Ruwan magarya ya ɗauka cikin wata kwalba ya buɗe , sannan ya yaye lulluɓin da yayi ma Bobbo ya kai zai watsa mishi ruwan magaryar Bobbo ya miƙe da ƙarfin tsiya ,cikin muryar da ba tashi ba ,wanda aljanar ce da kanta ta ce “Malam ” , ta kalli mamma ta ce “kar ki bari ƙonani ya zama mafarin tashin hankalinku.”
Zumbur Mamma ta miƙe tana faɗin “Malam Jafar, shin Bobbo ɗana ne ko, to ku ƙyale shi idan har sai an ƙona aljanar nan.”
Arɗo ya ce “ Haba Mamma ki bari yayi aikinshi ba a yiwa aljani yadda yake so.”
Da ƙarfi Bobbo ya juya wanda ba shi yayi hakan ba aljanar da ke jikinshi ce , wata wuta ta saki mai ƙarfin gaske sai saitin fuskar Arɗo ,cikin muryar da ke nuna hasala ta ce “Ka fita a sha’anin nan.”
Malam Jafar ya ce “To yanzu dai zauna ki faɗa mama sunanki ?”
Zama Bobbo yayi kamar yadda malam ya ce “ sunana Nahad Sulaiman , malam ku daina ce min aljana ni mutum ce kamar ku “.
Mamaki ƙarara ya bayyana a fuskokinsu ,kowa da tambaya a fuskarshi .
Malam Jafar ya ce “kina mutum taya kika iya zama a jikin wani ,wannan ba gaskiya ba ne ,yanzu kiyi abu ɗaya ki bar shi ya huta “.
Aljanar ta ce “To malam zan tafi ,amma Bobbo bazai tashi ba.”
Baffa ya ce “Na gaji da wannan wasar kwaikwayon , Malam Jafar yi aikinka.”
Ruwan magarya da malam ya rufe ya ƙara buɗewa ya watsa mata.
Da ƙarfi ta gantsare “Ahhhhhhhhhhhhhhhhhhh!”
Sai kuma ta ƙame , idonta suka ƙaƙƙafe , yayinda hannunta suka murɗe , Mamma ta miƙe cikin kuka tana faɗin “La’ilaha ilallahu Muhammadur rasulullahi (saw) shi kenan kun kashe shi ” ta ƙara fashewa da kuka , yayinda Malam Jafar ya shiga karanta ayoyinda Allah amma ko motsi bata ƙara yi ba . Arɗo da Baffa mamakin duniya ya cika su .
Jin Mamma na kuka ya saka Asama zuwa cikin sauri tana faɗin “wa suka kashe “.
Mamma ta ce “wa in ba Ibrahim ba ,sun kashe min ɗa “
*****
Cikin ruɗewa Hajiya Maryam ta juya tana kallon Nahad dake ihu tana faɗin “ya ƙona ni” , kallon yadda idon Nahad suka ƙaƙƙafe take yi, hannunta ya wani murɗe , ta wani ƙame , tashi Hajiya Maryam tayi ta dawo kusa da Nahad domin tabbatar da yanayin da take ciki , a firgice ta ja baya tana rufe ido tare da faɗin “Innalillahi wa’inna ilaihir raju’un ,Nahad me zan gani haka ” . Da sauri ta ɗauki waya ta kira Ahmad da bai daɗe da Fita ba shi da Abbansu.
Ahmad yana zaune parlor tare da Ammynshi suna fira , wayarshi ta hau ruri , “Hello Aunty ” ya faɗa , “Ahmad ka zo ba lafiya fuskar Nahad ba … ” bai ma bari ta ƙarasa zance ba zare wayar daga kunne ya miƙe zai fita duk ya rikice ,Ammy ta ce “Ahmad lafiya kuwa “, Ahmad “Ammy Nahad ce ba lafiya ” yayi maganar yana ƙara sauri .
Ammy ta ce “ kai dai ka sani , kayi ta rawar jiki akan waccan yarinyar mara kunya ” .
Ba tsaya ba ya fita , part ɗin da ke kusa da nasu ya shige , gani yake ma ba sauri yake ba , dan sai ya ta buɗe ƙofofi zai shiga parlorn in dai ta gaban gidan zaka bi to haka ne a ko wane ɓangaren na gidan .
Gudu ya fara yi yana haɗawa da sauri , har samu ya buɗe Ƙofar parlorn kamar wanda aka bankaɗo ya shigo . “Aunty me ya sami Nahad “, cikin rawar baki ta ce “du…duba ka ganii ” .
Matsawa yayi kusa da Nahad , da sauri ya ja da baya yana kallon Hajiya Maryam “waya ƙona mata jiki ” .
Hajiya Maryam ta ce “nima ban sani ba , yadda take kwance haka na ganta ” , Matsawa Ahmad ya sake yi ya kallonta , “Aunty har da wuyanta duk ya ƙone ,kuma Abba ya fita muna fita shugaban ƙasa ya kira shi wai meeting ɗin gaggawa , ya hau jirgi zuwa Abuja , Yaya Muhammad da Yaya Adam kuma sun fita bari in kira yaya Babangida ina tunanin yana gida “.
Hajiya Maryam “to kira shi mu ji “.
Hannu yasa cikin aljihu , ya laluba amma ba waya ciki , dafe goshi yayi tunawa da yayi ya bar wayar parlorn Ammy , Hajiya Maryam ta ce “me ya faru “, “lokacin da kika kira ni sai na kiɗime ashe na jefar da wayar parlorn Ammy “.
Hajiya Maryam ta ce “ga wayata kira shi da ita ” ta kai ƙarshen zancen tana nuna mishi wayar kan standard table ɗinta na talabijin.
*****
Garin Zawatu cike yake dam da rundunar Aljanu kowa da ƙungiyarshi , duk wanda ka gani zaka ganshi Saman doki Yana , sai wucewa ake yi zuwa filin da za a yi yaƙi , sai da aka gama hallara ba ɗaya Sarki Zimba da Sarki Zawatunduma suka shigo tare da ayarinsu , kowannensu ɗaure da takobi a ƙugun. Naheel ya shigo daga ƙarshe ,duk da tare yake da Mahaifinshi. Sarki Bahulandu ma da ayarinshi sun hallara wuri , a taƙaice ma su suka fara hallara wurin yaƙin.
Sarki Zawatunduma kuwa tun da ya iso filin daga yake raba ido ,amma har yanzu bai ga gimbiyarshi Naheela ba , duk yadda ya kai ga bincike yau dai ya gagara ganin komai game da gimbiyarshi.
“Mu kai musu hari ” Sarkin garin Bustumbula wato sarki Bahulandu ya faɗa .
Riiiiii! Ayarin sarki Bahulandu suka yi cikin ƴan Zawatu .
Shuuuuu shuuu ! Kukan wata ƙatuwar tsuntsuwa ya ruɗe wurin ,maimakon a yi faɗa sai kowa ya ɗaga kanshi sama dan ganin mine ne .
Wata irin ƙatuwar tsuntsuwa ce da Naheela ke kira Ruhaina , tsuntsuwar ta sha ado na ban mamaki duk ilahirin jikinta duwatsu sai ƙyalli take yi , a hankali ta fara saukowa in da aka fahimci akwai wata kan tsuntsuwar , takalminta baƙaƙe masu ado da dutsuna kamar irin na jikin tsuntsuwar.
Sai da da ta sauko gaba ɗaya sannan kowa a wurin ya tabbatar macece , Naheela ce sanye cikin baƙaƙen kaya riga da wando waɗanda suka zauna matuƙa a jikinta , jambakin bakinta baƙi , sannan rabin fuskarta daga hancinta har zuwa goshinta duk ta shafa baƙi . Idonta sai fitar da wuta yake yi wal-wal-wal . Tuni kowa a wurin ya sha jinin cikinshi ganin Naheela .
Tsananin fushi da ɓacin rai duk ya bayyana tare da ita . Hannu ta ɗaga ta juya ,cikin tsawa mai ƙarfi ta ce “Ruhaina ki saki macizai yanzun nan “
Baki Ruhaina ta buɗe wasu zara-zaran macizai masu kai uku suka fara fitowa daga bakinta .
“Kun san su wa zaku kaiwa hari “Naheela ta ce da macizan .
Nan take macizan suka nufi Ƴan Bustumbula , yayinda Naheela ta ce “Sarki Bahulandu ni ce daidai kai ,dan haka matso gani “.
Da azama ya nufo Naheela yayinda ya ɗaga takobinshi sama ,yana isowa rafka mata ita a kai , cikin rashin sa’a ashe…