Skip to content
Part 2 of 25 in the Series Nawa Bangaren by Queen-Nasmah

Da hanzari Macijin ya riƙa bin ƙasa, yayin da wutar da ke idon Naheela ta ci gaba da ruruwa, tana fitar da wani mashahurin zafi. Hannayenta duka suna a ware ta juyar da kowanne yana kallon wani ɓangare. Wani irin iska me matuƙar ƙarfi, ya riƙa fita daga tafin hannuwanra. Zamzila kuwa wani ƙarfi yake ji duk lokacin wannan iskan ya bugo sa, da ma ƙarfin iskan ke ƙara masa kuzari da karfin gudu kamar Ingarman doki. Shi kuma hasken wutar ke ƙara haskaka masa hanyar da zai bi, domin nemo Naheel, ba zato ba tsammani Zamzila yayi karo da wani ƙaton dutse.

“Ahhhhhhhhhh! “Ta saki wata mahaukaciyar ƙara wadda ta karaɗe ko ina na cikin dajin, sanadiyar Karo da zamzila ya yi da dutse. Jini ya kwaranyo daga cikin kanshi yana malala. Jinin da ke zuba a kan Zamzila ne ya janyo wa Naheela faɗuwa, guiwowinta suka lashi ƙasa. Tim! Ta durƙushe, kanta na kallon ƙasa, ta ɗauki kusan minti uku a haka. Daga baya ta ɗaga kanta sama, wani Koren haske ya fito cikin idonuwanta, wul-wul yana tsalle da sauka kamar ƙwallo. Sai da ta fitar da dunƙulen haske guda bakwai daga cikin idonta.

Kanta ta ɗaga tana kallon waɗannan ƙwallayen masu haske da ke zagaye Saman kanta. Cikin ɓacin rai ta fara magana “Ku kai wa Zamzila ɗauki.” Ta ƙarasa maganar cikin rawar muryar.

Bat! Waɗannan Ƙwallayen suka ɓace, tare da lula a sararin samaniya, cikin ƴan daƙiƙu suka isa in da Zamzila yake. Daidai kanshi suka tsaya, sannan suka haɗe kansu wuri ɗaya suka saki wani ɗorowan haske ya dinga sauka kan Zamzila duk ƙarfin hasken nan bai sa ya motsa ba. Nan take suka ƙara warewa, suki doki juna ƙarar karon da suka yi ya assasa baƙin hayaƙi ya turnuƙe wurin, wani ƙarfi ya shiga Zamzila, ya tashi ya fara bin ƙasa amma yanzu ba kamar ɗazu ba sanadiyar buguwar da yayi. Zumbur Naheela ta tashi tsaye ta sake sakin wannan wutar kamar yadda ta yi ɗazu, wata mahaukaciyar dariya ta saki har tana wani duƙewa. Nan ta tsagaita tare da haɗe rai kamar ba ita ke dariya ba. Ganin yadda Zamzila ke tafiya cikin ƙasa baya sauri, ƙara ware idonta tayi ta ce “ Me na ci na Asham da zan yi ramuwar sallah, Zamzila gara ma kar ka sare dan faɗuwa ba tawa .”

Ta kai ƙarshen maganar tana fitar da baƙin hayaƙi a cikin bakinta.

Fadar Zawatunduma

Kowa ce halitta tana da nata muhalli, haka yake a garin Zuwatu. Garin Zuwatu gari ne da babu wani Ɗan’adam da yake da ƙarfin ikon takawa zuwa gurin. Gari ne da ba a ba wata halitta damar zuwa ba. A wannan garin akwai wata teku mai ɗimbin tarihi.

Wannan tekun ta girmi duk wani aljani da za ka gani a wurin, idan ka zaftare Mai Martaba ZAWATUNDUMA (wato sarkin aljanun teku).

Tun kafin Zuwata ya zama gari, Zawatunduma yake zaune a cikin wannan tekun, hakan yasa duk wanda ya zo, ya same shi a cikin a nan.

Wannan dalilin yasa Sarki Zawatunduma mulkin duk wani aljani da ke cikin tekun Zuwatu. Babu mai gida irin nashi, dutse aka sassaƙa ya zama muhallinshi. Sauran aljanun suna zama ne a cikin ruwa ba su da damar da za su gina gida wannan ƙarfin iko umurnin Mai martaba ne.

“Mai Martaba an samu labarin inda Gimbiya Naheela ta ke “. Ɗaya daga cikin Bafadenshi ya faɗa. Naheela kaɗai ce wadda ke wahalar da su idan ta ɓata duk dubararka sai ka wahala zaka gane inda take. Yau ma tun safe ake nemanta amma babu ta babu labarinta.

Da sauri Sarki ya miƙe a duniya babu abin sa yake so kamar Naheela ita kaɗai ce wadda ya mallaka madadin jininshi, a rayuwarshi bai taɓa aure ba. Ƙaddara ta haɗa shi da mahaifiyar Naheela wanda a yanzu bai san in da take ba.

“Tana ina? Ina Naheelar take? “Ya tambaya cikin rawar murya. Bafaden ya ce “ A hasashenmu tana fadar Sarki Zimba, can ta ke zuwa wurin Yarima Naheel, kuma…”

“Dakata! Hasashe ne ma ashe! “Sarki ya faɗa a fusace.

“Yallaɓai mun haska abin duba, amma ƙarfin da Gimbiya Naheela ke aiki da shi ya mamaye duk wani kayan sihiri da muke da su. Ba zamu iya nemo ta da ƙarfinmu ba”.

Runtse ido Sarki ya yi , _”kamin alƙwari ba za ka taɓa amfani da ƙarfinka ikonka a kaina ya kai Abbana”_ Maganar Gimbiya Naheela ta dawo mishi a kai.

Da sauri ya buɗe idonshi saboda tunawar da ya yi na ya ɗaukar mata alƙwari.

A hankali ya ce, “Yanzu miye mafita? Na yi wa Gimbiya alƙwarin ba zan yi amfani da sihirina kanta ba “.

Cikin jinjina al’amarin Bafaden ya ce “Babbar magana gawa ta riƙe mai wanka, yanzu ya za mu yi?”

Sarki ya ce “ Kira min Muƙanzimu ka ce ya zo da kayan aikin shi”.

“An gama Mai martaba”. Bafaden ya faɗa. Sannan ya tashi ya fita.

Wuro Barka

Yara ne sun kai su sha biyar, wasu duk tsararraki ne, babban cikinsu ba zai wuce Shekara 8 ba, zaune suke kan wundi (tabarmar kaba), an zuba musu abinci cikin wani ƙaton kwano, rinɗima-rinɗiman ƙwaryoyi ne cike da fura , har ƙwarya uku aje gefensu, da kuma wata ƙatuwar roba an cika ta da ruwa duk yaran kayan fulani ne a jikinsu, sai faman cin tuwo suke da madarar shanu, yayin da wasu mata guda uku suke sharar tsakar gidan.

Daga can ɗayan gefen kuma Arɗo ne da matarshi Asama zaune tana faman renon tsohon ciki, sai yaransu guda uku zaune suna shan fura. Mamma kuma mahaifiyarsu Bobbo na tsaye gaban turmi tana dakan fura, Bobbo ya shigo kanshi a ƙasa, yaran da ke zaune kan tabarmar kaba suka fara tsalle, suna murnar ganinshi, “Bobbo sannu da zuwa ” duk suka faɗa a tare. Sai da ya shafa kansu gaba ɗaya yana murmushi , sannan ya gaida Mamma, Mamma ta ce “Lafiya ƙalau Bobbonmu, kuma Bobbon yara ya kake?”Murmushi ya ɗan yi ya ce “Ina lafiya, bari na shiga daga ciki Mamma”.

Mamma ta ce,“Kai kullum ka kama ka ƙunshe kanka cikin ɗaki Bobbo, a ce kai ba za ka karɓi ƙaddara ba, jarabawa ce ubangiji ya riga ya jarabce ka da ita sai ka yi haƙuri da taka ƙaddarar”.

Murmushin da ya fi kuka ciwo ya yi kana ya gaida su Arɗo, ya tashi ya shige cikin ɗaki. Arɗo da Mamma suka hau mita,“ A ce mutum kullum da damuwa a ranshi, ya kasa bar wa Allah komai bari Baffanku ya dawo zan ƙara tuna mishi.” Mamma ta faɗa Arɗo ya ce “Wallahi ni ma Mamma abin nan yana matuƙar damuna, ɗazu nake wa Asama maganarshi.”

Nan dai su ka shiga mayar da zance. Asama ta ce “Ku yi haƙuri, irin yanayin nan bai da daɗi ko kaɗan, ku taya shi da addu’a.”

Mariya ɗaya daga cikin matan da ke shara ta aje tsintsiya tana karkaɗe farin zaninta ta ce “Bari na je gurinshi”, da yake yau kwananta ya shiga, ko da ta shiga ya cire kayanshi ya sa wata riga marar nauyi, ya zauna kan katifar dake shimfiɗe ɗakin. Ta ce “Mai gida na kawo maka ruwa?”

Girgiza kai ya yi, sannan ya ce “Zauna magana nake son mu yi da ke.”

Samun wuri ta yi ta zauna jikinta duk ya yi sanyi dan ta san duk Bobbo ya ce zai yi magana da ke to ba lafiya ba.

Ido ya ƙura mata yana kallon yanayinta duk ta daburce, tausayinta ya kama shi, amma ba yadda ya iya, ya ce “Mariya bari na fara da cewa ki yi haƙuri, ki yi haƙuri, don Allah ki yi haƙuri.”

Ya numfasa, Sannan ya ci gaba da magana “A gidan nan ban taɓa yin wani abu da gangan dan in muzguna wa wani ba, duk wani da yake tare da ni, ba ni da buri irin na ga yana farin ciki.”

Ya ɗan yi jima kaɗan, sannan ya ce “Mariya, wannan dalilin yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa ba na yawan magana, ki fahimce ni, kuma ina so ki samu wuri a zuciyarki da za ki yafe min! Don Allah Mariya ki yi haƙuri da duk abin da na yi miki”.

Kanshi ya ɗago yana kallon yanayinta, ya fuskanci akwai tashin hankali muraran a idonta, ƙarfin hali ya yi ya ce “Na yanke hukunci a kan cewa Ni IBRAHIM JAƁƁO.

To masu karatu wane laifi Bobbo ya yi ma Mariya kuma mine ne hukuncin da Bobbo ya yanke.

Ya kuke ganin Naheela da Naheel, shin kuna ganin zata iya nemo Naheel ɗan Sarkin Zimba kuwa?

<< Nawa Bangaren 1Nawa Bangaren 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.