Yana miƙewa ya juyo tare da nufo ƙofan da zai sada shi da closet nashi.
Haɗaɗɗen gaye ne maƙura wanda kana ganinsa ka san kuɗi da jin daɗi sun samu ɗaurin wajan zama a tattare da shi, tsayinsa dai-dai haka ma jikinsa dai-dai, gashin kansa da ya tara a kwance suke a gyare sun sha askin matasa masu ji da kuɗi da aji da kyau, banda sheki da ƙamshi ba abinda gashin kan nasa ke yi, ga wani saje mai style da gashi dai-dai ɓakiƙƙirin, har zuwa gemunsa da gashin yake dai-dai ba za a ce. . .