Husna kanta a ƙasa ta shigo ɗakin, bakinta ɗauke da sallama cikin siririyar muryarta, amma ƙirjinta banda bugu ba abinda yake yi, hakan ya sanya ta tsaya a tsakiyar ɗakin tare da ƙara sunne kanta ƙasa ta kasa ƙarasawa inda yake.
Haidar da tunda ya jiyo sautin sallaman ya gane ba Nihal ba ce, ran shi idan ya kai dubu to ya ɓaci, duk da ya san wannan ba zai wuce aikin Hajiya da ke son cusa mishi Husna a lamuranshi ba, amma ita ma mahaukaciyar yarinyar da nata, idan ba hauka ba mai zai sa ta ke kutsa kanta. . .
