaya ta gaji da kallon film ɗin da take yi, tana da buƙatar nesanta kanta da mutanan nan. Ko rantsuwa ta yi ba zata yi kaffara ba, mutanan nan gaba ɗayansu aljanune masu shan jinin mutane.

‘Ko dai shanun nan da ta yanka mijinta ta yanka?’

Zuciyar Munaya ke yi mata waswasi. Jikinta babu ta in da baya kyarma, musamman da taga kamar tana nunota da wuƙa. Hayaniyar da ta cika tsakar gidan yasa gaba ɗayansu suka yo waje. Munaya ta, ware idanu. Gawar mijin aka shigo da shi, jikinsa duk jini. Da sauri ta waiwayo tana son kallon Anti Hauwa. Kallon duniyar nan ta yi mata, amma babu jini a ko ina na jikinta. Tana son ganin yadda mutanan falon za su yi, dan haka ta bi bayansu jikinta yana kyarma. Anan ma babu kowa a falon, kamar ba a taɓa halittar mutane a ciki ba.

Munaya ta jingine da bango ta runtse idanu tana jin wani irin jiri yana ɗibarta. Anan ta kife ba tare da ta sake sanin wani abu da ya biyo baya ba.


A natse ta buɗe idanunta tana jin ko ina na jikinta ya yi mata nauyi. Duk yadda taso ta tuna abin da ya faru hakan ya gagara. Ta juya ɓarayin dama, anti Zuwaira ce ke danne-dannen waya. Ta sake juyawa hagunta likita ne ke tsaye yana fasa allurai. A take ta gane likitan da ta ganshi ne a gidan Alhaji Mohd Hashim. Bata ce komai ba, ta mayar da idanunta ta rufe.
“Sweetheart ya kamata yau ki bani lokacinki, na yi matuƙar kewarki.”

Zuwaira ta ɗago a kasalance ta ce,

“Ka dai bi a hankali, kada ƙanwata ta farka.”

Ya yi murmushi tare da zagayowa ya jawota a jikinsa tsam yana shinshinarta. Cikin raɗa ya ce,

“Allurar barcin da na yi mata tana da ƙarfi ba zata tashi yanzu ba.”

A take suka fara wasu abubuwa masu matuƙar tayar da hankali. Munaya ta ware idanunta tana kallon yadda Anti Zuwaira ta saki jiki har yana rabata da rigar jikinta. Munaya ta mayar da idanunta ta rufe ruf! Zuciyarta ta dinga azalzalarta. Bata taɓa sanin Anti Zuwaira ƙazama ba ce sai yau. Ta yi danasanin zuwa gidanta.
Hawaye suka dinga bin gefen kuncinta. Likitan da ke duba surukinta da shi take irin wannan aikin. Amana ta yi ƙaranci a zuciyoyin al’umma.

‘Yanzu a wurin waye zan san haƙiƙanin abin da ke damun mahaifin Zayyad bare in taimaka masa? Likitan nasa maci amana ne.’ Tabbas zuciyarta tana sanar da ita, akwai wani babban sirri mai matuƙar girma da Anti Zuwaira ta daɗe tana ɓoye shi.

Kamar an ce ta buɗe idanu, ta sake ganinsu a cikin ƙazantacciyar yanayi, har yana neman ya wuce iyaka. Hakan yasa ta fara tari mai ƙarfi. Aikuwa da sauri suka rabu, ta yi sauri ta mayar da kayanta. Dukkansu sun ji haushin Munaya kasancewar idanunsu ya gama rufewa.

Buɗe idanunta ta yi sosai, abin mamaki basa nan a ɗakin. Hannu ta saka ta cire ƙarin ruwan ta lallaɓa ta bi bayansu. Ƙofar ta murɗa wanda batasan ko Ƙofar me ne ne ba. Ta leƙa ta hango su cikin yanayin da tunda take bata taɓa gani ba. Da sauri ta koma ta jingine da jikin bango tana Salati.
Ta kai mintuna goma a wurin, daga bisani ta koma, ta sake murɗa wata ƙofa. Gadaje ne sun kai arba’in, kowanne ɗauke da wasu abubuwa a rufe da farin ƙyalle. Tana ƙoƙarin shiga ta ji an yi magana daga bayanta,

“Nan ba hanya ba ce. Me kike nema?”

Da sauri ta dawo da baya tana duban idanun Nas ɗin.

“Dan Allah ina ne banɗaki?”

Ta tambaya cikin firgici da tsoro.

Nas ɗin ta nuna mata banɗaki, ta kuma tsaya tana jiranta. A lokacin da Munaya ta fito ta sami Anti Zuwaira zaune a kusa da gadonta, fuska cike da annashuwa kamar babu abin da ya faru. Tsanarta da ƙyamarta suka haɗu suka mamaye zuciyar Munaya. Bata son kallonta saboda tsana,

“Ki sa a, sallameni na sami sauƙi.”

Ba tare da ta yi magana ba, ta tashi ta fice. Munaya tana ta kallon ɗakin nan, kuma ta yi alƙawarin in dai tana numfashi sai ta ga me ne ne a cikin ɗakin nan. Tana ganin, sun fice ta, tashi da sauri ta sake komawa da nufin ta shiga. Abin mamaki ƙofar gam! Ta tsinewa wannan Nas ɗin domin tana da tabbacin ita ta rufe wurin saboda basu shirya gaskiya ba.

Bayan an sallameta sun dawo gida, tana kwance a falo ta saƙa wannan ta kwance wancen. Sai yanzu ta tuna da tunda ta zo garin bata yi waya da Ummanta ba.

“Anti taimaka mini da wayarki in kira Umma.”

Anti Zuwaira ta ƙaraso ta zauna kusa da ita,

“Munaya ki kwantar da hankalinki dan girman Allah. Yau satinki biyu a kwance bakisan wa ke kanki ba. Umma ta damu da rashin jinki, dan na kasa gaya mata. Na ce mata kin koma hostel ne shiyasa, kuna gab da fara jarabawa. Na kira malamai akan matsalarki, an tabbatar mini aljani ne ya ke nuna maki wasu abubuwa na tashin hankali. Yanzu zan kira maki ita amma dan Allah ki saki jiki ku yi magana bana son su san da wata matsala a ɗagawa mutanen gida hankali.”

Munaya ta haɗiye yamu da ƙyar, tana mamakin har sati biyu ta yi a asibiti? Azzalumin likitan nan yana ɗura mata allurar barci. Dole ta haɗiye komai, ta saki fuska ta yi waya da Ummanta. Tana jin kamar ta gaya mata duk abubuwan da suke faruwa, amma babu hali, anti Zuwaira ta kafe ta tsare.


Kwana biyu lafiya lau, ta mance komai, sai soyayyar Zayyad da ke ɗawainiya da zuciyarta. Ta kuma ci burin insha Allahu hostel za ta koma. Yau ta tashi da son yin aikace-aikace, dan haka ta kirawo mai aikin Anti Zuwaira ta ce mata su kakkabe ko ina.
Suna aiki suna ɗan taɓa hira, har Munaya ta kai kan wata ƙofa. Duk yadda ta yi ta buɗe ƙofar ta kasa. Laure mai aiki ta ɗagowa daga abin da take yi ta zaro idanu tare da cewa,

“Ke! Ki rufa mana asiri. Anti Zuwaira ta gargaɗemu akan wannan ƙofar. Dan Allah ko da wasa kada ki sake zuwa wurin. Tun yallaɓai na farko yana raye ba a buɗe wurin. Shi kansa Yallaɓai Zayyad da ya matsa akan ƙofar sai wani lamari ya, so ya faru.”

Munaya ta dawo da baya tana dubanta,

“Kina aiki a gidan nan lokacin da Uncle Zayyad ya rasu?”

Ta ɗaga kai,

“Eh. Ta sallami dukka masu aikin sai ni kaɗai ta bari.”

Munaya ta matso daf da ita ta dafa kafaɗarta ta ce,

“Gaya min, ciwo ya yi? An ce a gidan nan ya rasu.”

Laure ta zaro idanu,

“In ji wani maƙaryacin ya ce a gidan nan ya rasu? Ba zan taɓa mance mafarin abun ba..”

“Ke Laure!”

Ta ji wata razananniyar muryar da ta gigitata. Ita kanta Munaya sai da ganinta ya ɗauke na wani lokaci. Daga bisani suka dubi in da akayi tsawar. Anti Zuwaira ce a tsaye ranta a matuƙar ɓace.

“Laure ashe ke mahaukaciya ce? In ce ki dafa mini taliya sai in zo in ga shinkafa?”

Ta rufeta da faɗa. Mamaki dukkansu ya kama su. Domin a gaban Munaya ta ce a dafa shinkafa. Dole Munaya ta bar wurin, ta nufi ɗakinta da nufin za ta biyota sai ta ji labarin nan.
Sai dai tun daga ranar bata sake sanya Laure a idanunta ba, sai tashi ta yi ta ga an kawo sabuwar mai aiki.
Muje zuwa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 3Na Kamu Da Kaunar Matacce 5 >>

1 thought on “Na Kamu Da Kaunar Matacce 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×