Sai goshin magrib sannan Sadiya suka kuma waya da Haidar ya shaida mata yana hanya, hakan ya sanya ta sanar da Umma, sannan ta shirya cikin riga da skirt na leshi ruwan ɗorawa(yellow), ba ƙaramar karɓan kalar fatarta yayi ba, saboda ita Sadiya ba za a sanyata a layin farare tass ba, haka kuma ba za a sanya ta a jerin masu duhun fata ba ko da kuwa chocolate color ne, fatarta bai da duhu tana da haskenta dai-dai, amma ba fayau ba.
Sadiya kyakkyawar matashiya ce mai kimanin shekaru goma sha takwas da haihuwa, ƙiranta ƙira ne. . .