Da azama ya Nufo Naheela , yayinda ya ɗaga takobinshi sama, yana isowa ya rafka mata ita a kai , cikin rashin sa’a ashe ba ita ya sama ba ta kauce. Ɗagowa tayi cikin ɓacin rai ta cira sama da ƙarfi ta buga mishi wani ƙaramin ƙarfe wanda gara a watse maka kai da a buga maka irin wannan ƙarfen , ƙarami ne amma kuma idan aka buga maka shi yana durƙusar dai kai . A gigice Sarki Bahulandu yake , nan take ya faɗi ƙasa . Da ƙarfi Naheela ta biyo shi ƙasa , tare da kara hannayenta guda biyu ta saitin zuciyarshi , idonta suka fito daga mazauninsu suka zazzalo har suna shirin taɓa ƙasa , gantsarewa yayinda wani ɓakin haske ke fita daga jikin sarki Bahulandu yana shiga ta hannun Naheela , yana gama shiga ta miƙe kamar wadda aka tsikara . Sannan ta juya ta saki wata ƙwallon wuta daga idonta zuwa cikin Ƴan gari Bustumbula .
Ƴan garin Zawatu kuwa dawowa suka yi Ƴan kallon dan gefe suka koma suna kallon yadda macizai ke ta watsar da jini .yayinda wannan ƙwallon wutar da Naheela ta saki ke ta ƙona wasu . Cikin awa biyu Ƴan garin Bustumbula suka dawo ƙasa , wasu duk sun ji raunuka wasu kuma duk sun mutu .
Nan take a wurin sarki Zimba ya fara magana cikin muryar Babba “A yau ni Sarki Zimba na sauka daga kujerar Mulkina na barwa Naheela ƴar sarki Zawatunduma , taron Naɗin sarautar wani sati ne da izinin Allah ” yana faɗin haka ya ja doki , sauran Ƴan garin suka bi bayanta sarkin . Naheela kuwa matsowa tayi kusa da Naheel ta . Yayinda ya mata murmushi yana faɗin “Jinjina ga sauraniyar Zawatu , ina taya ki murna.”
Murmushi ta sakar mishi ,sannan ta ce “Na gode masoyin Ruhina ,ga shi dai kai ne ka fara taya ni murna.”
“Eh ni ne.” ya faɗa yana juya akalar dokinshi.
Naheela ta ce “Yaushe kai ɗin nan zaka so ni?”
Ba tare da ya juyo ba ya ce “so tarin yawa ina yunƙurin in ga na kyautata miki. Amma kiyi haƙuri bazan iya rayuwa tare da mace ba.”
“Zan koya maka rayuwa tare da ni Naheel.” ta faɗa .
Bai ce da ita komai ba ya wuce .
Ruhaina ta matso kusa da Naheela ta durƙusa domin ta ba Naheela damar hawa bayanta .
Hawa Naheela tayi , sannan Ruhaina ta cira sama.
Ba yadda malam Jafar bai yi da Mamma akan ta bari yayi abun da ya dace amma fir Mamma taƙi amincewa . Dole Baffa ya ba shi haƙuri ya tafi.
Kuka Bobbo ya fara yi “Mamma zafi nake ji.”
Da sauri Mamma ta matso tana faɗin “Ka farka?” Cikin kuka kamar ƙaramin yaro ya ce “Mamma zan mutu , ji nake kamar raina zai fita , Mamma an ƙona wani ɓangare na jikina, fuskata da wuyana zafi.” Mamma ta ce “ƙyale su Bobbo Allah ya zai saka maka , sai da na ce kar su yi , amma wancan yayan naka mai taurin rai da Baffanku suka nace sai an yi , ai ga irinta nan Allah dai ya isar maka wallahi “Rufe ido yayi ,yayinda hawaye masu zafin gaske ke sauka kan kuncinshi .
Baffa na jin Mamma bai ce mata ko ci kanki ba sai ma tashi da yayi ya fita tare da Arɗo.
Asibiti
Hajiya Maryam ce ke kai da kawo kusa da ɗakin da aka shiga da Nahad , yayinda Ahmad ke ta zirga-zirgar siyo wancan, mayar da wancan kawo wancan . Likita fito ,sauran nurses ɗin suka turo Gadon da Nahad take kwance kai ,duk fuskarta an naɗe ta da bandage har zuwa wuyanta . Idonta kawai aka bari buɗe ,da kuma hancinta da aka bar mata buɗe domin numfashi . Sai baki saboda cin abinci.
Hajiya Maryam na ganin an fito da Nahad ta matso da sauri tare da saurin riƙe hannun Nahad ,ta ce “Allah ya baki lafiya ƴata “. Ɗakin jinya aka shiga da ita aka kwantar ita ,duk Hajiya Maryam na riƙe da hannunta . Kan Nahad ta shiga shafawa lokacin da likita ke mata bayani.
“Gaskiya ban taɓa ganin ƙonewa mai abun al’ajibi irin wannan ba , abun mamakin ma sai an gama gyarawa kamar ana mata feshin jini sai komai ya dawo sabo , sai mun sake gyarawa , dalilin ma da yasa muka ɗauki lokaci kenan.”
Hajiya Maryam ta ce “Ashe abun har ya kai haka , to doctor ya maganar rashin lafiyarta.”
Likita ya ce “to his excellency ya ce min zaku je America , ni dai na shawarce shi da ya bari ayi bone marrow transplant ɗin a nan national hospital Abuja.”
Hajiya Maryam ta ce “to kai doctor kana ganin za a dace nan ɗin?”
“Eh mana , ai koma ina ne addu’a ake so , asibitin America ba abunda zasu nuna ma national hospital Abuja.”
“To shi kenan likita Allah yasa a dace ” ta faɗa .
Da ameen ya amsa sannan ya fita ya bar nurse ta ma Nahad allura sannan ita ma ta fita.