Skip to content
Part 26 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

Na Yarda Da Ke

Kin zamo burina

Hasken idanuna

Fitilar da ke raina

Sannan muradina

Idan ba ke na fa san

To babu ni

In kika barni a yanzu

Zan yi macewa.

*****

Na yarda da ke

Na yarda da ke

*****

Jira na zo masoyiya

Tsaya ki ji Sarauniya

Kin zamo ruwan sanyi

Da ke ta bin zuciya

Ke ce muradina

Amsar du’a’ina

Ni ke nake ƙauna

Don Allah zo guna

Idanuna ke suke yin marmari

In kika barni a yanzu

Zan yi macewa

*****

Na yarda da ke

Na yarda da ke

*****

Zan sha guba

Don na mace

Tsaya gani

Zana mace

Tunda babu ke fa

Ai gara ma kawai in mace

Allah nake roƙo

Gani da ɗan ƙoƙo

Ka cikan muradina

Kan Sahibar raina

Idan ba ke na fa san

To babu ni

In kika barni a yanzu

Zan yi macewa

*****

Na yarda da ke

Na yarda da ke

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fasaha Haimaniyya 25Fasaha Haimaniyya 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×