Babban parlorn gidan ya shiga ,masha Allah gidan ya tsaru ƙarshen mataki , parlorn wani irin katafaren parlorn mai ɗauke da manya-manyan kujera in dai ba an faɗa maka mutum yana zaune kai ba to daga nesa ba za ka san akwai mutum zaune ba . Cikin takun da dattako ya shigo tsakiya parlorn da baka jin ƙarar komai sai sautin akwatin talabijin .
Wata hanya ya bi wadda zata sada shi da ɗakimshi . Aka ce idan kana duniya baka gama kallo ba ,a wannan gidan ma kaɗai zaka ga abun al’ajabi dan wajen gidan ba komai ba ne in aka haɗa da cikin . Wasu manya-manya ƙofofi ne aka shiga buɗewa har guda uku ,ko wace ƙofa da maza guda biyu tsaye gefenta . Ƙofar ƙarshe da aka buɗe kuwa ta bayyana wane haske ban mamaki ,wanda sai ka kalla zaka fahimci haske zinari da aka yi amfani da shi ne wajen ƙawata bangon wurin da wasu kallar duwatsu masu mugun ƙyalli .Ɓata lokaci ne bayyana yadda gidan yake .
Wata ƙofa ya buɗe ya shiga . Kayan jikinshi ya fara ragewa sannan ya shiga toilet yayi wanka. Wata tsadaddar Jallabiya ya saka sannan ya bita da da wasu ni’imtattun turaruka masu ratsa ƙwaƙwalwar wanda ya shaƙa.
Washe Gari
“Wai ni Allah wai ni Kaina Bobbo har yanzu bai motsa ba.” Inji Mamma dake zaune tana ta faman gasa mishi jikinshi da ya mugun yin zafi.
Asama ta numfasa ta ce “wai Mamma ba zamu kai Bobbo asibiti ba ta iya yuyywa zafin ciwo ne ke sa shi sambatu.”
“Kuma kin kawo shawara ina ganin haka za a yi, bari mahaifinsu ya dawo mu gani ya za a yi.”
Manna ta faɗa tana ci gaba da danna mishi goshinshi a hankali da ƙyalle.
“Salamu alaikum” Arɗo yayi sallama ,“wa’alaikumus salam” suka amsa mishi a tare .
Zuwa yayi ya zauna kusa da Bobbo yana faɗin “har yanzu bai samu matsowa ba.”
Mamma ta ce “Ina Fa, ko ido bai samu ya buɗe ba.”
“Kai amma Bobbo yana jin jiki ” Arɗo ya faɗa.
“Bobbo da tun yana ƙarami ko ciwon kai yana jimawa be yi ba ” Mamma ta faɗa .
“Wallahi kuwa ” Arɗo ya faɗa.
Dai-dai lokacin Asama da ta tashi bayan shigowar Arɗo ta dawo ɗauke da ƙwarya ta miƙa mishi “Mai gida ga fura ka sha ” .
Karɓa yayi yana faɗin “Yauwa Allah ya miki albarka Asama” .
“Ameen ya Allah ” ta faɗa.
*****
Zumbur Sarki Zawatunduma ya miƙe tsaye yana faɗin “Me ka ce?”
Bafaden ya ce “Wai garin Bustumbul zasu kawo mana hari anjima da yamma “
Sarki Zawatunduma ya ce “Ka sanar da Sarkin garin Zawatu (Wato Sarki zimba mahaifin Naheel ) ya kamata a haɗu a je yaƙin Domin ɗaga tutar garin Zawatu.
“To Sarkin Teku mai mulkin duk wata halitta a teku an gama ” Bafaden ya faɗa.
Sarki Zawatunduma ya ce “mulkin hallitu sai Allah ,bana son surutun banza.”
“Ayi min aikin gafara ,kuskure ne kuma bazan sake maimaita shi ba.”
Hannu sarki Zawatunduma ya ɗaga mishi sannan ya juya ya ɓace ɓat da ganinshi.
Masarautar Zimba
Zaune yake ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana lilo da ita ,yayinda fadawa ke ta mishi fadanci suna kirari .
“Jinjina Sarki Jinnu . An buga an bar ka . Da wani ya taɓa ka gara ya jefa kanshi cikin wuta . Allah ya ja zamanin sarki Zimba shugaban shugabanni , …….” basu ƙarasa ba Sallamar wani ta dakatar da su .
Amsawa suka yi yayinda sarki ya ɗaga hannu kawai .
“Me ke tafe da kai Alumu ” wani Bafade ya faɗa .
Wanda suka kira da Alumu ya amsa musu da cewa “Saƙo ne daga MASARAUTAR BUSTUMBULA ,sarkin Bahulandu ya ce anjima da faɗuwar rana zasu kawo hari garin Zawatu ”
Da ƙarfin Sarki Zimba ya miƙe yana faɗin “Gafara dai raggwayen maza garin Zawatu gagara gasa ne gare ku ,a haɗa mana dakarun yaƙi kafin rana ta faɗi zamu hallara filin daga ”
Yana faɗin haka ya cira sama cikin daƙiƙa biyu ya ɓace .
Alumu ya tashi ya fita dan ya sanar da Sarki Zawatunduma yadda suka yi da Sarki Zimba.
*****
Bayan Sarki Zawatunduma ya ɓace da ganin Alumu ɗakin gimbiya Naheela ya dira wanda ita ma dawowarta kenan daga gidan sihirinta.
“Masoyi wurinka na ɗaura niyyar zuwa ,aka yi sa’a ka zo ” Naheela ta faɗa.
Sarki Zawatunduma ya ce “Ƴata ƴar lelena gani na zo”
Murmushi ta yi ta ce “kunnena ya kasa gazgata min abinda ya jiyo lokacin da ina gidan sihiri “(idan na Naheela na gidan sihiri takan ga abubuwa kuma ta ji su a cikin madubin sihirinta)
“Me kunnuwan ƴata suka jiyo mata da har ta gagara gasgatawa ” ya faɗa .
“Labarin zuwan sarki Bahulandu ” Ta faɗa .
Jinjina kai yayi sannan ya ce “Tabbas Madubinki bai miki ƙarya ba “
Nan take idonta ya canza kala zuwa Koren launi ,har wani juyawa suke yi “Garin Zawatu ba na yara ba ne Abbana ,ka sanar da shi kar yayi hasarar rayuwarshi da ta al’ummar Bustumbula , yau fa tunda na tashi nake son shan jini “.
Murmushi Sarki Zawatunduma yayi ya ce “Na ji a jikina gimbiyar sarkin teku na buƙatar jini shiyasa dana ji labarin zuwan shi na zo gare ki da sauri dan ki yi shirin shan jini iya yadda zaki iya “.
Idonta na walwalniya wani haske na fita ,ta ce “ai ba a gayyatar shege ranar shegantaka , Yau jinin Ƴan Bustumbula shi ne abincina kuma ruwan shana ,sai nayi hani’an “.
Wata Doguwar siririyar sandar ƙarfe ce ta fito daga idonta mai mugun tsinin gaske ,sai sheƙi take yi .
Tsayawa tayi cak ita ba sama ba ita ba ƙasa ba.
Naheela ta matso kusa da Sarki Zawatunduma ta ce “ Masoyi wannan sandar ita ce ƙwarin guiwata ,zan sakar mata duka ƙarfina idan har ta faɗi bazan sha jinin kowa ba ,domin kuwa na rasa ƙwarin guiwata” .
Murmushi yayi ya ce “ƴata baki san iya ƙarfin da kike da shi ba ,amma ki yi da iya ƙarfin da kika san kina da shi “.
Kallonshi tayi cike da tarin tambayoyi amma sanin bazai amsa mata ba yasa ta maida dubanta ga sandar tare da rufe ido ta miƙe Hannayenta guda biyu ya dai-daita su daidai da saitin Sandar ,tana juya hannun da ƙarfi .