Sadeeq ko da ya ji tayi shiru, kuma yana iya jiyo sautin numfashinta alaman ba wai ƙiran ya katse bane, sai ya busar da iska mai ɗumi a bakinshi, gani yake kamar laifi ya mata tayi shiru, may be ta fara fahimtan zai rusa mata farin cikinta ne, ko may be yanda yayi magana ya mata ba daɗi, sassauta muryarshi ya yi sosai yayi ƙasa sosai, kamar mai raɗa ya ce, "Fatan kina lafiya?"
Maganar Sadeeq shi ya dawo da Sadiya hayyacinta daga duniyar shauƙin yadda ya ƙira sunanta, murmushi ne ya yalwata sosai a fiskarta duk da yana ɗauke. . .
