Skip to content
Part 11 of 25 in the Series Nawa Bangaren by Queen-Nasmah

Cak ko ina na garin Zawatu ya tsaya, haske ya bayyana ko ina alamar gimbiya Naheela ta dawo hayyacinta.

Sarki Zawatunduma da Naheela kuwa ɓacewa suka yi ɓata . Sai gaban Teku . Wani tsalle suka yi a tare suka shige cikin ruwan .

Garin Mubanuwa kuwa babu wanda ke motsi ,ruwan duwatsun da aka yi sun yi musu muguwar illa ,wasu da yawa lokacin girgiza ƙasa sun faɗa cikin ƙasa .

Ko ina labarin garin Mubanuwa ake yi domin kuwa cikin ɗan ƙanƙanin lokacin labari ya zagaye ko ina .

*****

Bayan wasu kwanaki .

Yau ake taron sunan ƙaramin Sadauki .inda aka yanzu mishi ɗaya daga cikin shanun da suke kiwo da kuma rago ɗaya , dama Bobbo duk aka mishi haihuwa cikin dabbobin da yake kiwo ake ɗiba . Bobbo mutum ne da Allah yayiwa arzikin kiwo , yana da garken dabbobi sun fi a ƙirga , duk garke ɗaya ba za ka iya gane yawansu ,dan ko shi da yake kiwon bai san iya adadinsu ba .iya abinda kawai ya sani rago guda ɗaya ya siye amma da shi yayi arzikin da ya tara duk waɗannan dabbobin .

Mutane sai shiga suke yi gidan taron suna . Duk wanda ya shigo sai ya fita yana gulmar Mairo ,dan duk baƙon da ya shigo bata bashi ko ruwa ba ,ko wanka Mairo bata yi ba ,ga Sadauki sai kuka yake yi kamar ranshi zai fita ta ƙi da ɗaukarshi .

“Ke ko Mairo ki ɗauki yaron nan ki bashi nono ya sha mana” wata Tsohuwa ta faɗa ,wadda bata wani daɗe da shigowa ba. Kallon tsohuwar Mairo tayi a kaikaice ta ce “ai ki ɗauke shi ki bashi nonon ban hana ki ba “.

“A’a aha ,raba ni da yari bani auren sarki ,gani nayi yaron sai kuka yake yi ” tsohuwar ta faɗa.

Mamma ta shigo cikin ɗakin jin kukan Sadauki ya ƙi ci ya ƙi canyewa .

“Miƙo min shi nan tun da bata da imani “Mamma ta faɗa .

Wata yarinya dake zaune gefen katifa ta miƙa hannu ta ɗauki Sadauki ,sannan ta miƙa ma Mamma shi .

Mairo ta kalli Ƴan ɗakin ta ce “ku fitar min daga ɗaki ga yaron can an fita da shi “.

Tashi suka yi suka fita
Mairo ta ci gaba da bambami “ba wanda aka gayyata amma da yake harkar ci ce duk kun zo. “

Ba su kula ta ba suka fita suka bar ɗakin.

“NAWA ƁANGAREN ” Bobbo ya ji ana faɗi da ƙarfi duk muryar ta karaɗe jejin .

Da sauri ya juya dan jin daga ina sautin yake amma bai ga kowa ba .

Ta ɓangaren hagu ya ƙara jiyo sautin “Nawa ɓangaren ,Nawa ɓangaren ,Nawa ɓangarennnnnn !!!!!!!” da sauri ya juya ta ɓangaren hagu amma bai ga mai maganar ba .

Miƙewa tayi daga Saman kujerar da yake zauns . Take ya fara jin jiri ,da sauri ya dafe kanshi yana jin duniya na mishi yawo , gami da jin ana mai-maita abu ɗau .“NAWA ƁANGAREN “. Dafe kunnenshi yayi yana ji zuciyarshi na mishi barazanar tarwatsewa .

Da wani irin mugun ƙarfi yake jin zuciyarshi na bugawa , yayinda yake ganin alamar mutum na wucewa ta gabanshi da sauri ,sai kuma a dawo da sauri ,haka ya dinga ganin abu kamar wani shirin wasar kwaikwayo .

Yafi ƙarfin minti goma a wannan yanayin sannan daga baya komai ya tsaya cak ,a hankali ya fara buɗe idonshi ,in da ya sauke su kan wata Kyakkyawar yarinya mai Matuƙar kyau ,murmushi kawai take yi . Fuskarta bata da maraba da ta Naheela ,sai bambancin halitta .

Take jikin Bobbo ya ɗauki wani irin rawa ,zufa ta karyo mishi , wacece wannan yarinyar ? Ya ayyana a ranshi .

Murmushinta ya faɗaɗa yayinda fararen haƙoranta masu ƙyalli suka bayyana , “Ibrahim!” ta furta a hankali tana murmushi .

Rufe ido ya sake yi ,ya kuma buɗe su da sauri yana murza idon ,domin ƙara tabbatar da abunda idonshi ke nuna mishi .

“Ni ce ɓangarenka da kake gani a mafarki ” Ta faɗa .

Hannunshi ya miƙar yana ƙoƙarin taɓa ta ,amma sai ya ga da sauri ta cira sama . Ɗaga kai yayi yana kallonta .

Murmushi take sakar mishi, da ɗan ƙarfi yadda zai jiyo ta ta ce “Ibrahim ni wadda ba a iya taɓawa ce ,kuma ni ɓangarenka ce . Lokaci zai yi da zan baka dama ka taɓa ni, sai wata rana”. Bobbo na tsaye yana kallon ikon Allah har ta ɓace mishi da gani kamar hoto haka ta dinga dishewa har wurin ya koma ba kowa .

Saukar da kanshi Bobbo yayi daga kallon Saman da yake , wani mugun ciwon kai ya dabaibaye shi , jikin shi ya fara kakkwarwa ,haƙoranshi na gamewa .

Da ƙyar yake taka ƙasa a daddafe yana bin bango har ya samu ya shigo inda mutane suke .

Jatau mai Faskare yayi sauri a je gatarin da yake Faskare da shi ,ya nufo Bobbo da sauri ganin yana layi kamar zai faɗi ya taro shi yana faɗin “Lafiya dai Bobbo ” , cikin ƙarfi hali ya ce “ lafiya alhamdulillahi ,kama ni mu je gida dan Allah ” muryarshi sai rawa take yi .

Riƙa shi yayi har suka isa ,Jatau ya cika da mamakin ganin yanayin Bobbo .

Kewayensu Bobbo ya zagaya da shi . Mamma na goye da ƙaramin Sadauki aka shigo mata da Bobbo . Salati ta fara yi ,tana mamakin yau Sadauki ne aka riƙo haka ,da ƙyar Jatau ya ƙaraso da shi gaban Mamma dan Bobbo ya riga ya galabaita . Tabarmar kabar da Mamma ta shimfiɗa ,Jatau ya kwantar da Bobbo .

“Ina ka haɗu da shi Jatau ?” Mamma ta tambaya .

“Kin san ba a raba Bobbo da zama jeji ,ta wurina na ga ya gifto ,da alama daga can yake ” ya faɗa .

Mamma ta ce “Mun gode Jatau Allah ya biya ka “
Matsawa tayi kusa da Bobbo da jikinshi yayi wani mugun zafi kamar garwashi ,amma kuma sai zufa yake yi da rawar sanyi ,wannan wane irin al’amari ne .

“Sannu ka ji Bobbo ” ta faɗa .

Ba zai iya magana ba ban da bakin shi dake haɗewa tsabar sanyi da yake ji.

Da sauri Mamma ta shiga ɗakin ta ta ɗauko zani ta lulluɓe shi , sannan ta zauna gefenshi .

Tana zaunawa Sadauki ya ƙara fashewa da kuka ,da sauri ta miƙe tana jijjiga shi .

“Wannan wace jarabawa ce take tunkaro mu ?” Mamma ta faɗa .

Asama ta fito daga ɗakinta tana faɗin “Wai kukan me ƙaramin Sadauki ke yi da tsakar ra….. ” maganar ta tokare ganin an lulluɓe Bobbo .

“Me ? Me nake shirin gani haka ?” ta faɗa cikin ruɗani.

Mamma ta ce “ke ki zo ki gane mini wannan al’amari ,ɗa kwance uwa kwance haihuwar guzuma “.

Asama ta ce “Subahanallahi ,to me ya sami Bobbo ?”.

Mamma ta ce “yadda kika ganshi to nima haka na gashi . Ki mishi fatan Allah ya ba shi lafiya mu ji me ya same shi ,ni yanzu riƙe min Sadauki “.

“To Allah ya ba shi lafiya ” Asama ta faɗa .

Mamma ta miƙawa Asama Sadauki . Sannan ta duƙa gaban Bobbo . Kanshi ta kama tana mishi addu’a ,shi kuma ya rufe ido yana jin kamar zai yi barci .

<< Nawa Bangaren 10Nawa Bangaren 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×