Barhana da sarki Zawatundma ya aika zuwa garin Mubanuwa kuwa da sauri ta fara keta hazo har ta isa garin Mubanuwa inda wani mahaukacin iska mai matuƙar ƙarfi ya fara girgiza manyan duwatsun dake cikin garin. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci duwatsun suka fara tsagewa, garin ya rikiɗe, sai iska da ke ta kaɗa abubuwa, yana kwasar kayansu zuwa sama.
Take ƴan garin suka fara gudu suna neman mafaka, musamman da labari ya zo musu cewa babban dutsin garin wanda wani bai taɓa hawa ba saboda yadda suke girmama dutsin, akasari ma wasu daga cikin ƴan. . .