Kwana ɗaya, kwana biyu... Har aka ci kwanaki shida masu kyau, Sadeeq na a kwance maƙale da oxygen, ba abinda ya sauya kuma ba wani ci-gaba da aka samu, duk da kuwa likitoci na matuƙar ƙoƙarinsu, wajan kula da shi da ba shi duk wata taimako da ta kamata, kuma Umar na nan a tare da shi a ko da yaushe, sai Abba sun zo da dare sannan yake tafiya gida ya je yayi wanka yayi uzurinsa ya dawo, su kuma sai su tafi, dan shi yake kwana da Sadeeq ɗin, watarana Sa'ad ya taya shi, watarana kuma. . .