(Labarin Da Ya Yi Na Daya A Gasar Bakandamiya)
"Ki tafi gidanku na sake ki!"
Runtse idanu na yi jin sautin muryar Adamu a kaina, yana furta kalaman da suka kusan sanya ni haihuwar cikin da ke jikina. Da sauri na dago jajayen idanuwana da suka gajiya da kuka na sauke a saitin sa.
Wani irin tashin hankali da ciwon rai suka dirar mani, ji nake kamar na daura hannu a kai na kurma ihu ko zan samu raguwar tashin hankalin da nake ciki, amma ina, ba na tunanin hakan zai. . .