Ringing guda layin da Hajiya ta aika wa ƙira yayi aka ɗauka, "Assalamu alaikum."
"Wa'alaikissalam Hajiya barka, ya kuke? Ya shirye-shirye?", aka faɗa a ɗaya ɓangaren.
"Alhamdulillah Nadiya, yaushe kayakin nan za su iso? Alhaji ya ce a satin nan yake son a kai lefe, fatan kin yi yadda na ce?"
"Nayi Hajiya, kuma in sha Allah nima zuwa jibi ina Nigeria", faɗin Nadiya a ɗaya ɓangaren.
Hajiya ta ce, "To Allah Ya kai mu, Allah Ya kawo ki lafiya."
Sai da suka yi magana akan abinda ya shafi business nasu, sannan suka yi sallama, daga haka Hajiya. . .
