“Naheela Ummanki tana inda kika fi tsana.” Sarki Zawatunduma ya faɗa , numfashi Naheela ta saukar tare da faɗin “Amma Taya zan tunkari wurin,” Hannunta Sarki Zawatunduma ya jawo ya riƙe , sannan ya ce “Da kanki zaki tunkari wurin cike da soyayya, kuma zaki gane Mahaifiyarki da zuwanki wurin , idan zaki je ki bi ta cikin dutsin Kimbaya , ni zan wuce lokaci na tafiya ta yayi “, Naheela ta ce “Abbana aron shekaru da kayi ya zaka fanshe su?”, murmushi yayi hawaye suka fara gangorowa yana gogewa , “Zan bayar da fansar numfashina “, nan take Naheela ta ƙara matsowa kusa da shi a kiɗime ta ce “Ban fahimci me kake faɗi ba?”
Hannunta ya saki ya dafa kafaɗunta yana faɗin “na fanshi shekarun kasancewa tare dake ta hanyar sadaukar da jinina ga Gongumba (shugaban macizai )”, Hawaye suka fara bin kuncin Naheela cike da jin zafin maganar Abbanta ta ce “Kana nufin bazan sake ganinka ba ?” , “Naheela lokacina yayi na tafiya , ki kula da kanki da kuma sabon ahalin da zaki gina “. Ɓat ya ɓace daga ganin Naheela.
*****
Nahad ce zaune kan Kujera tana danna waya lokacin da Umma ta shigo , amma bata ɗago ta kalle ta ba, Hajiya Maryam ta ce “Ke Nahad baki iya gaisuwa ba “, idonta ta ɗago tana kallon Hajiya Maryam sannan ta saukar da su , Hajiya Maryam ta ce “La’ilaha illal lahu Muhammadur rasulillahi ( saw ) , Nahad kin fara halin naki ko ?” , ƙara ɗagowa tayi da kanta yanzu kam idonta sun fito waje sosai jijiyoyin idonta sun yi ja , Hajiya Maryam tayi saurin Ja baya tana jin wani zafi duk ilahirin jikinta.
Zaunawa tayi gefen Nahad ta ce “Nahad wai waya taɓa ki?”
“Abbana !” Nahad ta faɗa.
“Abbanki da baya nan ,Nahad ki ji tsoron Allah ,ina ce wata ɗaya da suka wuce kina nan kamar zaki mutu?”
“Kina ganin zan iya mutuwa ne ?” Nahad ta tambaya.
“Eh mana ai kowa sai ya mutu ” Hajiya Maryam ta faɗa . Nahad ta ce “To ni shekerun da zan yi duniya sai kin yi mamaki” , cikin kawar da zance Hajiya maryam ta ce “Faɗa min me Abban naki yayi miki ?”, “ an sha jininshi ne ” ta faɗa , Hajiya Maryam ta ce “ke kika sha jininko ja’irar yarinya “, “Umma ki Kira Abba ki ji in yana lafiya ” ta faɗa.
“Ni bazan iya da shiriritarki ba ta shi ki je ɓangaren Fulani ki ce ta baki saƙona ” , tashi Nahad tayi , amma Hajiya Maryam bata ƙara ganin ko walƙiyarta ba . Jinjina kai Hajiya Maryam tayi a hankali ta ce “Allah ka mini maganin abunda bazan iya yima kaina ba “, tashi tayi ta shige ɗaki.
Hajiya Fulani na kitchen sai ji tayi an taɓa ta , a razane ta juyo , sai kuma ta sauke numfashi ganin Nahad “Nahad ba za ki daina firgita mutane ba ko ?” , idonta da suke tsara-tsaye ta ware ta ce “Ko kaɗan ba da niya nake firgita ki ba Maman Muhammad ” . Numfashi ta sauke ta ce “Ta ina kika shigo bayan na rufe ko ina ” , Nahad ta ce “to ni dai gani na taho , Umma ce ta ce ki bata saƙonta , Fulani ta ce “To bari na ɗauko miki.”
Ɗaki ta wuce tana jinjina al’amarin Nahad “Wani lokaci sai ka ga kamar yarinyar can ba mutum ba ce “Fulani ta faɗa, Nahad dake nesa da ita ta ce “Amma kuma mutum ce ni ba ” ,Hajiya Fulani ta sha jinin jikinta dan ta san duk inda tayi magana Nahad sai ta ji , saboda haka ta shige ɗaki a tsorace ta ɗauko wata leda babba ta fito da ita.
Nahad na tsaye tana kallon yadda take yin ƙasa kamar zata nutse cikin ƙasa , ta ji fitowar Hajiya Fulani , mayar da idonta tayi ga Hajiya Fulani , tare da tsayawa cak kamar ba ita ba ce ke shirin nutsewa cikin ƙasa.
Ledar Hajiya Fulani ta miƙa mata tare da faɗin “ki ce mata lace ɗin kawai aka samu . Gyalen kuma sai gobe zai iso “, karɓa Nahad tayi tana faɗin “to shi kenan” juyawa tayi ta wuce .Hajiya Fulani kuma ta shige kitchen.
*****
Mamma ce ta fito daga ɗakinta riƙe da matakaɗin fura wanda kowa ya riga ya san dakan fura ya auri Mamma , dan kullum sai ta daka fura ta dama . Kallon Bobbo tayi da yake zaune Ƙofar ɗakinta ta girgiza kai , sannan nufi turmin dakan fura ta aje matakaɗin , tare da jawo kujerar katako ta zauna , “Wai kai Sadauki wane irin mutum ne , a ce mutum ya riƙa zama shi kaɗai , ko dai zuwa za a yi dawo maka da yaranka ?” , girgiza kai Bobbo yayi ya ce “Mamma kowane yaro mahaifoyarshi ita ce garkuwarshi , ni kaina ban gama kula da kaina ballantana Yarana , ina ganin Zaman kowannensu wurin Mahaifiyarshi ya fi ” , Mamma ta ce “Amma wannan zaman kaɗaicin bai yi ba ” . Numfashi Bobbo ya sauke ya ce “Haka Allah ya ƙaddara , ban isa in yi jayayya da abunda Allah ya ƙaddara min ba “. Mamma zata yi magana kenan Mairo ta shigo “Salamu alaikum ” , “wa’alaikumus salam ” Bobbo ya amsa . “Ina wuninku ” ta faɗa , Mamma da Bobbo suka amsa mata.
“Na same ku lafiya ” Mairo ta faɗa , Mamma ta ce “lafiya ƙalau” , Bobbo ya kalli Mairo ya ce “Ina Sadaukina ?” , Mairo ta ce “Yana wurin Inna na baro “, Bobbo ya ce “to ki shafa min kanshi “,“in sha Allah ” ta faɗa , numfashi Bobbo ya sauke sannan ya ce “Na ji saƙon da kika bar min na gode sosai , kuma ko kaɗan ban ga laifinki , ina so ki sani har abada bazan daina girmama ɗaya daga cikin matan da na aura ba , na aure ku ne dan so ba dan muzgunawa ba , dan haka kina da damar nema ma kanki farinciki ” , tun da Bobbo ya fara magana Jikin Mairo yayi sanyi kamar ta ce kar yayi . Amma ta san ba za ta iya zama da shi ba.
“Kafin mu je ko ina Mairo ina roƙonki da ki yafe min duk abunda na miki ina sane da kuma wanda ban sani ba , ko kaɗan ban yi haka dan in muzguna miki ba, kuma ban taɓa ji a raina ina son cutar da ke ba , ni kaina ban san me yake damuna ba , dan Allah ki yafe min a matsayin mahaifin ɗanki “, Mairo da hawaye suka cika ma ido cikin rawar murya ta ce “Na yafe maka duniya da lahira.”
“Na gode da yafiyar da kika min , Allah ya saka miki da mafificin alkhairi ” ya faɗa , Mairo ta ce “Ameen , nima ka yafe min duk abun da na maka,” “Ko akwai abun da kika min na yafe miki , ballanta baki yi hakan ba “ya faɗa ,Mamma dai har yanzu bata ce komai ba illa ma hankalinta da ta mayar wurin dakan fura . Bobbo ya ja numfashi mai nauyi ya sauki , sannan ya ɗago ya kalli Mairo ya ce “Allah shaida ne ina jin nauyin furta Kalmar saki amma kuma dole ne gare ni , Allah ka min afuwa ” ya faɗa yana runtse ido , Mairo ta ce “Bobbo ka…… ” katse ta yayi cikin Dakiya ya ce “Mairo na sake ki saki ɗaya ,idan kin gama idda miji ya zo ki yi aurenki , ina miki fatan miji na gari wanda zai riƙe ki amana ” yana faɗin haka Mairo ta fashe da wani irin kuka mai ratsa zuciya tana faɗin “,Wayyo ni Allah wai ni kaina , na shiga uku , yau ƙaddara ta raba ni da mai sona da gaskiya ” Bobbo tashi yayi ya shige ɗaki.
Mamma ta tsagaita dakan ta kalli Mairo ta ce “Abun rabo ya ƙare miƙa hannu na mine ne, ki tashi ki tafi gida kar ki cika mu da kuka ” . Tashi Mairo tayi tana share ƙwalla ta wuce . Mamma ta bita da kallo har ta fita , sannan ta ce “Yau ni na ga abunda ya ture ma buzu naɗi , matar nan da kanta ta ce a sake ta wai kuma ta zo tana kuka , to Allah ya kyauta ” tayi maganar tana riƙe haɓa , sannan ta ci gaba da dakan da take yi.