Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Na Sake Ta by Mustapha Abbas

Asabar 7:30 pm

Yanzu da nake zaune a ɗaya daga cikin kujerun alfarmar da suka yiwa katafaren falon saukar baƙin matashin ɗan kasuwa Usman One Boy ƙawanya ina raba idanun ta inda zan ga ɓullowarsa ƙarfe bakwai da rabi 7:30 dai-dai tafkeken agogon bangon da ke saƙale a jikin bangon yamma na falon ya nuna.

A hankali na kai duba na ga farantai guda biyu da ke gabana kan madaidaicin teburin gilashi, ɗaya shaƙe yake da kayan marmari, ɗayan kuwa soyayyen naman kaza ne, sai manyan kwalayen Juice har guda uku da kofunan glass. A ƙalla mintuna na biyu a zaune kuma tun shigowa ta ɗaya daga cikin hadiman gidan ya gabatar min da waɗannan kayan maqulashe bisa umarnin uban gidansa.

Na sauke ajiyar Zuciya a hankali tare da ɗauke kaina zuwa hanyar ƙafar bene lokaci guda da ƙamshin turaren Usman One Boy ya haɗe ko ina a falon, ya bayyana cikin shigar alfarma irin ta matasan attajiran da naira ke zigawa a lokacin su, ya tako har inda nake zaune ya bani hannu muka gaisa, kana ya samu guri shima ya zauna kujerar dake nesa da ni kaɗan yana kallo na.

“Kamal baka taɓa komai ba da aka kawo maka, ka saki jikinka fa.” Ya faɗa yana gyara zama.

Kaina a sunkuye na miƙa hannu na ɗauki kwalin lemo guda ɗaya na farke na tsiyaya a kofi, na fara kurɓa a hankali.

“Ashe ka samu saƙon kirana?” Ya tambaya.

“Eh, tun jiya ma, kasancewar babu mota a hannuna yasa ban samu ɓullowa ba sai yau.” Na amsa masa.

“Allah Sarki! To ya aikin naka?”

“Alhamdulillah! Muna nan muna lallaɓawa.” Na sake amsawa a karo na biyu.

A baya Usman ya yi min farin sani kasancewar duk tare muka taso a unguwa ɗaya tun ƙuruciya, bisa la’akari da yadda ya ke kama sunana kai tsaye yanzun ma bai manta ni ba duk da sauyin rayuwar da ya samu.

“Na kira ka nan ne domin ƙaruwa Kamal, da fatan ba za ka yiwa magana ta mummunar fahimta ba.” Ya faɗa bayan ya sauke ajiyar Zuciya.

“Babu damuwa Usman kai nake saurare.”

Ya numfasa a hankali, “Kamal wata buƙata ce da ni, ta wata fuskar kuma za mu iya kiran ta kasuwanci tsakanin ni da kai bisa yarda da amincewarka.” Ya saurara kaɗan tamkar yana jin nauyin furta abinda yake son faɗa sai kuma ya ci gaba bayan ya yi ƙasa da muryarsa.

“Babu batun ɓoye-ɓoye, bari in yi maka gwari-gwari Kamal, so nake ka saki matarka Hajir, zan baka Naira miliyan biyar, ina so zan aure ta.”

Lemon da na kurɓa ya dawo sakamakon sarƙewar maƙogwarona sannan kofin dake hannuna ya suɓuce ya faɗi kan rigata duk ta ɓaci da ruwan lemo.

*****

Litinin 8:00 pm

Na runtse idanuna na buɗe a hankali, burina in shafe ire-iren kalaman Usman daga kwanyata, duk a ƙoƙarina na zama jarumi wajen yiwa Hajir halaccin da zai ci gaba da kafa kyakkyawan tarihi a soyayyar da muka shafe sama da shekaru huɗu kafin ta kai mu ga aure, amma abin ya faskara, alal haƙiƙa na san hakan baya rasa nasaba da baƙin talaucin da ke bibiyar rayuwata kamar inuwa, in banda wannan babu wani dalili da zai sa kalaman Usman One Boy su samu wajen zama har su yi tasiri irin haka a cikin Zuciyata.

Muna masifar son junanmu ni da Hajir, ta yadda a cikin abubuwan da zan iya yi saboda kuɗi ban yi tsammanin akwai fansar da soyayyar ta ga wani ba, kamar yadda ita ma a rayuwar ‘yammatancinta ta tsallake attajirai irin su One Boy ta zaɓe ni ba don sisin kwabona ba, Abin na da matuƙar wuya in iya juya mata baya cikin sauƙi.

Tabbas ni mutum ne mai masifar son Kuɗi, dalilin kenan da yasa na kasa samun sukuni tun lokacin da Usman ya zo min da buƙatarsa. Wuni guda na share ina zagaye gari da tsohuwar motata ina ƙona fetur a banza, idanuna tuni sun daina kallon fasinjojin kan hanya, dama kuma ga yadda aikin Taxi ya zama a wannan lokacin sakamakon yawaitar baburin adai-daita sahu a faɗin jihar Kano, wanda ya zamo tamkar ɓullar annoba ga mu ‘yan Taxi. Ƙwaƙwalwata ta shiga ninƙayar neman mafita.

Da kyar na iya sarrafa tsohuwar mota ta zuwa bakin Chemist ɗin Mansur dai dai lokacin an fara kiran Sallar isha’i. Mansur yana zaune kan benci yana alwala ya bi ni da ido na san yana mamakin yadda na fita hayyacina cikin kwanaki biyu da ganawa ta da One Boy, yau ma rabona da abinci tun safe.

“Kana da ƙawa zuci sosai Kamal, ya kamata ka yiwa kanka zaɓi guda ɗaya ka huta da wannan tunane-tunanen wofin.” Ya faɗa yana kallon fuskata lokacin da nake ƙoƙarin zama kusa da shi, ban ce masa komai ba na ja butar da ya turo min na fara alwala.

Mansur ne ya ja mu muka yi Sallar magariba a ƙofar chemist ɗin sa. Bayan mun idar ko fatiha bamu shafa ba na dube shi, “Mansur ka san ina son Hajir ko?”

“Na san kana son Hajir kuma kana masifar son kuɗi Kamal, ba zan iya zaɓa maka ɗaya cikin biyun nan ba, kawai ka yi abinda ya dace, kai fa ba ƙaramin yaro bane ko?” Ya faɗa cikin kallo na.

Mansur abokina ne tun yarinta, bana iya ɓoye masa komai, duk da bai shawarce ni kan zaɓen Hajir ko miliyan biyar ɗin Usman One Boy ba, amma ina iya gane inda hankalinsa ya karkata, Mansur ya dame ni ya shanye wajen son kuɗi, babu abinda ba zai iya yi kan kuɗi ba.

Har misalin ƙarfe 9:30 na dare muna tattauna dabarun kasuwanci da yadda ake juya kuɗi ni da Mansur, wannan ya ƙara saita min hanyar da ba ni da tabbacin za ta ɓulle da ni zuwa Duniyar da nake shirin jefa kaina, muka yi sallama da Mansur na kama hanyar gida ina ta saƙe-saƙe.

*****

Ƙarfe 9:26 am

Ina tsaye a bakin ƙofar ɗakinmu riƙe da labule, Hajir na daga ciki kan gaɗo ta zuba min ido fuskarta cike da damuwar ganin yanayina a cikin ‘yan kwanakin nan, ta rasa gane kaina ko abinda yake damuna.

“Ni fa matarka ce kana da damar tattauna matsalolinka da ni, me yasa kake ba ni haƙuri bayan a iyakar sanina baka yi min laifin komai ba Kamal?” Duk yadda take so mu haɗa ido na ƙi yarda, ta marairaice kamar za ta yi kuka.

“Ka ga, ni idan ma baka da kuɗin da zaka bani in yi cefane ne kawai ka yi tafiyarka zan san yadda zanyi.”

“No ba haka ba ne Hajir.” Na faɗa muryata a sarƙe. Ta ɗan yi dum, har yanzu tana kallo na.

“To ka ga, idan ma wani laifin ka yi min a ɓoye ka kasa faɗa min wallahi na yafe maka, bana son wannan fuskar damuwar, ka je Allah Ya tsare!”

Hawaye suka kufce a idona, irin waɗannan kyawawan ɗabi’u na Hajir su na wuni na kwana ina kwatanta ta yadda zan iya rayuwa ba tare da su ba.

Hankalinta ya ƙara tashi ganin yanayin da na sake afkawa, kawo yanzu kuma Hajir ta tabbatar ba da wasa na zo mata ba.

“Hajir ki yi haƙuri lokacin rabuwar mu ya yi.”

“Dakata Kamal! Me kake nufi, me kake son faɗa, meye zai raba mu? Wallahi ban gan shi ba.” Ta faɗa hankalinta tashe. Saura kaɗan in fito da takardar sakin in yayyaga a wajen, amma kuma na riga na yanke hukunci na ƙarshe.

Sai da na tattaro dukkan jarumtata kafin na iya miƙawa Hajir mummunan saƙon da na shafe tsawon dare ina tunanin ta yadda zan fara rubuta shi kamar baƙon marubuci a fagen rubuta ƙagaggen labari.

Ba zan iya kwatanta irin tashin hankalin da Hajir ta shiga ba lokacin da ta gama karanta dogon rubutun da na yi a cikin takardar, don ina miƙa mata na fice daga gidan ina kukan zuci, abinda kawai zan iya tunawa shine Hajir ta wuni ta kwana cur tana kukan da ba ya buƙatar rarrashi har wayewar garin da ta kama hanyar unguwarsu.

Duk yadda manyanmu suka so jin musabbabin sakin abin ya faskara, dama Hajir ce mai faɗa kuma na roƙi alfarmar rufin asirinta a cikin takardar. Ta kuma rufa min, amma ban faɗa mata ina son ta auri Alh. Lado ba, na dai ce idan ta samu Miji ta yi aure, kuma amsa ɗaya kawai nake iya bawa duk wanda ya tambaye ni dalilin rabuwar mu, ‘Babu komai’

Wannan ya sa aka riƙa zargin ko wani mummunan laifin Hajir ta aikata da ba ya buƙatar a faɗa, ko ma dai mene ne ni dai na rabu da Hajir ba don bana sonta ba sai don tsananin soyayya ta da Kuɗi, na yi imanin da mahaifiyata na raye da wuya ta bari in tozarta Hajir saboda yadda take ƙaunarta da tausayinta kasancewar ta Marainiya.

TA FARU TA ƘARE

Wannan karon a Office na samu Usman.

“Kai nake saurare Kamal.” Ya faɗa bayan ya ajiye wayar da ya gama amsawa

“Dama na NA SAKE TA tun jiya, shine na zo in faɗa maka.” Na faxa kaina a sunkuye.

Usman ya saki gajeren murmushi tare da gyara zama sosai yana fuskanta ta ya ce, “Na yi tsammanin haka daga gare ka Kamal, domin tun sani na da kai kai wayayyen mutum ne, don haka ban yi tsammanin za ka yi wasa da damar zama miloniya ba, ba ni lambar akawun ɗinka, ina maka fatan samun macen da ta fi Hajir.”

Ina fara karanto masa lambar, yana sakawa a lokaci guda kuma ina tunanin wace irin mace ce yake min fata da ta fi Hajir ɗina?

Ban tashi daga wajen ba sai ga saƙo ya shigo cikin wayata, ya umarce ni na duba, na fiddo wayar ina dubawa sai ga naira miliyan biyar a account ɗin da ba a taɓa saka masa ko dubu biyar ba.

*****

SAUYI

Watannin da suka biyo baya na yi su cike da kewar rayuwar da muka yi da Hajir, duk da wannan ban bari mun sake haɗuwa da ita ba har lokacin da na samu labarin aurenta da Usman One Boy, ba zan iya kwatanta yadda na ji ba duk da a lokacin ina fafutukar zama attajiri, na tsunduma harkar magani da taimakon Mansur da ya haɗa ni da wani abokinsa a kasuwar ‘yan magani ta sabon gari, sana’a ce mai tarin samun da ban taɓa zato ba. Cikin ƙanƙanin lokaci na kai matakin da ake lissafa ni cikin abokanmu masu hali.

Na yi aure duk ta hanyar Mansur, auren soyayya ne amma ba kamar son da nake wa Hajir ba. Zama na da Kubrah bai yi nisa ba na gano wasu halayenta da ba lallai in iya jurar zama da su ba, ko da yake dama banyi tsammanin samun farin ciki kamar a auren farko ba. Mun rabu da Kubrah baram-baram saboda kama ta da satar kuɗaɗena da na yi imanin kaso chasa’in cikin ɗari Malamai da bokayenta take gyarawa tukunyar miyar gidajensu da su (Kuɗin).

Bayan Kubrah na auri Husna, ɗiyar wani attajiri cikin abokan kasuwancinmu, Husnah bata son aikin gida dai-dai da ƙwayar zarra. Duk da na tara mata ‘yan aiki a gidan ban tsira ba, sai da ta ƙarar da haƙurina da lalacinta. Daga ƙarshe muka rabu bayan tafka rigimar da ta kaimu har kotu da Iyayenta.

Daga wannan lokacin na ƙarasa yanke tsammani da samun macen da za ta yi dai dai da rayuwata.

Matata ta uku ita ce Maryam. Tun kafin muyi aure na fara samun matsala da ita, domin kuwa da ƙyar na raba ta da tarin samari da abokanta, na so ta sosai, wannan dalilin ne ma yasa na riƙa mata uzuri kan laifukanta, ta yi nisa a karatun da take na Lawyer, don haka na barta ta ci gaba har da alƙawarin aiki.

Har yau ina jin babu namijin da zai juri halin cuɗanya da maza irin yadda na jura game da Maryam, idan na yi magana sai ta ce abokanta ne, ta waye sosai. Abin takaici rana tsaka ta hura wutar sai na sake ta wai ina tauye mata ‘yanci. Haka na sake ta ba don ina son rabuwa da ita ba.

Habiba ce zama na da ita ya yi ƙarko, don mun shafe sama da shekaru uku tare, har na fara tunanin lissafin ƙidayar aure-aure na ya zo ƙarshe, duk da Allah Ya yi ta da shegen yawo, da wuya in dawo kasuwa in iske ta a gida, ga yawan ƙawaye, amma wannan duk bai dame ni ba, tunda tana bakin ƙoƙari wajen sauke min haƙƙoƙin aurena da ke kanta.

Katsam! ɗaya siffarta ta bayyana, tabbas halin Habiba ya fi na sauran muni, domin ban taɓa tunanin zan auri matar da take maɗigo ba. Har asibiti na kwanta saboda kaɗuwa, ɗimuwa da tashin hankalin abinda idanuna suka gane min.

Daga ƙarshe na tafi yajin aikin aure. Na gane babu abinda ya kai matar kwarai irin Hajir wuyar samu a wannan zamanin, kuɗi ba sa iya samar da ita, kai yanzu na gane ma ba komai kuɗi ke iya saye ba.

*****

NADAMA

Kawo yanzu da ƙidayar aure na ya cike bakwai cif ni kaɗai nake zaune a katafaren gidana, babu mata babu ɗa bare jika, kullum ina mafarkin samun Mace kamar Hajir wacce za ta kawo ƙarshen aure-aurena, in son samu ne ma Hajir ta dawo gare ni, amma kuma ta riga ta yi min nisa.

Ala tilas na sayar da gidana da ke Unguwar ‘Yan Kaba na tashi na koma New Side saboda yadda surutan jama’ar unguwar a kaina yake ɓata min rai, har an liƙa min lambar AURI SAKI.

Ban taɓa mamakin yadda tarihina ya sauya cikin ƙanƙanin lokaci ba, gashi dai ban rasa komai ba, a ɓangaren kuɗi zan iya cewa yawancin burikana sun cika, amma dangane da farin cikin rayuwa na rasa kuma na faɗi, ƙunci da rashin walwala suka zama abokaina don sun addabi Duniyata, na gane matsayin kuɗi daban matsayin farin ciki ma daban.

Wataran sai in ji ina ma a ce Usman zai yarda in ba shi dukkan abinda na mallaka ya saki Hajir in aure ta mu koma rayuwarmu ta baya.

Wataran kuma Zuciyata ta ayyana min in nemo Hajir duk inda take in roƙi yafiyarta ko da ba za ta dawo gare ni ba.

Wata wataran ɗin kuma sai dai hawaye su yi ta zubowa daga idanuna suna bin kumatuna kamar ƙaramin yaro. Wataƙila wannan shine hukuncina.

Ƙarshe

Mustapha Abbas R/Lemo

1 thought on “Na Sake Ta”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×