Skip to content
Part 24 of 25 in the Series Nawa Bangaren by Queen-Nasmah

Nahad da Bobbo Sun bazama neman Naheela amma duk zagayen duniyar nan sun yi shi amma sun gagara gano ta , wanda a ɓangaren Naheela ya kasance jikinta ya bata ƴar uwarta na nemanta . Naheela ta riga ta san daga gare ta ne shiyasa Nahad bata samu ganinta ba , kowa ya san irin ƙarfin sihirin Naheela . Hannunta ta miƙe duka hannayen suka wani ƙamƙame , sai kuma ta miƙe yatsanta ɗaya wanda ya fara fitar da wani hayaƙi , idonta kuma na fitar da wani haske , wannan hayaƙin dake fita ya dawo takobi . Duk abun da Naheela ke yi Naheel yana kallonta .

Kallon takobin Naheela tayi ta ce “Kiyi musu jagora zuwa gare ni ” , sai ta ɗauki takobin ta saita bangon wurin ka cilla ta , buɗewa bangon yayi wannan takobin ta shige sannan ya rufe .

Ɓangaren su Nahad kuwa suna nan zaune Nazarin wata hanya , tunda su ba kamar sauran Aljanu ba ne ,rabinsu mutum rabi aljan. Kwatsam sai ga wata farar takobi mai Matuƙar sheƙi ta zo , a jikinta an rubuta «_TAKOBIN SARAUNIYA NAHEELA_» da manyan haruffa . Miƙe Nahad tayi tana faɗin “Duk yadda aka yi wannan takobin zata taimaka , mu bi bayanta ” , Bobbo ya ce “Naheela ce ta aiko da ita da kanta ” .

Hannun Bobbo Nahad ta riƙe , sannan ta riƙe takobin da hannu ɗaya ɓat suka ɓace sai wurin Naheela.

Naheela zaune gefen Naheel da yanzu ya fara sabawa da ita su Nahad suka shigo . Miƙewa tayi ta rungume Nahad cikin kuka ta ce “Barka da zuwa Masoyiyar ƴar uwata ” , kuka Nahad ta fashe da shi , Naheela ta jaye ta daga jikinta tana kallonta cikin Matuƙar soyayya ta ce “Ki daina kuka ƴar uwata mun haɗu daga ƙarshe ” , gaɗa kai Nahad tayi tana murmushi ta ce “Eh bayan shekaru masu yawa gashi mun haɗu ” , Naheela numfasa ta ce “muna da sauran rayuwa a tare ƴar uwata ” , gaɗa kai Nahad tayi .

Naheela ta maida dubanta ga Bobbo sannan ta kalli Nahad ta ce “Miyasa nake ji a jikina aurenku gobe ne ke da Ibrahim Sadauki “, Sam Nahad bata yi mamaki ba kasancewar ko ita tana jin irin haka a jikinta , Nahad ta ce “Eh gobe ne da yardar Allah ” , kallon Naheel Tayi ta tunkare shi ta ce “Naheel zan lunka ƙarfin ikona gare ka domin na tabbatar an yi aurenmu tare da su Nahad ” , “Naheela !” Naheel yayi maganar ba tare da ya san ya furta ba , Naheela ta ce “Bazan saurare ka ba Naheel ka kalli idona kawai ” tayi maganar da ƙarfi wanda yasa ko ina amsawa , juyar da fuskarshi yayi yana faɗin “bazan kalle ki ba ” , zara-zaran faruttanta ta miƙe ta juyo da fuskarshi Yadda zai fuskance ta tana faɗin “Na ce ka kalle ni baka ji ” , “Ni na ce bana so na kalle ki baki ji ba ” ya faɗa shi ma a fusace.

Nahad ta sako Wata wata mai ƙarfi daga idonta zuwa tsakiyar bayan Naheela , wannan wutar ta janyo hankalin Naheel ya ƙura Mata ido yana kallon cikin idonta dan ya ga yanayinta , bai san tarko ba ne , kawai wani ɗan ƙaramin dutsi ya fito daga idon Naheela da ƙarfin gaske ya shige idon Naheel . Ji yayi kamar an zuba mishi wasu ruwa masu Matuƙar sanyi duk ilahirin jikinshi , sai kuma ya ji zuciyarshi ta wanke tas kamar ba ita ba ,da sauri ya miƙe tsaye a gigice ya jawo Naheela cikinshi yana faɗin “Ina sonki Naheela !” hawaye suka gangoro mata a kunci ta ɗaga hannunta sama tana murmushi ta ce “Alhamdulillahi !”.

Nan take garin Zawatu ya ɗauka da kiɗe-kiɗe da bushe-bushe , ana shelar auren Naheela da Nabeel , Nahad da Bobbo , duk wani Aljani da ka sani ya fito domin ayi shagalin biki da shi .

Ɓangaren Hajiya Maryam kuwa ta sanar da Su Ahmad da su Hajiya Fulani , Ahmad ya ce zai ji , amma sauran sun ce ba wanda zai kai su bikin Aljanu , Hajiya Mabaruka ba a maganarta dan ita hassada ba za ta bari ayi abun arziki da ita ba.

*****

Washe gari da safe duk wani maciji da sauran aljannun garuruwa da duniya daban-daban sun hallara . Garin baka jin tashin komai sai kukan tsuntsuye , dabbobi da kiɗe-kiɗe duk alama ce ta farinciki da ya cika masu ciki.

Sarki Zawatunduma da Sarki Zimba sun fi kowa farinciki da wannan ranar in aka cere su Naheela .

Naheela da Nahad suka je nema albarkar iyaye inda suka fara da inda sarki Zawatunduma ya tsaya , Nahad ta fara ƙarasawa cikin Kuka ta rungume wani narkeken maciji wanda girmanshi yayi uku ɗin ƙibar mutum ta fashe da kuka , “Abbana !” ta faɗa cikin kuka , can cikin macijin sautin magana ke tashi “Ƴata yau kin ganni , ina miki fatan a yau da zaku yi aure ke da Ibrahim Allah ya baku farinciki mai ɗorewa ” , “Ameen” ta faɗa tana matsawa , Naheela ta zo ta rungume shi tafi minti goma sannan ya fara magana “Kin san miyasa na taso na zo gare ki ?” ya numfasa “an bani aron gangar jikin nan ne , saboda na bayar da Jinina da gangar jikina fansar lokutan da na ara , ina so na sheda wannan rana shiyasa na shigar da Ruhina jikin wannan macijin , ina taya ki murna “,cikin kuka ta ce “Abba na gode maka godiya mai tarin yawa” , “ shi kenan ƴata je ki nemi albarka wajen Mahaifiyarki “, hannun Nahad Naheela ta riƙe suka ɓace sai ɗakin Hajiya Maryam .

Ganin Nahad da Naheela bai razana Hajiya Maryam ba dan dama ta san sai an yi haka , da sauri Naheela ta faɗa jikin Hajiya Maryam tana kuka ta ce “Ummana ” , ba tare da Hajiya Maryam ta ji komai ba abun ka da ɗa da mahaifi ta rungume Naheela tana faɗin “Ƴata ” , Nahad ta shigo jikin Hajiya Maryam duk ta rungume su , sun fi minti biyar a haka Nahad ta miƙe tana faɗin “Ummanmu ki saka mana albarka ” , “Na riga nayi haka Nahad ” , Naheela ta ce “ki ƙara to ” , cikin farinciki da ya bayyana a fuskarta ta ce “Allah ya sanya ma aurenku da zuri’ar da zaku haifa albarka ” , da amin suka amsa.

*****

Ɓangaren Naheel ma Bobbo ya mishi rakiya zuwa wurin sarki Zimba da Mahaifiyarshi Shamshan , rungume mahaifinshi yayi ya ce “Na gode da ka samu damar halarta “, Sarki Zimba ya ce “ Ai dole ne mu zo aurenka” ɗan duƙar da kai Naheel yayi ya ɗago ya kalli Mahaifiyarshi ya ce “Na gode miki mama ” , rungume shi tayi ta ce “Ɗana guda ɗaya tilo ina farinciki yau na kusance a karo na farko ban ga tashin hankali a tare da kai ba ” , ɗagowa yayi daga jikinta ya ce “kiyi haƙuri mama ko can baya ba laifina ba ne ” , gefen fuskarshi ta shafa ta ce “ ita uwa an yi ta ne ta zamo mai uzuri ga ƴaƴanta , Na fahimce ka tun ranar da ka zo duniya , yanzu da zaka yi aure ina roƙon Allah ya albarka wannan auren ” , ƙara rungume ta yayi yana ƙanƙame ta kamar zai maida ta ciki ya ce “ Ameen ameen Mama “, nan Maman Naheel ta gaisa da Bobbo , Naheel muka suka sake gaisawa babanshi yana tambayar Rayuwarsu a nahiyar macizai . Naheel ya ce “mu zamu Je duniyar bil’adama domin tahowa da mutanen Ibrahim . An jima zamu dawo duk tare ” , Shamshan ta ce “To ɗana ka kula sosai ka ji “, hannunshi ta saki da ta riƙe sannan suka tashi sama shi da Bobbo .

Gidansu Sadauki aka tafi , in da Sadauki ya nemi albarkar Mamma , da Baffa , da Arɗo , sannan suka ke gidan su Mariya amaryar Bobbo wadda ya fara saki a farkon labarin . Sallama yasa aka mishi da ita sai gata ta fito da ciki niƙi-niƙi, yana kallon cikin yayi saurin kai hannunshi cikinta nan take ta ji cikinta kamar ba Ƴan hanji , kallon cikin tayi ta ga ya lefe kamar ba nata ba da sauri ta ɗago cikin kiɗimewa ta ce “ Bob…..”, “Shhhhh !” Bobbo ya dakatar da ita , ido ta ƙura mishi tana mamakin yadda halittarshi ta sauya idonshi kamar na damisa . Bobbo ya ce “Abun ke cikinki zai janyo miki muguwar hasara a rayuwa , domin bazai iya rayuwa cikin mutane ba , wannan duka jinsina ne “, ido ta zaro waje tana faɗin “Dama labarin da nake ji da gaske ne kai ajiyar aljani ne ” gaɗa mata kai yayi , da sauri ta shige ciki gida cikin ruɗa ni da tsoro .

Haka Bobbo ya dinga bin gidan matanshi yana ɗauke yaran da ba jinsin bil’adama ba, ƙaramin Sadauki ma da shi ya taho Mairo ko ta sha kuka amma ba yadda ta iya dan ita da kanta ta san Ba za ta iya rainon ƙaramin Sadauki ba , gashi yana yawan tsorata ta a banɗaki , sai tana wanka ya dinga kiranta yana mata suratai yaron da ko wata biyar bai yi ba , Gidansu Bintoto shi ne ƙarshe da ya je , a gidansu Bintoto bai ɗauki kowa ba dan duk jinsin bil’adama ne , yayi ma Bintoto sallama ita ma ta sha kuka . Sannan suka dawo gidan .

Da misalin ƙarfe sha biyu na dare Naheel ya kira wata ƙatuwar tsuntsuwa ta kwashe su mamma wanda a gefen cikin wannan tsuntsuwar akwai wata hanya da mutum bi idan ya shiga kamar yana cikin ɗaki , duk nan su mamma suka shige , har su Bobbo . Asama da Arɗo ma ba a bar su baya ba .

Nahad da Naheela su ka taho da Alhaji Sulaiman , Hajiya Maryam da kuma Ahmad .

Nahiyar Aljanu kuwa tun safe ake ta Raye-Raye , wasu na wasa da wuta , wasu na wasar wuƙa .

Macizai suka yi naɗin ganwo kamar kujera su Naheela suka zauna , su mamma kuwa kujerar mutane Naheela ta haɗa musu da takobin tsafi suka zauna .

Nan aka fara gasar nuna tsafi kowa da yadda yake nuna ƙwarewarshi , Naheela tayi ma waɗanda suka yi nasara kyauta , sannan aka fara raba ruwan jini ana ba ma aljannun wurin, Naheela ta aika aljani Birshyam yayi suffar mutane , ya je Duniyar mutane ya siyo abinci mutane da lemu ,Cikin ɗakika goma ya dawo dawo aka ba su Mamma.

Ƙarfe 2:00 Daidai

Wasu fararen dawatsuna masu Matuƙar ƙyalli suka fara saukowa , nan Amare da angwayensu suka miƙe suka taya dai-dai saiti da wani haske , ko ina na wurin a ɗauki wata ƙara mai huda kunne ta ruɗe ko ina na wurin , daidai saiti da inda su Naheela suka tsaya jini ya fara zubowa daga cikin wannan hasken sai da ya jiƙe su sharkaf sannan wasu macizai masu Matuƙar girma suka sauko daga cikin hasken ɗaya ya naɗe Naheela da Naheel wuri ɗa , ɗayan kuma ya naɗe Nahad da Bobbo wuri ɗaya , ko kansu baka gani , sannan macizan suka warware , Naheela ta kwanta ƙasa bisa al’ada ta auren Naheel ya buɗe baki ruwan madara suka tare fitowa daga bakinshi , ita da Nahad da Bobbo haka , sannan suka miƙe angwayen suka yi kamar yadda amaren suka yi , amaren kuma suka musu wanka da ruwan madara , sannan suka miƙe ruwa suka fara saukowa Saman kansu daga cikin wannan haske , dai-dai 2:30 ruwan suka tsaya nan take aka fara ihu ana tsalle-tsalle aure ya ɗauru .

<< Nawa Bangaren 23Nawa Bangaren 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×