ALIYU HAIDAR POV
*****
Tsaye yake a gaban side na mirror da ke a hamshaƙin ɗakin nashi, sanye yake da ƙananun kaya, tsadaddun riga da wando, ya kammala shirinsa ya gyara kwantaccen baƙin gashin kan shi, wani gawurtaccen ƙamshi kawai ke tashi a jikinshi.
Riƙe yake da p-cap nashi yana ƙoƙarin maƙala agogonsa a hannunshi, yana kammmala maƙala agogon, ya sanya hannunshi guda ya gyara kwanciyar gashin kanshi, sai da ya kalli kan shi da kyau, sannan ya juya, hannunshi guda riƙe da p-cap nashi, ɗaya kuma riƙe da wayarshi, cikin takun ƙasaita da izza da aji ya fice. . .