Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Nacina Ya Jawo Mini by Aisha Abubakar

Zaune suke ɗaliban shiru a aji kasancewar malamin Maths ne kuma gashi mugu, hakan yasa ɗaliban maida hankulansu gaba ɗaya gun allon,calculations yake yana bayani amma babu mai ganewa, yana kai karshe yace “Do you all understand” ɗaliban suka ce “yes” saboda tsoransa da suke yi.

Uncle Musa ya ce “Good, now let me give class work “.

Nan fa ɗaliban suka ruɗe,Uncle Musa ya rubuta calculations guda biyu a board, sannan yace su fara.

Kwatsam sai ga wata  yarinya wacca bata wuce shekara 15 a duniya tashigo da gudu tana haki, saboda gudun da tasha, kawai ɗaliban sukeyi Uncle Musa yace,” Stop there!!!”, cike da tsawa, haka yarinya ta tsaya jikinta na bari, kafafunta suna rawa.

Uncle Musa ya ce” why are you late in my class”. 

Cikin rawar murya yarinyar tace “I’m sorry Sir”. Kawai sai tafashe da kuka, suko ɗalibai daɗi suke taji, harda dariya ƙasa ƙasa kar malamin yaji su,Uncle Musa ya ce “kneel down and give me your hand, next time you won’t come late to my class”.

Haka yarinyar ta mik’a hannunta tana kuka, yako zane ta babu sassauci, tashi tayi daga kneel down d’in tawuce seat d’inta wanda yake gaba ta zauna, kuma ya ce saita yi class work d’in.


Baiwar ALLAH haka ta ciro littafinta tafara rubutu, cikin wasu mintuna sai gata tagama class work d’in take yin submitting, cike da mamaki Uncle Musa ya bita da kallo, ɗaliban ma sai haushinta suke yi saboda tafisu nacin karatu da hazaƙa, haka ɗaliban suka kasance har lokacin tashi break yayi suka fita.

Bayan sun fita suna wasa naji ance Sa’eeda, ashe yarinyar nan ce wacca Uncle Musa ya duka ce, waiwayo tayi tana kalonta ta ce “Maryam ya aka yi ne”  wacce aka kira da Maryam ta ce “Sa’eeda me yasa kika yi latti, bayan kinsan yau Uncle Musa muke dashi”.

Cike da damuwa Sa’eeda ta ce “hmmmm Umma Kande ce ta aikeni kuma wurin da nisa, shiyasa nayi latti”.

Maryam tana kallonta ta ce “Amma tasan za ki makaranta ai, shi ne ta aike ki alhalin tana da mayyan Yara ‘yan mata “,  murmushi mai ciwo Sa’eeda tayi sannan tace” Ba komai ai lokaci ne, watarana sai labari “.


Haka suka cigaba da hiransu har aka koma aji, darussa  aka cigaba dayi har 2:00pm tayi aka tashi.

*****

A nutse suke tafiya ita da Maryam  suna hiransu, har kowa yabi hanyar gidansu. Tana shanyo kwanar gidansu gabanta ya fara dukan uku uku saboda tasan aikin gida na jiranta, hakan ta isa har zauran gidansu tana ɗauke da sallama, amma babu amsa duk da akwai mutane a gidan, shiga tayi ɗakin mahaifiyarta tare da sallama, cike da so da ƙaunar ƴarta tilo ta amsa tana fara’a, gaisheta tayi sannan ta ajiye jakarta.


Zama ta yi tana” Washhhhhh ALLAH na”, Ummanta dake linke wankin kayan mutanen da tayi ta ce “ALLAH yasa dai ba’a miki dukan latti ba”.

Marairaice fuska ta yi kamar zata yi kuka sannan ta ce “ALLAH Umma sai da Uncle Musa ya dukeni hada Ni da kneel down”, cike da tausayin ƴarta ta ta ce “Karki damu ƴar albarkha watarana sai labari kin ji, ki cigaba da haƙuri, in shaa ALLAH baza mu dawwama a haka ba, Ubangiji zai taimake mu”.

Sa’eeda ta ce “Umma bara na yi sallah sai inje inyi aikina” da kallo tabi ƴarta dashi tana tausayin halin da suke ciki.
Tuno kyara da tsangwamar da suke fuskanta ita da ƴarta wurin kishiyarta da mijinta yasa ta zubar da hawaye.

Fitowar Sa’eeda daga d’aki ke da wuya taji Umma Kande na kwalla mata kira har da ɗura mata ashariya  da cewa “Ubanwa kika ajiye da zai miki aikin gidan” a daburce Sa’eeda ta ce “Uhm… Uhmm sallah dama nake so nayi sai na fito  aikin “.

Tsaki mai karfi taja tana ce wa” Aikin banza, Ke ga ustaziya koh, maza kiyi sallar na baki minti 10 ki zo ki yi aikin “. A tsorace ta ce” to”.

Haka taje tayi sallah Ummanta na kallonta cike da tausayi ko abinci bata ci ba, taje ta gama aikin Kafin ta dawo dakinsu ta ci abinci.

*****

Wurin karfe 4:00pm na yamma ta shirya zuwa islamiya wacce take bayan layin su, tana tafiya tana karatunta cikin murya mai zaqi ga ƙira’ah ai daɗin gaske, har ta isa makarantar.

Faslul Imam Shafi’i naga  ta shiga wato ajin ƴan sauka, zama ta yi a bencin farko, duk da akwai ɗalibai amma basu da yawa, saboda yanxu ake shigowa, jakarta ta bude ta fito da Hadisi tana dubawa, a haka aka cika ajin har malaminsu ya shigo tare da sallama, duka ɗaliban suka amsa, sannan ya zauna yana fuskantar ƴan aji.

Malam Yusuf ya ce “Alhamdulillah tunda kun sauke har sau biyar, kuma wasunku ma sun kammala haddar alqur’ani mai girma, toh don haka time table na jarabawan sauka zai fito gobe, ku shirya sosai, sannan zamu fara karatuttukan sauka cikin satin nan”.

Farin ciki ne ya mamaye ƴan ajin banda Sa’eeda wacca tasan basu da halin biyan kuɗin saukar duk tafi kowa hazaƙa a ajin gaba daya.

Malam Yusuf ya katse musu surutu da cewa”sannan ku fada wa iyayenku maganar kuɗin sauka akan an yanke naira dubu ashirin ga kowani ɗalibi “.

Haka ya bar ajin, su kuma sai murna suke yi banda Sa’eeda wacca ko ƙawa bata da ita a ajin sede a boko, haka suka fara maraji’ah har lokacin tashi yayi aka tashe su, suna fitowa Sa’eeda ta nufi office ɗin shugaban makarantar su, don ita gaskiya ta fasa saukar don Ummanta ba tada halin biyan kudin saukar, gashi mahaifinta yana dashi babu laifi yana noma amma bazai biya mata ba, koda ma yayi niyyar biya, kishiyar Ummanta zata hana saboda taga yaranta basa karatu sai talla, da wannan labarin zucin ta shiga office ɗin shugaban makarantar da sallama.
Malam Harun ya amsa cike da fara’ah ya ce “Sa’eeda ke ce haka “.

Tana murmushi ta ce” Eh malam, daman nazo ne wurinka”.

Sai ya ce “To to ina jinki Sa’eeda”. Sai data lumfasa kafin ta ce “Malam dama ga me da maganar saukan mune, shine nazo in cema ko za’a iya cireni daga cikin ƴan sauka, saboda gaskiya iyaye na basu da halin biyamin kuɗin sauka, shine nace ko za’a cireni”.

Shiru yayi yana kallonta tare da yin nazari, don gaskiya yasan basu da halin biya hasalima a scholarship Sa’eeda take tun daga aji daya har zuwa a jin shiga saboda hazaƙar ta, haƙiƙa bai dace ya dakatar da Sa’eeda ba kodan ƙoƙarinta da natsuwarta.
Kawai yace”Sa’eeda “, cikin taushin murya ya ƙara da cewa” Naji bayanan ki, kuma na fahimta, in shaa ALLAH hukumar makaranta zata duba don baza muji daɗi ace mai hazak’ar aji batayi sauka ba saboda rashin kuɗin sauka ba, ki kwanatar da hankalinki in shaa ALLAH, ALLAH zai rufa asiri”.

Haka suka yi sallama cike da farin ciki tawuce gida.

*****

Isar ta gida ke da wuya aka fara Kiran sallah, jakarta ta ajiye taje alwala Sannan tayi sallah, sai taci abincin dare kana  ta dauko assignment ɗinta na makaranta tayi, sai tayi karatun littattafanta na boko da islamiya, sannan ta sanar ma Ummanta yanda suka yi batun sauka da shuganban makarantar su, cike da farin ciki ta ke jin ƴarta tana bata bayanin yanda sukayi da shuganban makarantar su.

Sa’eeda na kammala bayininta sai mahaifiyarta ta ce “ALLAH kaine abin Godiya, ka ƙara rufa mana asiri duniya da lahira”. Ameen Sa’eeda ta bita dashi.

Washegari ta tashi da wuri kasancewar tasan aiyukanta na gida, ta soma yi don tsoron yin latti a zaneta, haka ta kammala tayi shirin ta tsaf, sannan ta karya, ɗaukar jakarta tayi ta fito tsakar gida tana shirin wucewa taji an ƙwalla mata kira, a tsorace ta waiwayo sannan ta amsa saboda jin wacca tai mata Kiran, “Ke dan uwarki zo nan”.

Kanta aƙasa ta nufo inda take, kafin ta ƙaraso wurin taji an hankaɗeta, ji kayi timmmmm a ƙasa gashi gidan nasu ko siminti babu, haka uniform ɗinta yayi buju buju da shi, a raunane ta ɗago idanunta cike da ƙwalla tana kallon budurwar wacce ta riƙe ƙugu tana girgiza kai alamun masifa.

Sa’eeda da ƙyar ta iya miƙewa tace mata “Haba Nusaiba, mai na miki kika tureni alhalin akwai filin da zaki iya wucewa ba tare da kin taba ni ba”, tana magana hawaye na zuba a idanunta, ita ko wacca aka kira da Nusaiba mai zata yi inba shekewa da wata bazawarar dariya ba tana tafiya tana girgiza jiki kamar wata karuwa.

Buɗan bakin Nusaiba ta ce ” Hmm Sa’eeda ke nan, to ke a tunaninki zan bi wata hanyar don ina jin tsoranki, to wallahi kinyi kaɗan, Ke ba ma keba hatta wannan Uwartaki bata isa ba, eheh, irin wai ita Allazi boko, ana dai yawan ta zubar ne kawai aka ɓige da boko!!!”.

Duk wannan abinda yake faruwa a idanun ƴan gida banda mahaifiyar Sa’eeda da dake ɗaki tana jinsu, saide tayi murmushi da girgiza kai alamar ALLAH ya kyauta.

Sa’eeda ba mai hayaniya bace, haƙuri ta bata ta wuce wurin Umma kande,a ƙasƙance ta ke duban Sa’eeda, tace “Jeki wurin Maman Dije Kice nace tabani saƙon”, da,  “to” tabita dashi ta wuce don tasan idan tayi musumma ɓata lokacinta zatayi gashi gidan Maman Dije akwai ɗan nisa kaɗan.

Haka tawuce tana sassarfa ta amso saƙon ta kawo mata ba tare da ta shiga ɗakinsu ba ta wuce school.

*****

A class kuwa, principal na gani ya shigo Jss3, ashe ajinsu Sa’eeda ne, a tare ƴan aji suka miƙe suna gaisheshi, ya amsa musu cike da kulawa kana ya ce cikin harshen turanci “dan gane da Junior waec ɗinku, kowanne a cikinku zai biya #2500 sannan za’a zana exams ɗin 3rd na watan da zai shigo, don haka kowa ya maida hankalin sa sosai a karatu banda wasa”. Principal ya ɗau tsawan lokaci yana jawabi kana ya fita daga ajin.

Ɗalibai sai murna suke yi sun kusa zama seniors, haka darussa sukaita wakana har lokacin tashi yayi suka wuce gida .

BRIGHT STARS INTERNATIONAL SCHOOL shi ne sunan makarantar su Sa’eeda, makaranta ce mai kyau da tsari, ga koyarwa sosai, babbace don tana da field ɗin football da handball duk a ciki, tana ɗaya daga cikin makarantun da ake ji dasu a garin.

Kasancewa Sa’eeda ƴar talakawa ce kuma acikin wannan makaranta ya samo asaline a dalilin wani malamin primary dinsu wato Uncle Saleem wanda yake koyarwa a matsayin corper a government school ɗinsu, ganin Sa’eeda da ƙoƙari yayi cuku cuku har  ALLAH ya ƙaddara tasamu scholarship.

Bayan dawowarta makaranta ta sanar ma Ummanta batun Junior waec.

“lallai akwai karatu gabanki Sa’eeda, ga shima islamiya kun kusa fara exams” cewar Umma.

Murmushi Sa’eeda tayi tana fadin”Ai Umma yanxu zan fara karatu in shaa ALLAH “.

Umma ta murmusa da faɗin” ALLAH ya miki Albarkha, ya cigaba da tsare gabanki da bayanki” “ALLAH humma Aameen Ummina”.

Haka dai Sa’eeda ta cigaba da zuwa islamiya da boko, ga kuma karatun da tasa kanta tana yi, ba kama hannun yaro, a wannan week ɗin time table ɗin exams ɗinsu na boko da islamiya ya fito, aka fara shirye shiryen exams.
Alhamdulillah sun gama exams ɗin islamiya sannan sukayi na boko wanda ya ɗaukesu har tsawan wata daya.

KEBBI

“Mum, don ALLAH ki roƙa min Abba ya janye tafiyana UK karatu, duka abokaina Federal University, Birnin KEBBI suka yi applying , amma ace ni sai k’asar waje”. A shagwabe yake magana kamar zai yi kuka.

Mum ta ce ” Haba Sadam, sai Ka ce yaro, bayan kasan k’a’idar gidannan, duka y’an uwanka acan Oxford University suka yi, sai akanka kake so a canja tsari, haƙuri kawai zaka yi ka tafi, kar Dad ɗinka ya ɓata ma rai”.

Kamar zai yi kuka ya ce, “shikenan Mum”, Murmushi mum tayi sannan tace, “Yauwa Autana, kaga tafiyarka jibi ne sai ka fara yin shiri”,  “Allah ya kai mu”, kawai Sadam ya iya cewa.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×