Skip to content
Part 14 of 25 in the Series Nawa Bangaren by Queen-Nasmah

Bayan ya gama shiri tsaf ya dawo ya zauna gefen gado tare da jawo wayarshi ya fara taɓawa ,kara wayar yayi alamar kira yake yi . Bugu biyu kawai tayi aka ɗaga . “your excellency yanzu nake shirin kiranka ” Hajiya Maryam ta faɗa .

His excellency ya ce “Lafiya dai ko ?”

Hajiya Maryam “Wallahi Jikin Nahad ne ba sauƙi”

His excellency Alhaji Sulaima ya ce “Amma ɗazu na kira Muhammad ya ce min yanzu zai kai ta asibiti nayi tunanin da sauƙi, shi ne dalilin kiran naki ma.”

Numfashi ta ja ta ce “eh shi da Babangida da Adam suka je , allurai aka mata abun kamar da sauƙi yanzu ta ƙara rifcewa ko ido bata iya Buɗewa.”

“Okay bari na zo ” ya faɗa yana sauke wayar daga kunnenshi .

Tashi yayi ya saka takalmi ya buɗe wata ƙofa ta bayan gida ya shiga ɗaya daga cikin ɓangaroran.

Hajiya Maryam na zaune kan kujera tana shafa kan Nahad da take kwance tana birgima .

Alhaji Sulaiman ya ƙaraso gabansu yana faɗin “Hajiya Maryama tashi bani wuri.”

Tashi tayi tana komawa kan ɗayar kujerar .

Zama yayi kan kujerar da Nahad take tana birgima ya ce “Nahad !”da ɗan ƙarfi .

Idonta ta ware da suka fiffito waje ta kafe shi da ido. 

“Me yake damunki ?” ya faɗa da ɗan ƙarfi .

Rufe ido ta sake yi tare da ƙara ƙamewa tana faɗin “Ban sani ba ,na faɗa muku ban sani ba ,wayyo Abba zuciyata zata fashe ,Abba zafi nake ji ,wayyo ni Yaya Muhammad , Yaya Ahmad kayi haƙuri bazan ƙara maka rashin kunya ba , Ummana bazan ƙara miki rashin kunya , wallahi nima bana sanin ina yi , Abbana kayi haƙuri bazan ƙara ba ” ta ci gaba da ihu .

Jawota yayi jikinshi ya rungume ta yana hura mata iska “Kiyi shiru Nahad.”

Cikin kuka da kuma rauni da ya bayyana ƙarara a muryata ta ce “To Abbana ,ka kira min yaya Ahmad.”

Hajiya Maryam ta ce “ya je siyo mata magani fa ,ki bari ya dawo mana.”

Nahad “Ummana ki ce ya dawo zan mutu ,wallahi zan mutu , wayyo zuciyata Abbana kira shi muyi bankwana.”

“Assalamu alaikum ” Ahmad yayi sallama , Alhaji Sulaiman ya ce “Ga shi nan ya dawo kiyu shiru ki bar kuka.”

Hannu Nahad ta miƙa mishi tana faɗin “Yaya Ahmad ka dawo ” sai kuma ta fara yin ƙasa da hannunta da sauri ya taro hannun yana kallonta . “Haba Autar Abbanmu ki daina kuka zaki samu sauƙi.”

Rufe ido tayi tana ji kamar barci zai ɗauke ta , “Abba ga su nan sun zo , Yaya Ahmad dan Allah kar ka bari su tafi ne , wayyo ni Allah ,Yaya Ahmad kayi haƙuri da abunda na maka wayyo ni , ga su nan , ga su nan dab dani ” ta runtse ido ta ƙarfi ,tana ci gaba da faɗin “Raina zai fita Ummana ,wayyo ni ku ji tausayi na “tun tana iya maganar ma ta kai ko bakin baya motsawa ,duk ta sandare tayi mugun haske duk da dama Nahad Fara ce tass.

Ahmad ya kalli Hajiya Maryam ya ce “Auntynmu wai yanzu ba yadda za a yi da Nahad ni wallahi abun nan yana ɗaure min kai”

Hajiya Maryam ta ce “ ƙaddara ce masu ciwon sickle cell haka suke fama , your excellency duk yadda baka so mu kwanta asibiti fa dole ne “

Alhaji Sulaiman ya ce “A’a ku bari ayi booking flight mu je America ina tunanin a nema mata lafiya zai fi “.

Ahmad ya ce “Ɗazu ma abunda Yaya Muhammad ya ce kenan wai gara a mata bone marrow transplant duk a huta , Ammy ma haka ta ce ” .

Alhaji Sulaiman ya ce “ Eh Haka Fulani ma ta ce min jiya ” 

Hajiya Maryam ta ce “To Allah yasa a dace ,Amma Nahad kam tana jin jiki “.

Da ameen Ahmad da Alhaji Sulaiman suka amsa.

*****

“Mamma Baffa ya ce ku gyara yanzu zai shigo da malami ” Arɗo ya faɗa .

Mamma na dakan fura wanda ya riga ya zame mata jiki ta ce “To ni gyaran Me zan yi , mayafi kawai zan lulluɓa miƙo min shi nan ” ta kai ƙarshen maganar tana nuna wa Arɗo mayafin da ke laƙe a ƙofar ɗakinta .

Jawo shi yayi ya miƙa mata ,sannan ya bi ta gefen Bobbo dake kwance saman tabarmar wundi ya raɓa shi ya fita . Bayan minti biyar sai ga su Baffa sun shigo da sallama ,Mamma ta amsa tana aje taɓaryar hannunta .

Baffa na gaba Shi da Malam Jafar , Arɗo na biye da su har suka iso inda aka shimfiɗe Bobbo , Mamma karkaɗe zanenta tayi ita ma ta zo ta zauna gefensu .

“Sannu da shigowa mai gida , malam ina wuni ” Mamma ta faɗa ,Baffa ya amsa da yauwa ,malam Jafar ya ce “Lafiya Lau “.

Baffa ya ce “Miƙo mishi ruwa Mamman Bobbo “

“To ” ta faɗa tare da miƙewa ta ɗauko moɗa ta buɗe randar ruwa ta ɗibi ruwa sannan ta kawo mishi .

Malam Jafar ya karɓi ruwan ya fara karanta ayatul kursiyyu ƙafa bakwai , suratul iklas ƙafa uku , suratul nas ƙafa uku , suratul falaƙ ma ƙafa uku , amanar-rasulu ƙafa ɗaya ya tofa a ruwan ,sannan ya shafa mishi a ƙafa , sannan ya shafa mishi a hannun , ya shafa mishi a fuska , wanda haka yasa Bobbo sauke wata wahalalliyar ajiyar Zuciya .

Mamma ta ce “Ya motsa ,laaaa Bobbo na motsi ” ta faɗa da farinciki ƙarara a fuskarta .

Malam Jafar ya jawo Jakar dake rataye a bayanshi ya ɗauko wani kasko ya aje , sannan ya kalli Baffa ya ce “A bani garwashi” .

Mamma ta kwalawa Asama dake suyar ƙosai kira , sai ga ta tazo.

Mamma ta ce “ ɗan zubo mana garwasu cikin wannan kaskon “.

“To Mamma” Asama ta faɗa tana ɗaukar kaskon .

Malam Jafar kuma ya fitar da ƙullukan magani ya aje da wasu robi da magani ciki ya aje .

Bata ɓata lokaci ba ta dawo ɗauke da kaskon da ta zuba ma garwashi ta aje , sannan ta juya ta wuce .

Wani garin magani ya buɗe ya zuba cikin kasko ,sannan yasa su Arɗo suka ɗaga mishi Bobbo zaune ,ya lulluɓe shi da wani zani ya tura kaskon ciki .

Nan take idon Bobbo suka fiffito waje yana faɗin “Kar ku rabani da Nawa ɓangaren Wallahil Azim ina son Ibrahim ,bazan iya rayuwa babu shi ba, idan kuka kashe ni bazai ƙara minti ɗaya a doron ƙasa ba “.

Mamaki ya cika su Baffa jin murya mace a jikin Bobbo , Mamma kuwa zare ido tayi , “na bani aljana jikin ɗana “.

Malam Jafar ya ce “Ke wace irin halitta ce me kike yi jikin wannan bawan Allah “.

“Malam ina maka magiya ne saboda soyayyar da nake ma Bobbo bazan so ya mutu ba ” aka sake yin magana ta jikin Bobbo .

Kuka Mamma ta fashe da shi tana faɗin “ Na rantse da Allah bazan yarda ba ,ku ƙyale ta kar ɗana ya mutu “.

Baffa ya dakawa Mamma tsawa yana faɗin “yi mana shiru dan Allah , malam yi aikinka”.

Malam Jafar ya ce “kina ganin so ne ya kawo ki jikin Ibrahim “.

Ta ce“Ni ban taɓa shiga jikinshi ba ,yau ma dole ce ta sa saboda ka kira ni da ayoyin Allah “.

Malam Jafar ya ce “ idan har abunda nayi shi ya kawo ki nan kenan kina da alaƙa da halin da Ibrahim yake ciki ?”.

Ta ce “Eh malam ,ni ce cikon ɓangaren Ibrahim ,duk inda babu ni a wurin Ibrahim zai zama shi da matacce duk ɗaya kamar yadda ka same shi “.

Malam Jafar ya ce “to ki yiwa Allah ki bar azabtar da shi ko in ƙona ki da ayoyin ubangiji ,kuma kin ga na zo da ruwan magarya zan watsa miki su “.

Ta ce “Malam zaɓin biyu ne nima bani da wani sai shi ,wallahi in ina kusa da shi dole sai ya ganni kuma hakan yana azabtarshi , idan nayi nesa da shi kuma bazai iya motsi ba, idan kuma ka ce ko ƙona ni hakan zai nuna jikin Bobbo kuma yadda zan ji zafi haka Shi ma zai ji ” .

Malam Jafar ya ce “ shiyasa kika zaɓi ki yi nesa da shi “.

Ta ce “ eh malam ,kuma nima ina azabtuwa da hakan ,na gaya maka Shi ne Nawa ɓangaren “.

Malam Jafar ya ce “kina mana ƙarya dai ,ni zan ƙona ki yanzun nan “

Ruwan magarya ya ɗauka cikin wata kwalba ya bude

<< Nawa Bangaren 13Nawa Bangaren 15 >>

1 thought on “Nawa Bangaren 14”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×