Skip to content
Part 12 of 25 in the Series Nawa Bangaren by Queen-Nasmah

Ganye

Iskan da ke kaɗawa ko ina zai tabbatar maka da ruwan sama ke shirin sauka musamman yadda hadari ya taso yake ta majaujawa da ledodi a sararin samaniya.

Unguwar Ngurori 

Wani tamfatseten gida ne na ji na gani a unguwar, motocin dake cikin gidan idan ka gani zaka yi tunanin kamfanin motoci ne, ga furanni ko ina na gida .

Oda aka fara yi tare da jiniya alamar mota na ƙoƙarin shigowa cikin gidan,da sauri Burhama ya tashi sanye da kakinshi ya leƙa ta gate ɗin . Ta sauri ya kara wata waya me kamar radiyo ya ce “Excellency ne ya dawo ku matso.”

Nan take duk ma’aikatan masu kaki suka fito daga inda suke . Ma’aikatan kan su sun fi a ƙirga.

Duk suka jera kansu kamar waɗanda zasu yi assembly.

Gate ɗin Burhama ya tura ya buɗe .

Motoci guda biyar suka shigo inda duka sojojin suka ƙame wuri ɗaya tare da sarewa .

Dai-dai ma’ajiyar motoci suka yi parking motoci . Yayin da sojoji suka diddiro daga cikin motar suka nufi wata farar mota mai tinted (glass ɗinta baƙi).

Buɗe motar suka yi suna ƙamewa kamar ɗazu yayin da dattijon dake cikin motar ya fito ,sanye da babbar Riga ,yana ta ɗaga musu hannu cikin takun ƙasaita ,da ganinshi kuɗi sun samu wurin zama a gidan . Bai yi taku uku masu kyau ba ruwan sama suka sauko . Da sauri ɗaya Daga cikin sojan ya buɗe Lemar da ke hannunshi ya kara ma Excellency har ya shige cikin gida .

*****

Yadda Su Mamma suka ga safiya haka suka ga dare ko kaɗan Bobbo be yi rutsa ba sai sambatu da yake ta yi yana ihun Wacece ɓangarenshi.

Baffa ne ya shigo da wasu ruwan magani ya miƙawa Mamma yana faɗin “tashi ki tafasa maganin nan ina ganin gamo Bobbo yayi.”

Arɗo ya ce “wallahi ko,ni abun har tsoro yake bani.”

Mamma zata Karɓi maganin daga hannu Baffa kenan Asama ta ce a bari ta dafa .

Tashi tayi ta ɗora shi akan wuta ta dawo .

“Kin dame ni da kalmaminki guda biyu, ni ba ɓangarenki ba ne. kina azabtar da ni kawai.”

Babbo ya faɗa da ƙarfi.

Mamma ta fara mishi addu’a tana tofa mishi yayi da jikinshi ke ta kakkarwa .

Asama ta tashi ta juye maganin cikin kwano ta kawo .

Baffa karɓa ya ɗauki wani ƙyalle dake gefenshi ya tsoma yana matsewa yana shafa mishi a goshi .

Bobbo dai ji yake kamar ana zarar ranshi tsabar raɗaɗi .

Da ƙarfi ya ce “Nawa ɓangaren ,nawa ɓangaren kin takura min da Nawa ɓargaren ,dan Allah ki ƙyale ni ” ya kai ƙarshen maganar hawaye na gangaro mishi .

“Bazan jure hawayenka ba sadauki ” ɓangaren Bobbo ta faɗa tana ɓacewa .

Rufe idonshi yayi yana ji kamar an cire mishi rabin shashen jikinshi .

“Bobbo ” Mamma ta faɗa ganin baya motsi.

Yana jinta amma ba zai iya ɗaga hannunshi ba ,haka ma bazai Iya buɗe ido ba . 

“Mamma ” ya faɗa . Abun mamaki Mamma har yanzu sunanshi take kira .

Arɗo ya ce “ Ya na ga kamar baya numfashi.”

Bobbo ya ce “Ina numfashi mana ,idona ne bana iya buɗewa ” amma duk da haka babu wanda ya ji abun da ya ce .

Mamma ta ce “Kamar baya numfashi , me gida duba mana shi ” 

Matsowa Baffa yayi kusa da Bobbo ya ƙara hannunshi dai-dai saitin hancinshi .

Kallon Mamma yayi ya ce “Yana numfashi mana.”

Asama ta ce “Miyasa baya buɗe ido.”

Baffa ya ce “wataƙila yayi barci.”

Mamma ta ce “Allah yasa “

Da ameen suka amsa.

Dai-dai lokacin Mairo ta fito daga ɗaki goye da Sadauki .

Zuwa tayi ta duƙusa gaban su Mamma ta ce “Na san ba kowa ne zai fahimci ni ba ,amma ina da buƙatar namijin da zai biya min Buƙatuna ,Bazan iya zaman aure da Bobbo ba . Saboda haka zan tafi gida da Sadauki ,nayi alƙawari zan ci gaba da shayar da shi har na yaye shi .ina so idan Bobbo ya samu iya buɗe baki in nayi kwana ki arba’in nayi wankan tsarki a sanar da ni zan zo in karɓi takarda ta . Ina mishi Addu’a Allah ya bashi lafiya Allah ya mishi mafita ” .

Mamma ta ce “to kalama a baki dan bakinki “

Arɗo ya ce “Mamma ki bar yin irin haka Mairo na da gaskiya wallahi “

Baffa ya ce “haka ne ,Allah dai ya ba Bobbo lafiya.”

*****

Madubin sihiri Naheela ke kallo tana taɓa madubin da wata sanda .

Rufe ido tayi tana jan hanci .

“Naheel ” ta faɗa .

“Na jiyo ƙamshinka masoyi ” ta ƙara faɗa tana lumshe ido .

Tsalle ta daka nan take rufin ɗakin da take ya buɗe ta fita .

Idonta ne suka yi mata tozali da abin begenta Naheel .

Da ƙarfi ta diro

“Na ji a raina wuta na tunkaro ni ashe ke ce ” ya faɗa ba tare da ya juyo ba .

Naheela ta ɗan yi murmushi ta ce “shin ko zan iya sani me yareema ke yi cikin dokar dajin nan “

Har yanzu bai juyo ba ya ce “yawon miƙe ƙafa.”

“Ba wurin miƙe ƙafa sai wurin dubana” ta faɗa .

“Ki daina tunkaroni zaki ƙona ni wai baki fahimta ba ne ” yanzu kam cikin ɓacin rai yake maganar .

Murmushi ta ɗan yi tana “faɗin zaka saba dani a gefenka Yareemana, ka amsa mini tambayata.”

“Ke kika ɗauki nan wurin duba ni wurin shan iska na ɗauke shi.”

Zata yi magana kenan ya ɓace.

Murmushi tayi ta ce “da sannu zaka saba da bugun numfashina a kusa da kai.”

Juyawa tayi itama ta kalli gidan sihirinta nan take ta ɓace. sai gaban madubin ɗakin.

Rufe ido tayi kamar ɗazu.

Da wata gigitacciyar tsawa ta ce “Mudubin Sihiri ka haska min cikin zuciya Naheela.”

Warrrrrrr ! Ta buɗe ido wani koren haske ya fara fitowa daga idon ,nan take madubin yayi wani rame ya dinga juyawa kamar majaujawa .

Cikin daƙiƙa da basu wuce biyar ba madubin ya dawo ɗauke da hoton zuciyar .

“Cikinta na ce ba wajenta ba ” ta faɗa tana sakin jar wuta cikin Idonta .

Bayan wasu daƙiƙu madubin ya sake tsayawa daga juyawar da yake .yanzu ma ɗauke yake da hoton zuciyar .

“Cikinta na ce ko baka ji ba ” ta faɗa tana sakin tsanwan haske .

Amma har yanzu hoton zuciyar kawai yake bata .

Nan take jijiyoyin Idonta suka fiffito waje suka bude ƙuru-ƙuru da su .

Furuttanta suka miƙe suka yi zago-zago haƙoranta suka fiffito waje zara-zara da su . Cikin rawar murya da Matuƙar ƙarfi ta ce “Cikin zuciyar Naheel ” wani mahaukacin zafin ya fara bugun madubin .

“Ba Za ki iya ganin Zuciyar Naheel ba ,muddum in Raye ” wata murya ta karɗe ko ina .

Wuta Naheela ta fara saki ko ina duk ta haukace kamar ta ci babu .

“Ba mahalukin da ya isa ya min katanga tsakanina da Naheel ko shi Naheel ɗin da kan shi ballantana ke Zuhuriyya ,ki shirya tarbar bala’in da zai tunkare ki akan shiga gonata da kika yi “Naheela ta faɗa …

<< Nawa Bangaren 11Nawa Bangaren 13 >>

1 thought on “Nawa Bangaren 12”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×