Ɗaki Sadiya ta koma ta sako zumbulelen babban hijabinta, ko da ta dawo palourn samun Mama tayi ita ma da nata hijabin, gaba Mama tayi Sadiya ta bi ta a baya, kulle madaidaicin gidan nasu suka yi, sannan suka taka har ƙofan wani tangamemen katafaren gidan da ke manne da gidansu, bakin shirgegen gate na gidan wanda ya ci kuɗi suka tsaya, Sadiya ce ta yi knocking, mai gadi daga ciki ya ce, "Waye?".
Sadiya da siririyar muryanta mai ɗauke da damuwa ta ce, "Sadiya ce."
Da sauri mai gadin ya buɗe ƙofan yana musu sannu tare da basu haƙuri. . .